• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, September 29, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai Tsaro

Hukumomin tsaro suna aiki ba dare ba rana don kare ’yan Nijeriya – Minista

ABUBAKAR IBRAHIM by ABUBAKAR IBRAHIM
March 22, 2026
in Tsaro
A A
0
Hukumomin tsaro suna aiki ba dare ba rana don kare ’yan Nijeriya – Minista
Alhaji Mohammed Idris tare da Victoria Uwonkunda a lokacin tattaunawar su

Alhaji Mohammed Idris tare da Victoria Uwonkunda a lokacin tattaunawar su

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ce hukumomin tsaro suna aiki ba dare ba rana domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin ‘yan Nijeriya a duk faɗin ƙasar nan.

Ministan ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da wakiliyar BBC, Victoria Uwonkunda, inda ya yi tsokaci kan matsalolin tsaro na baya-bayan nan, ciki har da harin da aka kai Maiduguri.

A hirar, wadda za a iya kallo ta wannan liƙau a YouTube, Idris ya yi watsi da ra’ayin da wasu ke yaɗawa cewa hukumomin tsaron Nijeriya sun gaza, yana mai cewa ana ƙara ƙaimi domin hana aukuwar irin waɗannan hare-hare a gaba.

Ya ce: “Ba na ganin sun gaza. Ina ganin akwai buƙatar a ƙara ƙoƙari. Hukumomin tsaron Nijeriya suna aiki ba dare ba rana domin tabbatar da cewa hakan ba zai sake faruwa ba.”

Ya bayyana cewa Maiduguri ta samu gagarumin cigaba a ɓangaren zaman lafiya da kwanciyar hankali, ya ƙara da cewa Gwamnatin Tarayya tana ci gaba da ɗaukar matakai domin ƙarfafa tsaro a faɗin ƙasar nan.

A cewar sa,“Gwamnati tana mai da hankali sosai. Manufar tsare-tsaren gyaran da Shugaban Ƙasa yake aiwatarwa ita ce tabbatar da tsaron ’yan Nijeriya tare da hana sake aukuwar irin wannan lamari.”

Dangane da abubuwan da ke faruwa a duniya, musamman tashin hankalin Gabas ta Tsakiya, Idris ya ce a shirye Nijeriya take ta bayar da gudunmawa wajen tabbatar da zaman lafiyar duniya, musamman a fannin makamashi.

Ya ce: “A ko yaushe Nijeriya a shirye take ta taimaka wajen tsaron makamashi a duniya. Duk abin da za mu iya yi don rage tashin hankali, za mu yi. Duniya tana buƙatar mai, kuma Nijeriya na nan.”

Ministan ya kuma bayyana ziyarce-ziyarcen da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu yake yi a ƙasashen waje a matsayin masu muhimmanci wajen ƙarfafa dangantakar Nijeriya da sauran ƙasashe.

Ya ce: “Wannan ziyara tana nuna tsohuwar dangantaka, alaƙar al’adu da alaƙar tattalin arziki tsakanin Nijeriya da Birtaniya. Muna fatan za mu ƙara ƙarfafa wannan dangantaka domin amfanin ƙasashen biyu.”

Idris ya ƙara da cewa gyare-gyaren da gwamnati take aiwatarwa suna fara inganta matsayin Nijeriya a idon duniya.

Ya ce: “Da gyare-gyaren da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya aiwatar, mun fara ganin gagarumin sauyi a tattalin arziki.”

Ya yi nuni da cewa hulɗar ƙasashen waje da Shugaban Ƙasa ke yi tana nuna yadda duniya take ƙara amincewa da Nijeriya.

A ƙarshe, ya jaddada cewa Gwamnatin Tarayya za ta ci gaba da aiwatar da gyare-gyare tare da ƙarfafa tsaro domin tabbatar da cewa ’yan Nijeriya suna rayuwa da aiki cikin aminci.

Tags: BBChiraMohammed IdrisVictoria Uwonkunda
Previous Post

Yarjejeniya kan hijira da Birtaniya: A daina yaɗa labaran ƙarya, inji gwamnatin Nijeriya

Next Post

Kano ta samu cibiyoyin sauya motoci zuwa CNG guda 41 yayin da Gwamnatin Tarayya take ƙara faɗaɗa shirin

Related Posts

Kotu ta amince wa ICPC ta binciki na’urorin da aka ƙwato daga gidan El-Rufa’i
Tsaro

Cewar: El-Rufai Na koyi darussa daga shirun da abokan hulɗa ta suka yi kan halin da nake ciki

September 24, 2026
An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya
Tsaro

An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya

September 21, 2026
Ministan Yaɗa Labarai ya taya Kiristoci murnar bikin Ista
Tsaro

Gwamnatin Tarayya ta jajanta wa al’ummar Neja kan rasuwar mutane a Wushishi, ta bayar da umarnin bincike

September 18, 2026
Gwamnatin Tarayya ta dakatar da Kwamandan NSCDC na Neja
Tsaro

Gwamnatin Tarayya ta dakatar da Kwamandan NSCDC na Neja

September 18, 2026
Hukumar Shige da Fice ta kama wasu da ake zargi da satar mutane biyu, ta ƙwato Naira miliyan 34 a Adamawa
Tsaro

Hukumar Shige da Fice ta kama wasu da ake zargi da satar mutane biyu, ta ƙwato Naira miliyan 34 a Adamawa

September 9, 2026
Gwamnatin Tarayya ta ƙara ɗaukar sabbin dabarun kawo ƙarshen rashin tsaro, yayin da Matawalle ya ziyarci Kano kan harin Garun Malam
Tsaro

Gwamnatin Tarayya ta ƙara ɗaukar sabbin dabarun kawo ƙarshen rashin tsaro, yayin da Matawalle ya ziyarci Kano kan harin Garun Malam

September 1, 2026
Next Post
Kano ta samu cibiyoyin sauya motoci zuwa CNG guda 41 yayin da Gwamnatin Tarayya take ƙara faɗaɗa shirin

Kano ta samu cibiyoyin sauya motoci zuwa CNG guda 41 yayin da Gwamnatin Tarayya take ƙara faɗaɗa shirin

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!