Shugabar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, Misis Didi Esther Walson-Jack, ta aike da saƙon taya murna ga dukkan ma’aikatan gwamnati na Nijeriya dangane da bikin Ista.
A cikin wata sanarwa ga manema labarai, Walson-Jack ta ce: “Ina miƙa saƙon gaisuwa ta musamman gare ku duka yayin da muke bikin Ista na wannan shekara.
“Bikin Ista ba wai tunawa kawai ba ne; wani babban shaida ne na ƙarfin sadaukarwa, alƙawarin sabuntawa, da nasarar bege a kan yanke ƙauna. Bikin Ista yana kira gare mu da mu yi zurfin tunani kan kyawawan halaye na sadaukar da kai, juriya, da cikakken ƙwazo wajen hidima.
“A matsayin ku na ma’aikatan gwamnati da aka ɗora wa alhakin bunƙasa cigaban ƙasa, waɗannan ɗabi’u suna da matuƙar muhimmanci.
“Ruhin Ista yana ƙarfafa mu mu tashi sama da ƙalubale, mu tsaya tsayin daka a lokacin wahala, tare da sabunta jajircewar mu wajen ƙwarewa, tsare gaskiya, da hidimtawa ga ƙasa.
“Saboda haka ina kira a gare ku da ku ci gaba da rungumar sabon ruhin ƙwazo, ƙirƙire-ƙirƙire, da kishin ƙasa da Ista ke wakilta.
“Mu ci gaba da mai da hankali tare da aiki tare domin gina harkar aikin gwamnati na tarayya mai inganci, tsare gaskiya, kuma mai iya gogayya a duniya.
“Allah ya sa wannan lokaci ya ƙara mana azama, ya ƙarfafa ƙudirin mu na bayar da ingantacciyar hidimtawa, tare da sabunta alƙawarin mu ga gina ƙasa.
“Ina yi maku fatan zaman lafiya, farin ciki, da albarka a wannan bikin Ista. Barka da Ita.”
A wani labarin makamancin wannan, Ministan Gidaje da Raya Birane, Injiniya Ahmed Musa Ɗangiwa, shi ma ya taya mabiya addinin Kirista murna a wannan muhimmin lokaci na bikin addini.
Ya ce a cikin wata sanarwa: “Yayin da Kiristoci a faɗin Nijeriya da ma faɗin duniya suke bikin Ista, ina miƙa gaisuwa ta musamman da fatan alheri ga ‘yan’uwan mu Kiristoci.
“Ista lokaci ne da ke tunatar da mu muhimmancin sadaukarwa, bege, soyayya, da sabuntawa. Waɗannan ɗabi’u na kowa ne, kuma suna nuna burin gama-gari na dukkan ‘yan Nijeriya — wato gina ƙasa mai zaman lafiya, haɗin kai, da cigaba.
“A matsayi na na Musulmi, ina girmama tare da taya al’ummar Kirista murna a wannan lokaci mai tsarki.
“Saƙon Ista yana kira a gare mu da mu ci gaba da aiki tare cikin haɗin kai, tausayi, da hidimtawa ga juna.
“A madadin Ma’aikatar Gidaje da Raya Birane ta Tarayya, ina yi wa dukkan Kiristoci fatan murna da albarka a bikin Ista.
“Allah ya sa wannan lokaci ya sabunta begen mu na gaba ɗaya, ya kuma ƙarfafa jajircewar mu wajen gina Nijeriya mafi alheri ga kowa.
“Barka da Ista.”







