• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, September 29, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai Tsaro

Fadar Shugaban Ƙasa ta bayyana dalilin da ya sa Tinubu ya tsaya a filin jirgin sama yayin ziyarar sa a Jos

ABUBAKAR IBRAHIM by ABUBAKAR IBRAHIM
April 3, 2026
in Tsaro
A A
0
Fadar Shugaban Ƙasa ta bayyana dalilin da ya sa Tinubu ya tsaya a filin jirgin sama yayin ziyarar sa a Jos
Shugaba Tinubu a tsakiyar Gwamnan Filato da Shugaban APC na Ƙasa a filin jirgin saman Jos

Shugaba Tinubu a tsakiyar Gwamnan Filato da Shugaban APC na Ƙasa a filin jirgin saman Jos

Fadar Shugaban Ƙasa ta bayyana dalilin da ya sa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya tsaya a filin jirgin sama lokacin da ya kai ziyara Jos, jihar Filato, tana mai cewa hakan ya faru ne sakamakon rashin isasshen lokaci da kuma ƙalubalen gudanarwa.

Idan kun tuna,  Shugaban ya gana da iyalan waɗanda aka kashe lokacin da ‘yan bindiga suka kai hari a Angwan Rukuba da ke Ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa a Jihar Filato, a ranar Lahadi.

Yayin da yake jawabi ga waɗanda aka kawo domin ganawa da shi a filin jirgin saman, Shugaban Ƙasa ya ce: “Ba ku da wutar lantarki a filin jirgin sama, kuma dole ne in tashi cikin mintuna 10 masu zuwa. Ga waɗanda abin ya shafa, babu abin da zan iya ba ku, ko da kuɗi ne na miliyoyi, sai dai in yi muku ta’aziyya kuma in yi muku alƙawarin cewa wannan lamari ba zai sake faruwa ba.”

Ɗakin taron ya cika da magoya bayan siyasa, sarakunan gargajiya, jami’an tsaro, da sauran su.

Tsayawar Tinubu a filin jirgin sama ta haifar da ce-ce-ku-ce mai yawa, inda masu suka suka zargi Shugaban da rashin adalci ga iyalan da ke cikin jimami.

Daga cikin waɗanda suka fara sukar lamarin akwai jagoran ‘yan adawa kuma tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, wanda ya mayar da martani ta bakin mai taimaka masa, Phrank Shaibu.

A cewar sa, abin da ya faru ya mayar da wannan mummunan lamari zuwa wani “abin kallo da aka tsara,” inda aka fifita nuna hoto da salo sama da tausayi da mutuntawa.

Sai dai a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara na Musamman kan Yaɗa Labarai da Dabaru, Bayo Onanuga, ya ce tsarin tafiyar Shugaban na ranar Alhamis tun farko ya haɗa da karɓar Shugaban ƙasar Chadi, Mahamat Idriss Déby Itno, a Fadar Shugaban Ƙasa, kafin daga bisani ya wuce Iperu a Jihar Ogun.

Amma bayan wani bayani na tsaro da Gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang, ya gabatar, sai Shugaba Tinubu ya dakatar da tafiyar sa zuwa Ogun, inda ya shirya cikin gaggawa ya tafi Jos a daren ranar.

Duk da wannan sauyi, Shugaban bai samu damar sauya lokacin ganawar manyan shugabannin ƙasashen biyu ba, wadda ta mayar da hankali kan ƙarfafa haɗin gwiwar tsaro tsakanin Nijeriya da Chadi.

A cewar Onanuga, ganawar ta ɗauki lokaci fiye da yadda aka tsara, lamarin da ya jinkirta tashin Tinubu zuwa Jos.

Ya ce: “Da isar sa Jos, ziyarar ta fuskanci wasu ƙalubalen gudanarwa. Duk da cewa nisan hanya daga filin jirgin sama zuwa cikin garin Jos kusan minti 40 ne, filin jirgin ba ya karɓar saukar jirage da daddare saboda rashin kayan jagorancin sauka. Wannan ya sa ba zai yiwu a shiga gari, a gana da waɗanda abin ya shafa kai-tsaye, sannan a dawo filin jirgin kafin dare ya yi ba.

“Saboda haka, jami’an gwamnati na jiha da na tarayya suka yanke shawarar kawo wakilan al’ummar da abin ya shafa zuwa wani ɗaki da ke kusa da filin jirgin saman domin Shugaban ya gana da su cikin gaggawa, tare da bin ƙa’idojin zirga-zirgar jirage.

