• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Wednesday, September 30, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Binciken NNPC: EFCC ta samu umurnin ƙarshe na ƙwace jirgin sama mallakin Abdulsalam Kachallah

IRO MAMMAN by IRO MAMMAN
May 18, 2026
in Labarai
A A
0
Binciken NNPC: EFCC ta samu umurnin ƙarshe na ƙwace jirgin sama mallakin Abdulsalam Kachallah
Jirgin, ƙirar Hawker 125, wanda kotu ta ƙwace a yau Litinin 

Jirgin, ƙirar Hawker 125, wanda kotu ta ƙwace a yau Litinin 

Ƙarshen tika-tika, tik! A yau Litinin ne Babbar Kotun Tarayya da ke Maitama, Abuja, ta ba umurnin ƙarshe na ƙwace wani jirgin sama mallakar Abdulsalam Mustapha Kachallah saboda an gano cewa an saye shi ne ta hanyar sata.

Mai Shari’a Emeka Nwite ne ya zartar da hukuncin bayan ya gamsu da cewa Kachallah ya mallaki jirgin, ƙirar Hawker 125, sakamakon alaƙar sa da zamba, cin hanci da rashawa da kuma halasta kuɗaɗen haram da suka shafi aikin Samar da Wutar Lantarki Cikin Gaggawa na Maiduguri (MEPP).

Hukumar Yaƙi da Yi Wa Tattalin Arzikin Ƙasa Ta’annati (EFCC)

An ƙwace jirgin, mai lambar ƙira 800XP, lambar jeri 258553 da lambar rajista 5N-AMK, bayan wata buƙata da Hukumar Yaƙi da Yi Wa Tattalin Arzikin Ƙasa Ta’annati (EFCC)  ta gabatar a kotun.

Yayin yanke hukunci kan buƙatar, Mai Shari’a Nwite ya ce kamfanin Valiente Jet Limited, wanda Abdulsalam Mustapha Kachallah ke mallaka kuma yake a matsayin mai ruwa da tsaki a shari’ar, bai gabatar da isasshiyar hujja da za ta nuna dalilin da ya sa bai kamata a ƙwace jirgin har abada a ba Gwamnatin Tarayya ba.

Ya ce: “Mai ruwa da tsakin bai nuna tare da hujjoji sahihancin tushen kuɗin da aka yi amfani da su wajen sayen jirgin ba.”

Alƙalin ya jaddada cewa yadda aka ɓoye yadda aka mallaki jirgin ta hanyar amfani da sunan wani mai sana’ar canjin kuɗi wanda ya musanta sanin irin mu’amalar, ya ƙara tabbatar da cewa gaba ɗayan mu’amalar ba ta bisa doka ba ce.

Tun da farko kotun ta bayar da umurnin wucin gadi na ƙwace jirgin a ranar 13 ga Nuwamba, 2025, sannan ta umurci hukumar ta EFCC da ta wallafa umurnin a wata jarida ta ƙasa domin masu ruwa da tsaki su bayyana dalilin da ya sa bai kamata a ƙwace jirgin na dindindin ba.

Bayan wallafa sanarwar, sai wani kamfani mai suna Valiente Limited, wanda Alhaji Abdulsalam Mustapha Kachallah ya mallaka, ya shigar da takardun rantsuwa domin nuna dalilin adawa da ƙwarewar.

Buƙatar ƙwarewar ta ƙarshe ta samu goyon bayan takardar rantsuwa da Aminu Abdullahi, wani mai bincike a EFCC, ya gabatar.

A cewar mai binciken, hukumar ta samu bayanan sirri kan zargin haɗa baki, karɓar kuɗi ta hanyar yaudara da kuma halasta kuɗaɗen haram da suka shafi Kachallah.

Binciken ya nuna cewa a shekarar 2021, Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPCL) ya bayar da kwangiloli a ƙarƙashin aikin Samar da Wutar Lantarki ta Gaggawa na Maiduguri da darajar su ta kai dala $114,148,155 da kuma ₦23,172,969,904.

Kachallah, wanda a lokacin shi ne shugaban Hukumar Samar da Wutar Lantarki ta Karkara ta Jihar Borno kuma memba a kwamitin jagorancin aikin, ya yi amfani da matsayin sa da dangantakar sa da jami’an NNPCL wajen aikata haramtattun mu’amaloli masu alaƙa da aikin.

Binciken ya nuna cewa Kachallah ya shiga yarjejeniyoyi ba bisa ƙa’ida ba da kamfanin China Machinery Engineering Company (CMEC) ta hanyar wasu kamfanoni da yake da ɗimbin ruwa da tsaki a cikin su, sannan ya sayar da bayanan sirri na neman kwangilar aikin domin samun kuɗin cin hanci.

Binciken ya ƙara nuna cewa daga baya an bai wa CMEC kwangiloli uku a ƙarƙashin aikin, da darajar su ta kai $52,120,172 da kuma ₦20,213,956,953.

