• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Monday, September 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Nijeriya tana darajta daɗaɗɗiyar dangantakar ta da Saudiyya, kuma za ta ƙarfafa ta – Minista

Wakilin Mu by Wakilin Mu
February 26, 2026
in Labarai
A A
0
Kamfanin jiragen Saudiyya zai dawo da zirga-zirga a Nijeriya
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, yana musabaha da Jakaden Saudiyya a Nijeriya, Yosef Bin Mohammed Al Balawi, a lokacin ziyarar a hedikwatar Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai ta Tarayya da ke Abuja a ranar Laraba.

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, yana musabaha da Jakaden Saudiyya a Nijeriya, Yosef Bin Mohammed Al Balawi, a lokacin ziyarar a hedikwatar Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai ta Tarayya da ke Abuja a ranar Laraba.

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, tare da Jakaden Saudiyya a Nijeriya, Yosef Bin Mohammed Al Balawi, a lokacin ziyarar a hedikwatar Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai ta Tarayya da ke Abuja a ranar Laraba.

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya sake jaddada ƙudirin Nijeriya na ƙarfafa dangantakar ta da Masarautar Saudiyya ta hanyar bunƙasa haɗin gwiwa a fannonin yaɗa labarai, sadarwa, tattalin arziki da tsaro.

Ministan ya bayyana haka ne a lokacin da ya karɓi baƙuncin Jakaden Saudiyya a Nijeriya, Yosef Bin Mohammed Al Balawi, tare da tawagar sa a hedikwatar Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai ta Tarayya da ke Abuja a ranar Laraba.

Yayin da yake maraba da Jakaden, Ministan ya bayyana ziyarar a matsayin wani muhimmin mataki na zurfafa haɗin gwiwar hukumomi tsakanin ƙasashen biyu.

Ya jaddada cewa Nijeriya na daraja dangantakar ta mai ɗorewa da Saudiyya, kuma ta himmatu wajen faɗaɗa haɗin kai a muhimman fannoni.

Ya ce: “Nijeriya tana darajta dangantakar ta mai daɗaɗɗen tarihi da Masarautar Saudiyya, kuma mun ƙudiri aniyar mayar da tarihin haɗin kan mu zuwa ƙarfafa hulɗodin hukumomi, musamman a fannonin haɗin gwiwar kafofin yaɗa labarai, tattalin arziki da harkokin tsaro domin amfanin al’ummomin mu.”

Ministan ya bayyana cewa Nijeriya ta amince da manyan Takardun Yarjejeniyar Fahimtar Juna guda uku (MOUs) da hukumomin Saudiyya suka gabatar domin ƙarfafa haɗin gwiwa a fannin yaɗa labarai da sadarwa.

Waɗannan sun haɗa da musayar labarai tsakanin Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) da Kamfanin Dillancin Labarai na Saudiyya, haɗin gwiwa wajen watsa shirye-shiryen rediyo da talbijin tsakanin Hukumar Talbijin ta Nijeriya (NTA) da Hukumar Watsa Labarai ta Saudiyya, da kuma haɗin gwiwa a fannin kafafen yaɗa labarai na sauti da gani tsakanin Hukumar Kula da Watsa Labarai ta Nijeriya (NBC) da hukumomin da suka dace a Masarautar.

A cewar sa, waɗannan yarjejeniyoyi za su ƙarfafa musayar ƙwarewa, inganta daidaitaccen yaɗa bayanai, da kuma bunƙasa diflomasiyyar kafofin yaɗa labarai tsakanin ƙasashen biyu.

Ya ce: “Takardun Yarjejeniyar Fahimtar Juna tsakanin cibiyoyin mu na yaɗa labarai ba takardu ba ne kawai; suna wakiltar wani muhimmin mataki na ƙarfafa diflomasiyyar kafofin yaɗa labarai, inganta musayar sahihan bayanai, da zurfafa dangantakar ƙasashen mu.”

