• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Wednesday, September 30, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

Taron IILM na 35: Yadda CBN ya gudanar da taron kwamitin gudanarwar manyan bankunan ƙasashe takwas

ASHAFA MURNAI BARKIYA by ASHAFA MURNAI BARKIYA
December 5, 2025
in Kuɗi Da Tattalin Arziki
A A
0
Taron IILM na 35: Yadda CBN ya gudanar da taron kwamitin gudanarwar manyan bankunan ƙasashe takwas

A ƙarƙashin jagorancin Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Olayemi Cardoso, CBN ya gudanar da taron Kwamitin Gudanarwa na 35 na manyan bankunan duniya guda takwas, wato International Islamic Liquidity Management Corporation (IILM) a karon farko a Nijeriya, a Hedikwatar CBN da ke Abuja.

Wannan taron dai ya yi daidai da wa’adin Gwamna Cardoso a matsayin Shugaban Kwamitin Gudanarwa na IILM, wanda tabbas ke nuna ƙaruwar tasirin Nijeriya a fannin hadahadar bisa tsarin kuɗin Islama na duniya da kuma jajircewar ta wajen ƙarfafa kasuwancin kuɗin da ba su da ruwa.

Shugabannin manyan bankuna daga Indonesiya, Kuwait, Maleshiya, Mauritius, Nijeriya, Ƙatar, Turkiyya, UAE da ICD ne suka hallara domin tantance nasarorin da suka samu a cikin shekarar 2025 da kuma saita muhimman abubuwan da za a mayar da hankali a kan su cikin tsarin kula da kuɗaɗe na duniya.

A lokacin shugabancin Nijeriya na shekarar 2025, Kwamitin Gudanarwa na IILM ya samu gagarumin ci gaba, wanda ya haɗa da ƙarin fitar da takardun sakamako na SUKUK, faɗaɗa yawan masu zuba jari, da ƙarfafa kayan aikin likwiditi ga cibiyoyin kuɗi na Islama.

CBN ya kuma gudanar da taron ƙwarewa kan Gudanar da Tsarin samar da kuɗaɗe ta hanyar SUKUK, na Islama ga sashen bankunan da ba su da ruwa a Nljeriya, wanda ya ƙara inganta ƙwarewar fasaha da bunƙasa kasuwa.

Nijeriya ta ƙara tabbatar da jajircewarta ga tsarin kuɗi na duniya na game-gari, tare da karfafa amincewar masu zuba jari a sashen kuɗin da ba shi da ruwa da ke bunkasa, ta hanyar gudanar da wannan muhimmin taro.

IILM dai wani kwamiti ne na Manyan Bankunan ƙasashe takwas da kuma wata babbar ƙungiya ta duniya, domin samar da kuɗaɗe a bisa tsarin da Shari’ar Musulunci ta tanadar, wato SUKUK.

Tags: CBNIILMSUKUK
Previous Post

Tinubu ya rantsar da sabon Ministan Tsaro Janar Christopher Musa

Next Post

Tinubu ya yabi sojojin Nijeriya kan kare dimokiraɗiyya a Benin

Related Posts

CBN: Tasirin rage kuɗin ruwa zuwa kashi 23% ga ’yan kasuwa da ’yan Nijeriya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Gangamin CBN a Kano: A daina wulaƙanta takardun naira, a riƙe su cikin inganci da nagarta – CBN

September 29, 2026
Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso

September 25, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN: Tasirin rage kuɗin ruwa zuwa kashi 23% ga ’yan kasuwa da ’yan Nijeriya

September 24, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Yadda Cardoso ya sauya fasalin CBN, ya saisaita manufofin kuɗi, ya daidaita tsare-tsaren tattalin arzikin Nijeriya

September 22, 2026
Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba

September 16, 2026
Tsakuren muhimman bayanai daga jawabin Gwamnan CBN a Taron Shugabannin Kamfanoni na 2026 wanda BusinessDay ta shirya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Lambar yabo daga NES ta tabbatar da ingancin manufofin CBN wajen tabbatar da daidaiton tattalin arziki — Cardoso

September 13, 2026
Next Post
Tinubu ya yabi sojojin Nijeriya kan kare dimokiraɗiyya a Benin

Tinubu ya yabi sojojin Nijeriya kan kare dimokiraɗiyya a Benin

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!