• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, September 29, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

Kano ta samu cibiyoyin sauya motoci zuwa CNG guda 41 yayin da Gwamnatin Tarayya take ƙara faɗaɗa shirin

Wakilin Mu by Wakilin Mu
March 22, 2026
in Kuɗi Da Tattalin Arziki
A A
0
Kano ta samu cibiyoyin sauya motoci zuwa CNG guda 41 yayin da Gwamnatin Tarayya take ƙara faɗaɗa shirin
Babban Jami’in Shirin CNG na Ƙasa (PCNGi), Barr. Ismaeel Ahmad, a lokacin ziyarar

Babban Jami’in Shirin CNG na Ƙasa (PCNGi), Barr. Ismaeel Ahmad, a lokacin ziyarar

Gwamnatin Tarayya na ƙara ƙaimi wajen samar da hanyoyin makamashi masu sauƙi da aminci a fannin sufuri, inda aka riga aka samar da cibiyoyi 41 na sauya tsarin motoci zuwa amfani da iskar gas (Compressed Natural Gas, CNG) a Jihar Kano.

Manufar shirin, wanda Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya samar, ita ce rage tsadar sufuri da ƙarfafa tsaron makamashi ta hanyar amfani da makamashi mai tsafta.

A wata ziyara da ya kai wurin ajiyar kayan sauya motoci da ke No. 12 Kakara Warehouse, Titin Haɗeja a Kano, a yau Lahadi, Babban Jami’in Shirin CNG na Ƙasa (PCNGi), Barr. Ismaeel Ahmad, ya bayyana cewa a halin yanzu akwai kimanin kayan sauya mota 3,524 a cikin rumbun, waɗanda suka haɗa da tankuna masu girman lita 30, 65 da 75, kuma a shirye suke domin raba wa cibiyoyin da aka amince da su a faɗin jihar.

Ya ce cibiyoyin suna da alhakin sauya motoci da a-daidaita-sahu daga man fetur zuwa amfani da CNG, matakin da ake sa ran zai rage kuɗin sufuri ga direbobi da fasinjoji.

A cewar sa, a yanzu cibiyoyi 41 suna karɓar kayan daga rumbun domin hanzarta aikin sauya tsarin motoci tare da faɗaɗa damar cin gajiyar shirin.

Wasu daga cikin cibiyoyin sun haɗa da Trade Source Integrated Concept, PKM Global Resource Ltd, Drive Green, Safe Auto Gas Ltd, Dazle Integrated Service, Go CNG Now Ltd, SJ Resource Limited, Arus CNG Conversion Centre, Fonnd Motor Manufacturing, Enormous International Centre, Danfyrt Autos Ltd, Afriks Ltd, AMK Integrated, ABG Oil & Gas, Green Africa Solutions, Amani Automobile Ltd, Ahad Projects Ltd, Pro-Prestige Ltd., Nuts and Bolt, da sauran su.

Shugaban na PCNGi ya sake jaddada aniyar Gwamnatin Tarayya na faɗaɗa shirin a faɗin ƙasar nan, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen rage tasirin tsadar mai tare da inganta amfani da makamashi mai tsafta.

Rumbun kayan CNG a Kano

Ya ƙara da cewa yawaitar cibiyoyin a Kano ya nuna yadda kamfanoni masu zaman kan su ke ba da gudunmawa tare da karɓuwar shirin daga jama’a.

Masu ruwa da tsaki a ɓangaren sufuri sun yaba wa shirin, suna masu cewa lokaci ya yi da ya dace, musamman wajen rage kashe kuɗi da inganta rayuwar al’umma.

Ana sa ran wannan faɗaɗawar za ta ƙara bunƙasa harkokin kasuwanci ta hanyar rage kuɗin jigilar kaya da fasinjoji, tare da tallafa wa ƙananan ’yan kasuwa da haɓaka tattalin arzikin Jihar Kano baki ɗaya.

Tags: CNGIsmaeel AhmadKanosufuri
Previous Post

Hukumomin tsaro suna aiki ba dare ba rana don kare ’yan Nijeriya – Minista

Next Post

Ba za mu bari rashin tsaro ya dusashe ƙoƙarin da muke na taimaka wa marasa ƙarfi ba — Tinubu

Related Posts

CBN: Tasirin rage kuɗin ruwa zuwa kashi 23% ga ’yan kasuwa da ’yan Nijeriya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Gangamin CBN a Kano: A daina wulaƙanta takardun naira, a riƙe su cikin inganci da nagarta – CBN

September 29, 2026
Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso

September 25, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN: Tasirin rage kuɗin ruwa zuwa kashi 23% ga ’yan kasuwa da ’yan Nijeriya

September 24, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Yadda Cardoso ya sauya fasalin CBN, ya saisaita manufofin kuɗi, ya daidaita tsare-tsaren tattalin arzikin Nijeriya

September 22, 2026
Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba

September 16, 2026
Tsakuren muhimman bayanai daga jawabin Gwamnan CBN a Taron Shugabannin Kamfanoni na 2026 wanda BusinessDay ta shirya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Lambar yabo daga NES ta tabbatar da ingancin manufofin CBN wajen tabbatar da daidaiton tattalin arziki — Cardoso

September 13, 2026
Next Post
Ba za mu bari rashin tsaro ya dusashe ƙoƙarin da muke na taimaka wa marasa ƙarfi ba — Tinubu

Ba za mu bari rashin tsaro ya dusashe ƙoƙarin da muke na taimaka wa marasa ƙarfi ba — Tinubu

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!