Shugaban Hukumar Alhazai ta Ƙasa ta Nijeriya, Ambasada Ismail Abba Yusuf, ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya tana duba hanyoyi daban-daban domin tallafa wa kamfanonin jiragen saman Nijeriya, ciki har da waɗanda ke jigilar alhazai, wajen rage tasirin tashin farashin man jiragen sama a duniya kafin gudanar da aikin Hajjin 2026.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, Fatima Sanda Usara, ta fitar a yau Alhamis, an ambato Yusuf yana magana ne a daidai lokacin da ake ci gaba da shirye-shiryen aikin hajjin.
Yusuf ya ce hukumar tana ci gaba da tattaunawa da masu ruwa da tsaki a fannin zirga-zirgar jiragen sama domin tabbatar da ingantacciyar jigilar maniyyata ba tare da wata matsala ba.
Ya ƙara da cewa tattaunawa kan harkokin aiki, musamman batun man jiragen sama, wani ɓangare ne na yau da kullum a shirye-shiryen kafin hajji, kuma ana gudanar da shi ne cikin tsarin da aka saba.
Ya ƙaryata rahotannin da ke cewa wasu daga cikin kamfanonin jiragen saman da aka ɗauka ba sa son shiga aikin jigilar alhazai saboda tsadar mai, inda ya bayyana irin waɗannan rahotanni a matsayin hasashe marar tushe kuma ba sa nuna yadda ake haɗin kai tsakanin gwamnati da masu aiki a halin yanzu.
“Don kauce wa shakku, duk shirye-shiryen da ake buƙata suna tafiya yadda aka tsara, kuma an sa ranar fara jigilar maniyyata ta Hajjin 2026 a ranar 3 ga Mayu, 2026,” inji shi.
Yusuf ya kuma bayyana cewa shigar da Gwamnatin Tarayya cikin lamarin na nufin tabbatar da daidaito, ta yadda kamfanonin jiragen sama ba za su yi asara ba, haka kuma maniyyata ba za su fuskanci tsadar kuɗin tikiti mai yawa ba.
Ya ƙara da cewa duk kamfanonin jiragen saman da aka ɗauka domin aikin hajjin sun sake jaddada kudirin su na tabbatar da tsaro, inganci, da kuma gudanar da aiki ba tare da wata tangarɗa ba, yayin da tattaunawa da hukumomi da sauran masu ruwa da tsaki ke ci gaba.
Duk da matsin tattalin arziki da ake fuskanta, shugaban hukumar ya nuna ƙwarin gwiwa cewa duka jigilar maniyyata zuwa da dawowa daga Hajjin 2026 za su gudana cikin nasara.
Ya sake jaddada fatan hukumar cewa, tare da ci gaba da tallafin gwamnati da kuma kyakkyawan haɗin kai, maniyyatan Nijeriya za su samu ingantaccen aikin hajji mai nasara a shekarar 2026.







