• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, September 29, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai Tsaro

Sojojin Amurka sun fitar da bidiyon farmakin da ya halaka mataimakin jagoran ISIS, Al-Minuki

ALI KANO by ALI KANO
May 16, 2026
in Tsaro
A A
0
Sojojin Amurka sun fitar da bidiyon farmakin da ya halaka mataimakin jagoran ISIS, Al-Minuki
Abu-Bilal al-Minuki

Abu-Bilal al-Minuki

Rundunar Sojin Amurka ta Afrika (AFRICOM) ta fitar da bidiyon farmakin soji da ya kai ga kashe kwamandan ƙungiyar Da’ish (ISIS), Abu-Bilal al-Minuki.

A cikin wata sanarwa da AFRICOM ta fitar a yau Asabar, ta ce an gudanar da farmakin ne bisa umurnin Shugaban Amurka da Sakataren Yaƙi, tare da haɗin gwiwa ta kusa da gwamnatin Nijeriya.

Ta ce bayanan farko sun nuna cewa an kashe ‘yan ta’adda da dama a yayin farmakin.

Rundunar ta ce an kai harin ne kan wata babbar cibiyar ISIS a arewa maso gabashin Nijeriya, tana mai bayyana hakan a matsayin wani ɓangare na ci gaba da haɗin gwiwar yaƙi da ta’addanci a yankin Tafkin Chadi.

“Bisa umarnin Shugaban Amurka da Sakataren Yaƙi, tare da haɗin gwiwa da gwamnatin Nijeriya, Rundunar Sojin Amurka ta Afrika ta gudanar da wani farmaki kan ISIS a arewa maso gabashin Nijeriya a ranar 16 ga Mayu, 2026.

“Binciken farko na rundunar ya nuna cewa an kashe ‘yan ta’adda da dama, ciki har da Abu-Bilal al-Minuki, daraktan ayyukan duniya na ISIS, da kuma wasu manyan shugabannin ƙungiyar. Babu wani sojan Amurka da ya ji rauni.

“Kamar yadda Shugaba Trump ya bayyana a daren jiya, AFRICOM tare da haɗin gwiwa da Sojojin Nijeriya sun gudanar da nasarar aiki cikin jarumtaka wanda ya kai ga hallaka Abu-Bilal al-Minuki da wasu shugabannin ISIS da dama,” inji Janar Dagvin Anderson na Rundunar Sojin Sama ta Amurka, kwamandan AFRICOM.

“Wannan farmaki ya nuna muhimmancin haɗin gwiwar Amurka da Nijeriya, kuma ya samu ne sakamakon haɗin kai da daidaiton aiki tsakanin rundunonin mu a watannin baya-bayan nan. Ku sani sarai, ƙasashen mu biyu za su ci gaba da bibiyar barazanar ta’addanci ba tare da sassauci ba tare da kawar da su, kuma muna da ƙudirin kare al’ummar mu da muradun mu.”

Rahotanni sun ce Al-Minuki na bayar da shawarwari na dabaru ga cibiyar ISIS ta duniya kan harkokin yaɗa labarai da kuɗaɗe, da kuma bunƙasa da ƙera makamai, bamabamai da jiragen sama marasa matuƙi.

An bayyana shi a matsayin ɗaya daga cikin ‘yan ta’adda mafi hatsari a duniya, wanda ke da dogon tarihin shirya hare-hare da kuma jagorantar garkuwa da mutane.

Tags: Abu-Bilal al-MinukiAFRICOMAmurkakisasojojita'addanciTafkin Chadi
Previous Post

Tinubu ya yaba wa sojojin Nijeriya da na Amurka kan kisan Al-Manuki, jagoran ISIS a Tafkin Chadi

Next Post

Nijeriya da Jamus sun ƙulla yarjejeniyar zuba jari ta dala miliyan 428

Related Posts

Kotu ta amince wa ICPC ta binciki na’urorin da aka ƙwato daga gidan El-Rufa’i
Tsaro

Cewar: El-Rufai Na koyi darussa daga shirun da abokan hulɗa ta suka yi kan halin da nake ciki

September 24, 2026
An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya
Tsaro

An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya

September 21, 2026
Ministan Yaɗa Labarai ya taya Kiristoci murnar bikin Ista
Tsaro

Gwamnatin Tarayya ta jajanta wa al’ummar Neja kan rasuwar mutane a Wushishi, ta bayar da umarnin bincike

September 18, 2026
Gwamnatin Tarayya ta dakatar da Kwamandan NSCDC na Neja
Tsaro

Gwamnatin Tarayya ta dakatar da Kwamandan NSCDC na Neja

September 18, 2026
Hukumar Shige da Fice ta kama wasu da ake zargi da satar mutane biyu, ta ƙwato Naira miliyan 34 a Adamawa
Tsaro

Hukumar Shige da Fice ta kama wasu da ake zargi da satar mutane biyu, ta ƙwato Naira miliyan 34 a Adamawa

September 9, 2026
Gwamnatin Tarayya ta ƙara ɗaukar sabbin dabarun kawo ƙarshen rashin tsaro, yayin da Matawalle ya ziyarci Kano kan harin Garun Malam
Tsaro

Gwamnatin Tarayya ta ƙara ɗaukar sabbin dabarun kawo ƙarshen rashin tsaro, yayin da Matawalle ya ziyarci Kano kan harin Garun Malam

September 1, 2026
Next Post
Nijeriya da Jamus sun ƙulla yarjejeniyar zuba jari ta dala miliyan 428

Nijeriya da Jamus sun ƙulla yarjejeniyar zuba jari ta dala miliyan 428

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!