• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Thursday, October 1, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Fitaccen malamin makaranta kuma ɗan jarida Bashir Ashara ya rasu

ABUBAKAR IBRAHIM by ABUBAKAR IBRAHIM
May 1, 2026
in Labarai
A A
0
Fitaccen malamin makaranta kuma ɗan jarida Bashir Ashara ya rasu
Marigayi Dakta Bashir Hadi Ashara

Marigayi Dakta Bashir Hadi Ashara

Tsohon Shugaban Sashen Koyon Aikin Jarida (Mass Communication) na Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Kaduna (Kaduna Polytechnic), Dakta Bashir Hadi Ashara, ya rasu.

Ya rasu ne a daren jiya Alhamis, inda ya bar tarihi na hidima ga fannin ilimi da aikin jarida.

Za a gudanar da sallar jana’izar sa a yau a Masallacin Ɗanfodiyo da ke Unguwar Sanusi a Kaduna.

Ashara ƙwararren ɗan jarida ne da ya yi aiki da kamfanin jaridun New Nigerian da kuma tsohon kamfanin Nationhouse Press, inda ya bayar da gudunmawa ga mujallar The Sentinel da jaridar Nasiha.

Abokan aikin sa na tuna shi a matsayin mutum mai tawali’u kuma ginshiƙi a cikin al’ummar kafafen yaɗa labarai.

A cikin wani rubutu da aka wallafa a Facebook domin ba da sanarwar rasuwar sa, wani na kusa da shi ya bayyana wata ƙaramar nadama: Ashara ya aiko da saƙon gaisuwa mai daɗi a yammacin Laraba, amma wanda aka tura wa saƙon bai sani ba domin yana jagorantar wani taron horaswa da Ƙungiyar Matan ‘Yan Jarida ta Nijeriya (NAWOJ) ta shirya a Zariya, don haka bai samu damar mayar da martani ba. Wannan rubutun ya zama tunatarwa mai taɓa zuciya game da raunin rayuwa.

Ashara ya horar da ɗimbin matasa a lokacin da yake shugabantar Sashen Koyon Aikin Jarida a Kaduna Polytechnic.

Abokai da tsofaffin ɗaliban sa sun yi ta bayyana alhinin su a soshiyal midiya kan rasuwar wannan mutum da aka bayyana a matsayin fitaccen malami kuma nagari.

Allah ya gafarta masa kurakuran sa, ya saka masa da alherin hidimar sa ga ilimi, ya kuma ba shi Aljannar Firdausi, amin.

Tags: Dakta Bashir AsharaKaduna Polytechnicrasuwa
Previous Post

Juyin Zamani: Yadda CBN ke ƙarfafa wa ɗalibai koyon ilmin sarrafa kuɗi, yayin da tattalin arziki ke sauyawa a zamanance 

Next Post

Gwamna Uba Sani ya gode wa Tinubu kan kwangilolin ayyuka na sama da Naira tiriliyan 1 da biliyan 178 a Jihar Kaduna

Related Posts

Nijeriya ta gyara tafiyar ta, yanzu zamanin wadata ya zo – Tinubu
Labarai

Nijeriya ta gyara tafiyar ta, yanzu zamanin wadata ya zo – Tinubu

October 1, 2026
Ranar Zuciya ta Duniya: Idris ya yi kira da a ƙara kaimi wajen yaƙi da cututtukan zuciya
Kiwon Lafiya

Ranar Zuciya ta Duniya: Idris ya yi kira da a ƙara kaimi wajen yaƙi da cututtukan zuciya

September 30, 2026
Zaɓen 2027: Idris ya yi kira da a gudanar da watsa shirye-shirye cikin ɗa’a domin kare dimokiraɗiyya
Labarai

Zaɓen 2027: Idris ya yi kira da a gudanar da watsa shirye-shirye cikin ɗa’a domin kare dimokiraɗiyya

September 29, 2026
Abin da ya sa na fice daga NNPP – Gwamnan Kano
Labarai

Gwamnatin Kano ta hana hawan dawakai da hawan Durbar na sarakuna saboda dalilan tsaro

September 27, 2026
Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta
Labarai

Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta

September 25, 2026
Kotu ta amince wa ICPC ta binciki na’urorin da aka ƙwato daga gidan El-Rufa’i
Tsaro

Cewar: El-Rufai Na koyi darussa daga shirun da abokan hulɗa ta suka yi kan halin da nake ciki

September 24, 2026
Next Post
Gwamna Uba Sani ya gode wa Tinubu kan kwangilolin ayyuka na sama da Naira tiriliyan 1 da biliyan 178 a Jihar Kaduna

Gwamna Uba Sani ya gode wa Tinubu kan kwangilolin ayyuka na sama da Naira tiriliyan 1 da biliyan 178 a Jihar Kaduna

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • October 2026
  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!