• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, September 29, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Yarjejeniya kan hijira da Birtaniya: A daina yaɗa labaran ƙarya, inji gwamnatin Nijeriya

Wakilin Mu by Wakilin Mu
March 22, 2026
in Labarai
A A
0
Yarjejeniya kan hijira da Birtaniya: A daina yaɗa labaran ƙarya, inji gwamnatin Nijeriya
Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, tare da ministar Birtaniya bayan sun rattaba hannu kan yarjejeniyoyin

Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, tare da ministar Birtaniya bayan sun rattaba hannu kan yarjejeniyoyin

Nijeriya ta yi karin haske kan yarjejeniyar haɗin gwiwa kan harkar hijira tsakanin ta da Birtaniya,.

Wannan ya biyo yawaitar bayanan ƙarya da ake yaɗawa a wasu kafofin soshiyal midiya.

A cikin sanarwar da mai ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Yaɗa Labarai da Dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar, gwamnatin ta ce yarjejeniyar da aka ƙulla a lokacin ziyarar aiki ta Shugaba Bola Ahmed Tinubu a Birtaniya tana da nufin ƙarfafa dangantaka da kuma tsara hanyoyin zirga-zirgar jama’a cikin tsari mai kyau.

~ Ba a tilasta wa Nijeriya karɓar baƙin haure ba

Sanarwar ta jaddada cewa babu wani sashe a cikin yarjejeniyar da ya tilasta wa Nijeriya ta karɓi baƙin haure waɗanda ba ‘yan ƙasar nan ba. Ta ce duk wanda za a dawo da shi dole ne ya kasance ɗan Nijeriya ne wanda aka tabbatar da asalin sa ta hanyoyi da dama na tantancewa.

Haka kuma, idan aka samu kuskure wajen kawo mutum, ƙasar da ta turo shi ce za ta sake karɓar sa tare da ɗaukar nauyin dukkanin kuɗin da abin ya shafa.

~ Mayar da ‘yan ƙasa cikin mutunci

Yarjejeniyar ta tanadi cewa duk wani ɗan ƙasar nan da za a dawo da shi daga wata ƙasa dole ne a yi hakan cikin mutunci, tare da kiyaye haƙƙoƙin sa na ɗan’adam.

Hukumomin tsaro na ƙasashen biyu za su yi aiki tare domin kare lafiyar ‘yan ƙasa da kuma rage matsalolin da ka iya tasowa daga batun hijira.

~ Tsare-tsaren dawo da ‘yan ƙasa

An bayyana cewa za a iya dawo da mutum ta jirgin sama na yau da kullum ko na musamman, tare da bayar da cikakken bayani kafin kwanaki biyar da aiwatar da hakan.

Haka kuma, dole ne a tabbatar da sahihancin takardun tafiya, ko ta hanyar fasahar tantance bayanai (biometric), kafin a kammala shirin mayar da mutum.

~ Nijeriya ce ke da ikon bayar da takardu

Sanarwar ta fayyace cewa Hukumar Shige da Fice ta Nijeriya ce kaɗai ke da ikon bayar da takardun da suka dace ga ‘yan ƙasar da za a dawo da su, ba tare da wani tsoma baki daga ƙasashen waje ba.

~ Tallafin sake tsugunar da masu dawowa

A cewar sanarwar, yarjejeniyar ta tanadi tallafi ga masu dawowa, ciki har da:

  •  Taimakon gaggawa kamar masauki da sufuri
  • Haɗa su da iyalan su
  • Tallafin sana’o’i da ilimi
  • Samar da damar kafa kasuwanci

Haka kuma, za a samar da asusun tallafi domin taimaka wa masu dawowa su samu dogaro da kai a rayuwar su.

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa irin wannan yarjejeniya ba sabuwa ba ce, domin an taɓa ƙulla makamanciyar ta a shekarun baya, kuma wannan sabuwar yarjejeniyar za ta ɗauki tsawon shekaru biyar kafin a sabunta ta.

A ƙarshe, gwamnati ta buƙaci kafafen yaɗa labarai da su riƙa neman sahihin bayani kafin wallafa labarai, domin kauce wa yaɗa bayanan da ba su dace ba.

Tags: Birtaniyahijiralabaran ƙaryayarjejeniya
Previous Post

Tinubu a London: Yadda Gwamnan CBN ya bayyana inganci, ƙarfi da juriyar sauye-sauyen manufofin kuɗi a Nijeriya, a taron masu zuba jari a Afrika

Next Post

Hukumomin tsaro suna aiki ba dare ba rana don kare ’yan Nijeriya – Minista

Related Posts

Abin da ya sa na fice daga NNPP – Gwamnan Kano
Labarai

Gwamnatin Kano ta hana hawan dawakai da hawan Durbar na sarakuna saboda dalilan tsaro

September 27, 2026
Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta
Labarai

Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta

September 25, 2026
Kotu ta amince wa ICPC ta binciki na’urorin da aka ƙwato daga gidan El-Rufa’i
Tsaro

Cewar: El-Rufai Na koyi darussa daga shirun da abokan hulɗa ta suka yi kan halin da nake ciki

September 24, 2026
Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96
Labarai

Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96

September 24, 2026
Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya
Labarai

Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya

September 22, 2026
An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya
Tsaro

An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya

September 21, 2026
Next Post
Hukumomin tsaro suna aiki ba dare ba rana don kare ’yan Nijeriya – Minista

Hukumomin tsaro suna aiki ba dare ba rana don kare ’yan Nijeriya – Minista

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!