Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Dakta Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana komawar sa jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) a ranar Litinin, matakin da aka bayyana a matsayin wani muhimmin cigaba ga siyasar adawa a jihar.
Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) ya ruwaito cewa Shugaban ADC na Ƙasa, Sanata David Mark, ya karɓi Kwankwaso tare da magoya bayan sa a gidan sa a ranar Litinin.
Mark ya jaddada cewa sauya sheƙar Kwankwaso ba kawai sauyin jam’iyya ba ne, yana mai bayyana hakan a matsayin martani ga ƙara yawan kiraye-kirayen da ‘yan Nijeriya suke yi na samar da ƙaƙƙarfan haɗin kan adawa mai iya kare ƙimar dimokiraɗiyya.
Ya ce yanzu ADC ta zama wata kafa ta haɗaɗɗiyar ƙungiyar siyasa ta ƙasa da ta ginu kan haɗin kai, gaskiya, ƙwarewa da ci gaba.
A cewar sa, manufar wannan haɗaka ita ce samar wa ‘yan Nijeriya ingantattun zaɓuɓɓuka tare da dawo da amincewa ga tsarin mulkin dimokiraɗiyya.
Mark ya nuna damuwa kan abin da ya kira raguwar sararin siyasar adawa a hankali, yana mai gargaɗin cewa duk wani mataki da zai tauye damar shiga harkokin siyasa barazana ce ga dimokiraɗiyya.
Ya jaddada muhimmancin kare haƙƙin ‘yan ƙasa na zaɓar shugabannin su cikin ‘yanci.
Ya ce: “Makomar Nijeriya ba za a gina ta bisa rinjaye da danniya ba, sai dai bisa shiga da gudunmawar kowa. Dole ne shugabanci ya samu ta hanyar amincewar jama’a, ba ta hanyar riƙe iko ba.”
A cewar sa, Kwankwaso yana da ɗimbin magoya baya a matakin ƙasa, musamman a Arewacin Nijeriya, ƙarƙashin tafiyar Kwankwasiyya.
Shugaban ADC ɗin ya yi kira ga ‘yan Nijeriya daga kowane ƙabila, addini da yanki da su shiga wannan tafiya, yana mai ƙarfafa musu gwiwa su taka rawar gani wajen gina tsarin mulki mai haɗa kowa da kowa tare da ɗaukar nauyin shugabanci.
Ya kuma miƙa gayyata ga sauran jam’iyyun siyasa, ƙungiyoyin fararen hula da ƙungiyoyin matasa da su haɗa kai a cikin wannan gamayya, yana mai cewa ƙarfafa dimokiraɗiyya aiki ne da ke buƙatar sadaukarwa da haɗin gwiwa daga kowa.
Mark ya bayyana fata cewa wannan sabuwar haɗaka za ta zama wani muhimmin sauyi a tafiyar dimokiraɗiyyar Nijeriya, yana mai kira ga ‘yan ƙasa da su rungumi haɗin kai, shiga harkokin siyasa da kuma kyakkyawan fata wajen tsara makomar ƙasa.
Tun da farko, Kwankwaso ya buƙaci magoya bayan ADC da su yi rijista da yawa a matsayin membobin jam’iyyar.
Ya kuma yi kira a gare su da su yaɗa manufofin jam’iyyar tare da shirya zaɓen shugabanni nagari domin tabbatar da kyakkyawan shugabanci ta hanyar rajistar INEC.
Alhaji Mubarak Fagge ya shaida wa NAN cewa ya yanke shawarar bin Rabiu Kwankwaso zuwa ADC ne domin tabbatar da nasarar jam’iyyar a zaɓuɓɓukan da ke tafe.
“Mun riga mun fara gangamin wayar da kan jama’a daga gida zuwa gida domin tabbatar da bunƙasar jam’iyyar a jihar,” inji shi.







