• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Wednesday, September 30, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Yadda muka ta cafke tsohon Ministan Wutar Lantarki Saleh Mamman a Kaduna bayan ya tsere – EFCC

ALI KANO by ALI KANO
May 19, 2026
in Labarai
A A
0
Yadda muka ta cafke tsohon Ministan Wutar Lantarki Saleh Mamman a Kaduna bayan ya tsere – EFCC
Alhaji Saleh Mamman cikin ankwa bayan an kama shi a yau

Alhaji Saleh Mamman cikin ankwa bayan an kama shi a yau

Hukumar Yaƙi da Yi Wa Tattalin Arzikin Ƙasa Ta’annati (EFCC) ta kama tsohon Ministan Wutar Lantarki, Saleh Mamman, wanda ya tsere, a unguwar Rigasa da ke cikin birnin Kaduna a yau.

Hukumar ta bayyana cewa ta kama Mamman da safiyar yau ne bayan an shafe makonni tana neman sa ruwa a jallo, tana sa ido sosai tare da tattara bayanan sirri ta hannun jami’an ta.

Da yake ganawa da manema labarai kan kamen, Shugaban EFCC, Ola Olukoyede, ya bayyana cewa tsohon ministan ya ɓuya ne bayan da Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta same shi da laifin cin hanci da rashawa.

Ya ce: “A ranar 7 ga Mayu, 2026, Mai Shari’a James Omotosho ya sami Mamman da laifi a kan dukkan tuhume-tuhume 12 da suka shafi karkatar da kuɗaɗen da aka ware domin ayyukan samar da wutar lantarki na ruwa na Zungeru da Mambilla. Kotun ta same shi da laifi ba tare da yana gaban kotu ba, bayan ta amince da hujjar hukumar cewa masu gabatar da ƙara sun tabbatar da laifin sa ba tare da wata shakka mai ma’ana ba.

“A gare mu, yana da matuƙar muhimmanci a tabbatar da cewa wanda aka yanke wa hukunci ya fara zaman gidan yari, duba da yadda muke ɗaukar yaƙi da cin hanci da rashawa da muhimmanci. Wannan ƙudiri ne ya sa muka tura jami’an leƙen asiri domin gano inda yake tare da kama shi. Za mu bi hanyoyin da suka dace domin mayar da shi gidan gyaran hali.”

A hukuncin da ya yanke, Mai Shari’a Omotosho ya ce EFCC ta tabbatar da cewa Mamman da abokan hulɗar sa sun karkatar da aƙalla Naira biliyan 22 da aka ware domin aiwatar da manyan ayyukan samar da wutar lantarki.

Kotun ta kuma ce ɓangaren kariya ya kasa gabatar da hujjoji masu inganci da za su rusa ƙarar masu gabatar da ƙara.

Alƙalin ya yi Allah-wadai da karkatar da kuɗaɗen jama’a da aka ware domin ayyukan samar da wutar lantarki na Zungeru da Mambilla, yana mai bayyana hakan a matsayin babban cin amanar ƙasa.

Ya kuma lura da cewa wanda aka yanke wa hukuncin ya yi amfani da kamfanonin bogi da wasu abokan hulɗa domin wawure kuɗaɗen da aka ware domin muhimman ayyukan more rayuwar ƙasa.

Mamman, wanda ya kasance Ministan Wutar Lantarki tsakanin shekarar 2019 zuwa 2021 a gwamnatin tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, shi ne ke kula da ɓangaren wutar lantarki na Nijeriya da manyan ayyukan samar da wutar lantarki na ruwa, ciki har da ayyukan Mambilla da Zungeru.

Bayan samun sa da laifi, kotun ta bayar da umurnin a kama shi kuma a gurfanar da shi a ranar 13 ga Mayu, 2026, domin yanke masa hukunci.

Sai dai bai bayyana a kotu a ranar da aka tsara ba, lamarin da ya sa kotun ta ci gaba da yanke masa hukunci ba tare da halartar sa ba.

Daga bisani, Mai Shari’a Omotosho ya yanke wa Mamman hukuncin ɗaurin shekaru bakwai-bakwai a tuhume-tuhume na 1, 2, 3, 6, 7, 8, 9, 10, 11 da 12, ba tare da zaɓin tara ba.

An kuma yanke masa hukuncin ɗaurin shekaru uku a tuhuma ta 4 tare da zaɓin biyan tara ta Naira miliyan 10, sannan ɗaurin shekaru biyu a tuhuma ta 5 ba tare da zaɓin tara ba.

Kotun ta kuma ba da umurnin cewa hukuncin ya kasance a jere, wanda hakan ya kai jimillar shekaru 75 a gidan yari.

Baya ga wannan hukuncin, Mamman na kuma fuskantar wata shari’ar cin hanci da rashawa a Babbar Kotun Babban Birnin Tarayya, Abuja, kan zargin damfarar Naira biliyan 31.

A ranar 11 ga Mayu, 2026, Mai Shari’a Maryanne Anenih ta bayar da sammacin kama shi bayan ya kasa bayyana a gaban kotu a shari’ar da ta shafe shi da wasu mutum bakwai.

Tags: cin hanciEFCCMai Shari'a OmotoshorashawaSaleh Mamman
Previous Post

Binciken NNPC: EFCC ta samu umurnin ƙarshe na ƙwace jirgin sama mallakin Abdulsalam Kachallah

Next Post

Ofishin kula da ƙorafe-ƙorafen haraji zai ƙara amincewar jama’a da tsarin haraji – Ministan Yaɗa Labarai

Related Posts

Zaɓen 2027: Idris ya yi kira da a gudanar da watsa shirye-shirye cikin ɗa’a domin kare dimokiraɗiyya
Labarai

Zaɓen 2027: Idris ya yi kira da a gudanar da watsa shirye-shirye cikin ɗa’a domin kare dimokiraɗiyya

September 29, 2026
Abin da ya sa na fice daga NNPP – Gwamnan Kano
Labarai

Gwamnatin Kano ta hana hawan dawakai da hawan Durbar na sarakuna saboda dalilan tsaro

September 27, 2026
Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta
Labarai

Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta

September 25, 2026
Kotu ta amince wa ICPC ta binciki na’urorin da aka ƙwato daga gidan El-Rufa’i
Tsaro

Cewar: El-Rufai Na koyi darussa daga shirun da abokan hulɗa ta suka yi kan halin da nake ciki

September 24, 2026
Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96
Labarai

Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96

September 24, 2026
Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya
Labarai

Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya

September 22, 2026
Next Post
Ofishin kula da ƙorafe-ƙorafen haraji zai ƙara amincewar jama’a da tsarin haraji – Ministan Yaɗa Labarai

Ofishin kula da ƙorafe-ƙorafen haraji zai ƙara amincewar jama’a da tsarin haraji – Ministan Yaɗa Labarai

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!