• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Monday, September 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Gwamnatin Tarayya na shirin tallafa wa gidaje miliyan 15 ta hanyar HoPE-CT – Ministan Yaɗa Labarai

ABUBAKAR IBRAHIM by ABUBAKAR IBRAHIM
March 30, 2026
in Labarai
A A
0
Ba da yawu na Sa’idu Enagi ya yi rubutu kan siyasar Neja ba, kuma na dakatar da shi – Ministan Yaɗa Labarai
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ce Gwamnatin Tarayya za ta kai tallafi ga gidaje masu rauni miliyan 15 a faɗin ƙasar nan ta hanyar Shirin Tallafin Kuɗi na Inganta Rayuwar Iyali (HoPE-CT).

Idris, wanda Daraktan Hulɗa da Jama’a a ma’aikatar, Dakta Suleiman Haruna, ya wakilta, ya bayyana hakan ne a ranar Litinin a Abuja yayin taron bayani kan aiwatar da shirin da kuma ganawa da manema labarai.

Ya bayyana shirin a matsayin ɗaya daga cikin manyan shirye-shiryen tallafin jama’a mafi tasiri, yana mai cewa ya riga ya kai ga sama da mutane miliyan 9.2 a sassa daban-daban na ƙasar nan.

A cewar sa, shirin ya haɗa da bayar da tallafin kuɗi na N50,000 ga gidaje miliyan 3.6 domin tallafa wa rayuwar su da kuma rage talauci.

Ya ce: “Shirin HoPE-CT na nufin dawo da kyakkyawar fata, faɗaɗa damarmaki da kuma shimfiɗa tubalin wadata mai haɗa kowa. Hakan na nuna cewa gwamnati tana kula da buƙatun jama’a, musamman marasa galihu.”

Ministan ya buƙaci kafafen yaɗa labarai da su mayar da hankali kan tasirin da irin waɗannan shirye-shiryen suke yi ga rayuwar jama’a, ta hanyar bayar da sahihan rahotanni.

Ya ce: “A matsayin ku na masu bayar da labari, ya dace ku haskaka yadda waɗannan shirye-shirye suke canza rayuwar jama’a, ta hanyar nuna halin da suke ciki a baya da kuma yadda rayuwar su ta inganta, domin ƙarfafa kyakkyawar fata da amincewa da gwamnati.”

Idris ya sake jaddada cewa Shirin Sabunta Fata yana daga cikin manyan manufofin gwamnatin yanzu, kuma ya yi kira ga ƙarin haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da kafafen yaɗa labarai.

Ya kuma bayyana wasu shirye-shiryen tallafin jama’a, ciki har da rancen kuɗi ba tare da jingina ba ga matasa da mata, shirin lamunin ɗalibai, da kuma shirye-shiryen koyar da sana’o’i domin ƙarfafa tattalin arziki.

Ministan ya ce Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai za ta ci gaba da aiki tare da sauran hukumomi domin inganta harkar yaɗa bayanai da hulɗa da jama’a kan shirye-shiryen gwamnati.

A ƙarshe, ya ce: “Yayin da muke karɓar shawarwari tare da inganta aiwatar da shirye-shiryen mu, za mu ci gaba da sauraro da kuma aiwatar da abin da ya dace. Tare, za mu gina Nijeriya inda babu wanda za a bari a baya.”

Previous Post

Cikar wa’adin ƙarfafa jari: Yadda bankunan Nijeriya suka bazama tara Naira tiriliyan 4.6 a ƙoƙarin cika sharuɗɗan CBN

Next Post

Kwankwaso ya koma ADC, ya ƙarfafa haɗakar adawa a Kano

Related Posts

Abin da ya sa na fice daga NNPP – Gwamnan Kano
Labarai

Gwamnatin Kano ta hana hawan dawakai da hawan Durbar na sarakuna saboda dalilan tsaro

September 27, 2026
Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta
Labarai

Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta

September 25, 2026
Kotu ta amince wa ICPC ta binciki na’urorin da aka ƙwato daga gidan El-Rufa’i
Tsaro

Cewar: El-Rufai Na koyi darussa daga shirun da abokan hulɗa ta suka yi kan halin da nake ciki

September 24, 2026
Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96
Labarai

Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96

September 24, 2026
Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya
Labarai

Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya

September 22, 2026
An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya
Tsaro

An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya

September 21, 2026
Next Post
Kwankwaso ya koma ADC, ya ƙarfafa haɗakar adawa a Kano

Kwankwaso ya koma ADC, ya ƙarfafa haɗakar adawa a Kano

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!