Sai aka karkatar da wani ɓangare na kuɗaɗen kwangilar ta hannun kamfanin Afuwa Integrated Services Limited, wani kamfanin canjin kuɗi, bisa ƙaryar cewa an ba shi kwangilar ƙarƙashin CMEC.

CMEC ta tura kuɗin $2,070,000 zuwa asusun Stanbic IBTC na Afuwa Integrated Services Limited bisa umurnin Kachallah.

Binciken ya kuma gano cewa an ƙirƙiri jabun takardun biyan kuɗi da sunan Afuwa Integrated Services Limited domin a yi ƙaryar cewa kamfanin ya yi wasu halastattun ayyuka ne ga CMEC.

Daga nan aka tura kuɗin zuwa wani asusu a ƙasar Brazil domin sayen jirgin daga wani kamfani na Brazil.

An ce Kachallah ya yi amfani da Afuwa Integrated Services Limited ta hanyar yaudara wajen sayen jirgin, kafin daga bisani ya ƙirƙiri jabun takardu domin mayar da mallakar sa zuwa Valiente Jet Limited, wani kamfani da ke da alaƙa da shi.

Ko da yake Kachallah ya yi adawa da buƙatar, yana cewa kuɗin da aka biya ta asusun Afuwa Integrated Services sun samo asali ne daga kwangilar da kamfanin sa ya yi da CMEC domin taimakawa wajen samun kwangilar aikin MEPP tare da ba da shawarwarin ƙwararru.

An saurari ɓangarorin shari’ar a ranar 30 ga Afrilu, 2026.

EFCC, wadda lauyoyin ta Iheanacho Ekele SAN da O.S. Ujam suka wakilta, ta kafa hujjar cewa matakin Kachallah ya karya tanade-tanaden Sashe na 8, 10 da 53 na Dokar ICPC, da kuma Dokar Hana Halasta Kuɗaɗen Haram, tare da cewa hujjoji sun nuna Kachallah jami’in gwamnati ne da gwamnatin Jihar Borno ta naɗa.

Lauyan Kachallah, M.E. Oru SAN, ya dage cewa Kachallah daban yake da kamfanonin sa da suka shiga yarjejeniyoyin, sannan wasu takardun da EFCC ta haɗa ba su cancanci karɓuwa a kotu ba.

Sai dai Iheanacho ya yi gaggawar mayar da martani, inda ya kawo misalan hukunce-hukuncen kotu da ke nuna cewa a lokutan zamba ko haramtacciyar mu’amala, doka na ba da damar a tona mutanen da ke bayan kamfanoni. Ya jingina da shari’ar Oyebanji vs State.

Ya kuma ce takardun da aka haɗa da takardar rantsuwa ba sa buƙatar ƙarin sahalewa bisa hukunce-hukuncen Aondoakaa vs Obot & Anor da Musa vs Jika.

A cikin hukunci mai zurfin nazari, bayan gamsuwa da hujjojin da aka gabatar, Mai Shari’a Nwite ya amince da ƙwace jirgin tare da miƙa shi ga Gwamnatin Tarayyar Nijeriya har illa masha Allahu.

Tags: Abdulsalam Mustapha Kachallahalmundahanacin hanciEFCC
Previous Post

ICPC ta musanta zargin an hana El-Rufa’i samun kulawar iyali da ta lafiya

Next Post

Yadda muka ta cafke tsohon Ministan Wutar Lantarki Saleh Mamman a Kaduna bayan ya tsere – EFCC

Related Posts

Zaɓen 2027: Idris ya yi kira da a gudanar da watsa shirye-shirye cikin ɗa’a domin kare dimokiraɗiyya
Labarai

Zaɓen 2027: Idris ya yi kira da a gudanar da watsa shirye-shirye cikin ɗa’a domin kare dimokiraɗiyya

September 29, 2026
Abin da ya sa na fice daga NNPP – Gwamnan Kano
Labarai

Gwamnatin Kano ta hana hawan dawakai da hawan Durbar na sarakuna saboda dalilan tsaro

September 27, 2026
Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta
Labarai

Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta

September 25, 2026
Kotu ta amince wa ICPC ta binciki na’urorin da aka ƙwato daga gidan El-Rufa’i
Tsaro

Cewar: El-Rufai Na koyi darussa daga shirun da abokan hulɗa ta suka yi kan halin da nake ciki

September 24, 2026
Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96
Labarai

Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96

September 24, 2026
Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya
Labarai

Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya

September 22, 2026
Next Post
Yadda muka ta cafke tsohon Ministan Wutar Lantarki Saleh Mamman a Kaduna bayan ya tsere – EFCC

Yadda muka ta cafke tsohon Ministan Wutar Lantarki Saleh Mamman a Kaduna bayan ya tsere - EFCC

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!