• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Wednesday, September 30, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai Tsaro

Tinubu ya rantsar da sabon Ministan Tsaro Janar Christopher Musa

Wakilin Mu by Wakilin Mu
December 4, 2025
in Tsaro
A A
0
Tinubu ya rantsar da sabon Ministan Tsaro Janar Christopher Musa
Shugaba Bola Ahmed Tinubu yana rantsar da tsohon Babban Hafsan Tsaro, Janar Christopher Gwabin Musa (ritaya), a matsayin Ministan Tsaro

Shugaba Bola Ahmed Tinubu yana rantsar da tsohon Babban Hafsan Tsaro, Janar Christopher Gwabin Musa (ritaya), a matsayin Ministan Tsaro

Shugaba Bola Ahmed Tinubu a yau ya rantsar da tsohon Babban Hafsan Tsaro, Janar Christopher Gwabin Musa (mai ritaya), a matsayin Ministan Tsaro.

Rantsarwar, wadda aka yi a wani taro da aka gudanar a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, ta biyo bayan murabus ɗin Alhaji Mohammed Badaru Abubakar a ranar 1 ga Disamba, wanda aka ce ya buƙaci a sauke shi daga muƙamin saboda dalilan lafiya.

A ranar Talata ne aka ba da sanarwar naɗin Musa, aka tura wa Majalisar Dattawa, wadda ta yi sauri ta tantance da amincewa da shi jiya.

Tinubu da sabon Ministan suna gaisawa bayan rantsarwar

Janar Musa, wanda aka haifa a Sakkwato a 1967, ya shiga aikin soja a 1991 bayan kammala horo a matsayin ƙaramin laftanar. Ya yi dogon aiki a rundunar, inda a 2023 Shugaba Tinubu ya naɗa shi Babban Hafsan Tsaro, kafin ya yi ritaya a watan Oktoba 2025.

A lokacin da yake jagorantar rundunar tsaro, Janar Musa ya yi fice wajen ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin sassan tsaro domin inganta ayyukan yaki da rashin tsaro.

Da aka rantsar da shi a yau, zai fara aiki nan take, yayin da Gwamnatin Tinubu ke ƙoƙarin ƙarfafa nasarorin tsaro da aka samu baya-bayan nan da kuma hanzarta sauye-sauyen da ake gudanarwa don tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a faɗin ƙasar nan.

Matar sabon ministan, Mrs Lilian Oghogho Musa, da Babban Hafsan Tsaro Janar Olufemi Oluyede, suna kallon Janar Musa yana rattaba hannu a kan takardar rantsarwar

A wajen rantsarwar akwai Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio, Jagoran Majalisar Dattawa Opeyemi Bamidele, Shugaban Kwamitin Shari’a na Majalisar Dattawa Sanata Adeniyi Adegbonmire, Ministan Yaɗa Labarai Mohammed Idris, da Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro, Malam Nuhu Ribadu.

Matar sabon ministan, Misis Lilian Oghogho Musa, Babban Hafsan Tsaro Janar Olufemi Oluyede; Bishop Matthew Hassan Kukah na Cocin Katolika ta Sakkwato, da Mai Shari’a Kumai Bayang Akaahs (mai ritaya) su ma sun halarci taron.

Tags: JanarChristopherMusaMinistan TsarorantsarwaShugabaBolaTinubu
Previous Post

CBN ya ƙara yawan kuɗin da za a iya cira daga ATM zuwa N100,000 a kullum

Next Post

Taron IILM na 35: Yadda CBN ya gudanar da taron kwamitin gudanarwar manyan bankunan ƙasashe takwas

Related Posts

Kotu ta amince wa ICPC ta binciki na’urorin da aka ƙwato daga gidan El-Rufa’i
Tsaro

Cewar: El-Rufai Na koyi darussa daga shirun da abokan hulɗa ta suka yi kan halin da nake ciki

September 24, 2026
An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya
Tsaro

An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya

September 21, 2026
Ministan Yaɗa Labarai ya taya Kiristoci murnar bikin Ista
Tsaro

Gwamnatin Tarayya ta jajanta wa al’ummar Neja kan rasuwar mutane a Wushishi, ta bayar da umarnin bincike

September 18, 2026
Gwamnatin Tarayya ta dakatar da Kwamandan NSCDC na Neja
Tsaro

Gwamnatin Tarayya ta dakatar da Kwamandan NSCDC na Neja

September 18, 2026
Hukumar Shige da Fice ta kama wasu da ake zargi da satar mutane biyu, ta ƙwato Naira miliyan 34 a Adamawa
Tsaro

Hukumar Shige da Fice ta kama wasu da ake zargi da satar mutane biyu, ta ƙwato Naira miliyan 34 a Adamawa

September 9, 2026
Gwamnatin Tarayya ta ƙara ɗaukar sabbin dabarun kawo ƙarshen rashin tsaro, yayin da Matawalle ya ziyarci Kano kan harin Garun Malam
Tsaro

Gwamnatin Tarayya ta ƙara ɗaukar sabbin dabarun kawo ƙarshen rashin tsaro, yayin da Matawalle ya ziyarci Kano kan harin Garun Malam

September 1, 2026
Next Post
Taron IILM na 35: Yadda CBN ya gudanar da taron kwamitin gudanarwar manyan bankunan ƙasashe takwas

Taron IILM na 35: Yadda CBN ya gudanar da taron kwamitin gudanarwar manyan bankunan ƙasashe takwas

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!