Jami’an Hukumar Tsaron Cikin Gida (DSS) sun kama wata mata mai shekara 25, Nafisa Usman, bisa zargin ƙoƙarin kai harsasai ga ‘yan bindiga da ke aiki a jihohi da dama a Arewa.
A cewar wata majiya ta tsaro, an kama wadda ake zargin ne a wata babbar tashar mota a Kano, inda aka same ta da harsasai 200 sababbi.
Wata majiya ta ƙara da cewa wannan aiki ya biyo bayan sahihan bayanan sirri ne da suka bayyana motsi da ayyukan Nafisa.
Nagisa, wadda ta fito daga ƙauyen Zango a Ƙaramar Hukumar Ƙanƙara ta jihar Katsina, ta ɗauko harsasan ne daga Lafiya a Jihar Nasarawa zuwa Kano, inda daga nan za ta wuce da su zuwa Ƙanƙara.
A yayin tambayoyi, ta amsa cewa an miƙa mata kayan ne a tashar mota ta Unguwa Uku a Kano, da nufin ta kai su ga wani ɗan bindiga da ke dajin Ƙanƙara.
Nafisa ta kuma bayyana cewa ta shafe kusan watanni biyu tana wannan harkar, inda ta ƙara da cewa wani mutum mai suna “Teso”, wanda ta ce yana aiki tare da wani soja a Lafiya, shi ne ke ba ta harsasan.
Wadda ake zargin ta yi iƙirarin cewa tana kai harsasan ga wani ɗan bindiga mai suna Malam Haruna, ta ƙara da cewa wani dillalin dabbobi a Kano mai suna Sulaiman ne ya haɗa su.
A cewar ta, ta gudanar da harkoki da darajar su ta kai kimanin naira miliyan 5, tana kai harsasai ga Haruna da wasu mutane da aka bayyana da sunayen Buba da Abu, waɗanda kuma ake cewa suna aiki a dajin.
Wadda ake zargin ta nuna nadama kan shigar ta cikin wannan lamari, tana cewa yanzu gaskiya ta bayyana.






