• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, September 29, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Tinubu ya isa Legas bayan balaguro a ƙasar waje, zai halarci taron fidda gwani na APC ranar Asabar

ABUBAKAR IBRAHIM by ABUBAKAR IBRAHIM
May 15, 2026
in Labarai
A A
0
Tinubu ya isa Legas bayan balaguro a ƙasar waje, zai halarci taron fidda gwani na APC ranar Asabar
Shugaba Bola Ahmed Tinubu tare da Gwamna Sanwo-Olu da sauran jami'an gwamnati jim kaɗan bayan saukar sa a Babban Filin Jirgin Sama na Murtala Muhammed da ke Legas a daren yau

Shugaba Bola Ahmed Tinubu tare da Gwamna Sanwo-Olu da sauran jami'an gwamnati jim kaɗan bayan saukar sa a Babban Filin Jirgin Sama na Murtala Muhammed da ke Legas a daren yau

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya isa Legas a ranar Juma’a bayan ziyarar da ya kai ƙasashe uku—Faransa, Kenya da Ruwanda.

Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara na Musamman kan Yaɗa Labarai da Dabaru, Bayo Onanuga, ya faɗa a wata sanarwar manema labarai da ya sanya wa hannu cewa jirgin Tinubu ya sauka da misalin ƙarfe 7:12 na yamma a ɓangaren shugaban ƙasa na Babban Filin Jirgin Sama na Murtala Muhammed da ke Ikeja.

Waɗanda suka tarbe shi sun haɗa da Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu; Mataimakin Gwamna, Femi Hamzat; Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila; Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Legas, Mudashiru Obasa, da sauran jami’an gwamnati.

Yayin da yake Faransa, Shugaba Tinubu ya gana da masu zuba jari na duniya, inda ya jaddada gaskiya da bin ƙa’idojin kuɗi, tare da bayyana dalilan gaggauta aiwatar da manyan sauye-sauyen tattalin arzikin da gwamnatin sa ta ƙaddamar.

Ya kuma halarci taron “Africa Forward Summit” a Nairobi, Kenya, wanda Shugaban Faransa Emmanuel Macron da Shugaban Kenya William Ruto suka jagoranta tare.

A wurin taron, Tinubu ya yi kira da a sake fasalin tsarin kuɗaɗen duniya tare da ƙarfafa haɗin gwiwar tattalin arziki da zai fifita cigaban Afrika da wadata.

Ya bayyana irin damar da Nijeriya take da ita a fannin tattalin arzikin teku a matsayin ɗaya daga cikin ginshiƙan cigaban Afrika, tare da alƙawarin raba tsarin bayanan leƙen asirin harkokin teku na Nijeriya da ƙasashen yankin Tekun Guinea da suke da sha’awar hakan.

A Nairobi, Shugaban ya kuma gana da takwaran sa na Madagaska, Michael Randrianirina, a wata ganawar ƙasashe biyu.

A Kigali, babban birnin ƙasar Ruwanda, Shugaba Tinubu ya haɗu da sauran shugabannin Afrika, da masu zuba jari, da manyan shugabannin kamfanonin duniya da na Afrika a taron “Africa CEO Forum”, domin tattauna hanyoyin gaggauta sauyin tattalin arzikin nahiyar ta hanyar faɗaɗa haɗin gwiwa, haɗewar yankuna, da ƙara zuba jari tsakanin ƙasashe.

Ya kuma gana da shugaban Ruwanda kuma mai masaukin baƙi, Paul Kagame.

Haka kuma ya gana da wakilan kamfanoni da cibiyoyi na ƙasa da ƙasa, ciki har da International Finance Corporation (IFC), APM Terminals, da Winme Group, inda aka samu sakamako masu kyau.

Tinubu ya kuma shiga tattaunawa da zaman kwamitoci da suka bayyana manufofin shirye-shiryen sauye-sauyen tattalin arzikin gwamnatin sa.

A lokacin da yake Legas, Shugaban Ƙasa zai halarci zaɓen fidda gwani na jam’iyyar APC da za a fara gobe Asabar.

Tun da farko, a cikin wata sanarwa da ya aike wa membobin jam’iyyar, Tinubu ya buƙaci duk masu halartar zaɓen fidda gwanin da su “kiyaye zaman lafiya kuma su kasance masu nuna wasa da tsare gaskiya da adalci domin moriyar jam’iyya da ƙasar mu baki ɗaya.”

Tags: APC primariesBola Ahmed TinubuLegasSanwo-Olutaro
Previous Post

Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da motocin gas da na lantarki don rage kuɗin sufuri a Kano

Next Post

CBN ya ƙaddamar da sabon kundin dokokin canjin kuɗaɗen waje

Related Posts

Abin da ya sa na fice daga NNPP – Gwamnan Kano
Labarai

Gwamnatin Kano ta hana hawan dawakai da hawan Durbar na sarakuna saboda dalilan tsaro

September 27, 2026
Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta
Labarai

Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta

September 25, 2026
Kotu ta amince wa ICPC ta binciki na’urorin da aka ƙwato daga gidan El-Rufa’i
Tsaro

Cewar: El-Rufai Na koyi darussa daga shirun da abokan hulɗa ta suka yi kan halin da nake ciki

September 24, 2026
Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96
Labarai

Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96

September 24, 2026
Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya
Labarai

Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya

September 22, 2026
An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya
Tsaro

An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya

September 21, 2026
Next Post
CBN ya ƙaddamar da sabon kundin dokokin canjin kuɗaɗen waje

CBN ya ƙaddamar da sabon kundin dokokin canjin kuɗaɗen waje

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!