Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa Mai Zaman Kan ta (ICPC) ta musanta zarge-zargen cewa an hana tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, samun kulawar lafiya da kuma ziyartar iyalan sa yayin da yake tsare a cibiyar hukumar.
Ana ci gaba da tsare El-Rufai a hannun ICPC tun daga ranar 19 ga Fabrairu bisa zargin almundahanar kuɗi a lokacin mulkin sa na gwamnan Jihar Kaduna tsakanin 2015 da 2023.
A ranar 13 ga Afrilu, hukumar yaƙi da cin hancin ta gurfanar da tsohon gwamnan a gaban Babbar Kotun Kaduna kan sababbin tuhume-tuhume guda tara da suka shafi zargin damfara da cin zarafin ofis.
Taƙaddamar ta ƙara kamari a ranar Juma’a bayan da Mohammed Bello, ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Mazaɓar Kaduna ta Arewa kuma ɗan tsohon gwamnan, ya zargi ICPC da hana matar mahaifin sa kai masa abinci.
Ɗan majalisar ya kuma yi zargin cewa jami’an hukumar sun hana likita ganin El-Rufai, yana mai cewa hakan ya saɓa wa haƙƙoƙin sa na ɗan ƙasa.
Sai dai da yake magana a wani taron manema labarai a yau Litinin, kakakin ICPC, Mista Okor Odey, ya yi watsi da zarge-zargen, yana mai bayyana su a matsayin “ƙarya da yaudara.”
Odey ya ce hukumar ta damu da yadda wasu ke “ƙirkirar ƙarya” domin ɓata mata suna.
A cewar sa, tsarin kula da shiga da fita na ICPC yana bai wa baƙi damar shiga cibiyar ne kawai tsakanin ƙarfe 9:00 na safe zuwa 6:30 na yamma kowace rana.
Ya bayyana cewa matar El-Rufai ta isa harabar cibiyar ne bayan lokacin ziyara da aka amince da shi ya ƙare.
“An sanar da iyalan duk waɗanda ake tsare da su a hannun ICPC, ciki har da wannan iyalin, game da wannan tsari, kuma har zuwa wannan lamari suna bin dokar,” inji Odey.
Ya ƙara da cewa, “A ranar Juma’ar da ake magana a kai, an bai wa ɗaya daga cikin matan wanda ake tuhuma da kuma wata ma’aikaciyar gida damar kawo masa abinci aƙalla sau uku tsakanin ƙarfe 10:30 na safe zuwa 5:30 na yamma.”
Kakakin ICPC ya ƙara da cewa rajistar baƙi, wadda ke ɗauke da sunayen ‘yan’uwa da dalilin ziyarar su, tana nan domin tantancewa.
“Baƙin da aka amince da su — ciki har da ‘yan’uwa, lauyoyi, da ma’aikatan lafiya — ana ba su damar ziyara, kawo abinci, da kuma ganin waɗanda ake tsare da su,” inji shi.“ Amma ba a amince da shiga bayan ƙarfe 6:30 na yamma ba.”
Odey ya kuma yi martani kan wani bidiyo da ya karaɗe kafafen sada zumunta inda ɗaya daga cikin matan El-Rufai, wato Hajiya Aisha, ta yi zargin an hana ta shiga cibiyar, yana cewa ta isa wajen misalin ƙarfe 7:00 na yamma, kusan mintuna 30 bayan lokacin ziyara ya ƙare.
“Har ila yau, akwai bayanan da ke nuna cewa a wasu lokuta da suka gabata takan wuce lokacin ziyarar da aka amince da shi,” inji shi.
“Bugu da ƙari, matar da kan ta ta amince a cikin bidiyon cewa ta kai wa mijin ta karin kumallo da abincin rana a wannan rana, wanda hakan ya saɓa da zargin cewa ICPC ta hana shi samun abinci.
“Saboda matsayin sa, ICPC tana da ikon ɗaukar tsauraran matakan tsaro domin kare shi, da kuma sauran mutanen da ke tsare a hannun ta.”
Hukumar ta kuma musanta zargin cewa an hana likitocin El-Rufai damar ganin sa.
Odey ya bayyana cewa abin da hukumar ta yi shi ne neman shaidar tantancewa daga ma’aikatan lafiyar tare da tabbatarwa daga tsohon gwamnan kafin a ba su damar ganin sa a ƙarƙashin kulawa, yana mai cewa wannan tsari ne na tsaro na yau da kullum.
Ya ce: “Wannan matakin tsaro ne na yau da kullum. Ya kamata a ambata cewa a makon da ya gabaci wannan lamari, Malam El-Rufai ya nemi izini kuma aka ba shi damar ziyartar likitan haƙora da kuma likitan ido a lokuta biyu daban-daban.
“Hukumar ta raka shi a dukkan ziyarar biyu. Haka kuma, baya ga haka, yana da damar ganin ma’aikatan lafiyar cikin gida na hukumar da amfani da cibiyoyin ta idan ya buƙata.”
Kakakin na ICPC ya ƙara da cewa hukumar ba za ta bari a jawo ta cikin “labaran wasan kwaikwayo da aka ƙirƙira domin kauce wa hanyoyin hukuma na doka” ba.