“Daga cikin waɗanda ke wurin akwai Ministan Tsaro, Babban Hafsan Soja, da Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, waɗanda suka kai ziyara Rukuba, cibiyar rikicin.

“Shugaba Tinubu ya tura wannan tawagar ta manyan jami’ai zuwa Rukuba, ciki har da Babban Mataimaki na Musamman kan hulɗa da al’umma, domin gudanar da muhimman shirye-shirye na tsaro da hulɗa da jama’a kafin zuwan sa.

“Bayan ta’aziyya da ya yi ga waɗanda abin ya shafa, manufar Shugaba Tinubu ita ce tattaunawa da manyan masu ruwa da tsaki a Jihar Filato kan yadda za a kawo ƙarshen rikicin da ya daɗe yana faruwa tsawon shekaru, wanda ya jawo asarar rayuka da dukiyoyi ba tare da dalili ba.”

Onanuga ya ƙara da cewa ziyarar Tinubu zuwa Jos ba wai kawai ta alama ba ce, illa wani “muhimmin mataki na dabaru a matakin ƙoli domin haɗa dukkan masu ruwa da tsaki wajen magance tushen rikici da rashin tsaro a jihar.

“Ya gana da waɗanda abin ya shafa, ya yi musu ta’aziyya, ya kuma saurare su.

“Haka kuma ya saurari shugabannin al’umma, ya kuma tabbatar musu da cewa Gwamnatin Tarayya za ta tabbatar da adalci tare da kawo ƙarshen wannan zagayowar tashin hankali.

“Ya yi alƙawarin girka kyamarori 5,000 masu amfani da fasahar AI domin sa ido a cikin birnin da kuma sauƙaƙa gano da kama masu tada hankali.

“Haka kuma, Shugaban ya gayyaci shugabannin al’umma zuwa Abuja domin ci gaba da tattaunawa kan yadda za a samar da mafita mai ɗorewa ga rikicin da ke yawan faruwa a jihar.

“Taron, wanda aka watsa kai-tsaye, ya kasance cikin natsuwa da kwantar da hankali, wanda ya ƙara wa mazauna yankin ƙwarin gwiwa.

“Shugaba Tinubu ya cimma manufar ziyarar sa duk da ƙoƙarin masu suka na ƙoƙarin raina ta. Ya isar da saƙo mai ƙarfi: dole ne a gina zaman lafiya mai ɗorewa tare da jama’a, ba a tilasta masu ba.”

Tags: Bayo OnanugaFilatojajantawaJosTinubuziyara
Previous Post

Ministan Yaɗa Labarai ya taya Kiristoci murnar bikin Ista

Next Post

Iran ta kakkaɓo jirgin yaƙin Amurka a sararin samaniyar ta

Related Posts

Kotu ta amince wa ICPC ta binciki na’urorin da aka ƙwato daga gidan El-Rufa’i
Tsaro

Cewar: El-Rufai Na koyi darussa daga shirun da abokan hulɗa ta suka yi kan halin da nake ciki

September 24, 2026
An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya
Tsaro

An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya

September 21, 2026
Ministan Yaɗa Labarai ya taya Kiristoci murnar bikin Ista
Tsaro

Gwamnatin Tarayya ta jajanta wa al’ummar Neja kan rasuwar mutane a Wushishi, ta bayar da umarnin bincike

September 18, 2026
Gwamnatin Tarayya ta dakatar da Kwamandan NSCDC na Neja
Tsaro

Gwamnatin Tarayya ta dakatar da Kwamandan NSCDC na Neja

September 18, 2026
Hukumar Shige da Fice ta kama wasu da ake zargi da satar mutane biyu, ta ƙwato Naira miliyan 34 a Adamawa
Tsaro

Hukumar Shige da Fice ta kama wasu da ake zargi da satar mutane biyu, ta ƙwato Naira miliyan 34 a Adamawa

September 9, 2026
Gwamnatin Tarayya ta ƙara ɗaukar sabbin dabarun kawo ƙarshen rashin tsaro, yayin da Matawalle ya ziyarci Kano kan harin Garun Malam
Tsaro

Gwamnatin Tarayya ta ƙara ɗaukar sabbin dabarun kawo ƙarshen rashin tsaro, yayin da Matawalle ya ziyarci Kano kan harin Garun Malam

September 1, 2026
Next Post
Iran ta kakkaɓo jirgin yaƙin Amurka a sararin samaniyar ta

Iran ta kakkaɓo jirgin yaƙin Amurka a sararin samaniyar ta

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!