Ministan ya kuma jaddada muhimmancin haɗin gwiwa a dandamalin ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa irin su Ƙungiyar Haɗin Kan Ƙasashen Musulmi (OIC) da UNESCO, inda ƙasashen biyu suke da muradu iri ɗaya.

Ya ce Nijeriya tana da niyyar yin aiki kafaɗa da kafaɗa da Saudiyya wajen inganta zaman lafiya a duniya, tattaunawar al’adu, da cigaba mai ɗorewa.

Yayin da ya amince da ƙaƙƙarfar alaƙar addini da al’adu tsakanin ƙasashen biyu, Ministan ya yi godiya ga Saudiyya bisa ci gaba da tallafa wa harkokin aikin Hajji da Umrah ga maniyyata ‘yan Nijeriya.

Ya kuma yi maraba da tattaunawar da ake yi kan yiwuwar dawo da jiragen sama kai-tsaye tsakanin Jiddah da Abuja, yana mai cewa hakan zai ƙara ƙarfafa hulɗar jama’a da jama’a, yawon buɗe ido da musayar tattalin arziki.

A nasa jawabin tun da farko, Jakada Yosef bin Mohammed Al Balawi ya nuna godiya bisa kyakkyawar tarbar da aka yi masa, tare da isar da muradin ƙasar sa na ƙarfafa haɗin gwiwa da Nijeriya a muhimman fannoni da suka haɗa da tattalin arziki, tsaro, yaɗa labarai da dangantakar siyasa.

“Saudiyya tana ɗokin yin aiki tare da Nijeriya domin ƙarfafa haɗin gwiwa a fannonin yaɗa labarai, tattalin arziki, tsaro da harkokin addini, tare da tabbatar da cewa ana yaɗa sahihan bayanai masu ma’ana game da ƙasar mu ta hanyar ƙarfafa hulɗodin hukumomi,” inji Jakaden.

Jakaden ya kuma sake jaddada aniyar Saudiyya na ci gaba da hidimta wa maniyyatan Nijeriya, tare da bayyana cewa ana ci gaba da ƙoƙarin inganta haɗin kai da sauƙaƙa zirga-zirga domin amfanin al’ummomin ƙasashen biyu.

Waɗanda suka halarci zaman ziyarar sun haɗa da Babban Sakataren Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Ogbodo Chinasa Nnam; Daraktan Sadarwar Jama’a, Henshaw Ogubike; Daraktan Hulɗa da Jama’a da Tsare-tsare, Dakta Suleiman Haruna; Daraktar Cibiyar Adana Takardun Ƙasa, Dakta Evelyn Odigboh, da sauran su.

Tags: hulɗaMohammedIdrisSaudiyyaYosefBinMohammedAlBalawi
Previous Post

Kamfanin jiragen Saudiyya zai dawo da zirga-zirga a Nijeriya

Next Post

Tsaraba daga CBN: Muhimman darussa biyar daga taron Kwamitin Tsare-tsaren Manufofin Kuɗi

Related Posts

Abin da ya sa na fice daga NNPP – Gwamnan Kano
Labarai

Gwamnatin Kano ta hana hawan dawakai da hawan Durbar na sarakuna saboda dalilan tsaro

September 27, 2026
Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta
Labarai

Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta

September 25, 2026
Kotu ta amince wa ICPC ta binciki na’urorin da aka ƙwato daga gidan El-Rufa’i
Tsaro

Cewar: El-Rufai Na koyi darussa daga shirun da abokan hulɗa ta suka yi kan halin da nake ciki

September 24, 2026
Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96
Labarai

Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96

September 24, 2026
Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya
Labarai

Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya

September 22, 2026
An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya
Tsaro

An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya

September 21, 2026
Next Post
Yadda asusun kuɗaɗen waje na Nijeriya zai cika maƙil, bayan CBN ya yi wa naira allurar ƙarin ƙarfin wujijjiga dala a tsakiyar kasuwa

Tsaraba daga CBN: Muhimman darussa biyar daga taron Kwamitin Tsare-tsaren Manufofin Kuɗi

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!