Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yaba wa haɗin gwiwar tsaro tsakanin Nijeriya da Amurka, kan wani gagarumin samame da suka Kai a maɓoyar mayaƙan ƙungiyar IS a yankin Tafkin Chadi, wanda ya yi sanadin hallaka babban jagoran su da ake nema ruwa a jallo, Abu-Bilal Al-Manuki, wanda aka fi sani da Abu-Mainok.
Rahotanni sun ce an gudanar da harin ne a daren jiya bayan samun bayanan sirri da suka nuna inda jagoran kungiyar da wasu manyan kwamandojin sa suke ɓoye.
Majiyoyi sun bayyana cewa samamen ya kuma yi sanadin kashe wasu daga cikin na hannun damar sa tare da lalata sansanonin da ake zargin kungiyar na amfani da su wajen tsara hare-hare a yankin Tafkin Chadi da wasu sassan Arewa-maso-gabas.
An ce aikin haɗin gwiwar ya gudana cikin ƙwarewa, inda aka yi amfani da bayanan leken asiri da kuma kayan aiki na zamani wajen kai harin ba tare da bata lokaci ba.
Da yake yabo kan nasarar aikin, Shugaba Tinubu ya nuna muhimmancin zumuncin ƙasashen biyu wajen yaki da ta’addanci.
Ya ce: “Ina miƙa godiya ta ta musamman ga Shugaba Donald Trump saboda jagorancin sa da kuma goyon bayan da Amurka ke bai wa Nijeriya a wannan fafutuka.”
Tinubu ya kuma jinjina wa bajinta da ƙwarewar da dakarun suka nuna wajen aiwatar da samamen, yana faɗin, “Munanan hare-hare irin wannan su ci gaba da faɗawa maɓoyar ‘yan ta’adda a duk inda suke a faɗin ƙasar nan.”
Masana harkokin tsaro na ganin hallaka Abu-Bilal Al-Manuki na iya zama babbar koma-baya ga ayyukan ƙungiyar IS a yankin Tafkin Chadi, musamman ganin yadda ake alaƙanta shi da shirya hare-hare da safarar makamai a tsakanin ƙasashen yankin.
A ‘yan shekarun baya-bayan nan, Najeriya ta kara ƙarfafa haɗin gwiwar tsaro da ƙasashen duniya domin daƙile matsalar ta’addanci da ta addabi wasu sassan ƙasar nan, musamman Arewa-maso-gabas.







