An sake zaɓar Farfesa Nentawe Yilwatda da Sanata Ajibola Basiru a matsayin Shugaba da Sakatare na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na ƙasa.
An zaɓe su ne a yau Juma’a a wurin babban taron ƙasa na huɗu na zaɓen shugabannin jam’iyyar APC da aka gudanar a dandalin Eagle Square da ke Abuja.
Kwamitin gudanar da zaɓe na taron jam’iyyar ne ya bayyana zaɓen su a matsayin wasu daga cikin shugabannin da aka dawo da su ba tare da hamayya ba.

A makon da ya gabata, jam’iyyar mai mulki ta bayyana cewa za ta ci gaba da amfani da tsarin rabon muƙamai (zoning) na kwamitin gudanarwa na ƙasa (NWC) a lokacin taron nata na ƙasa.
A cikin wata sanarwa, sakataren yaɗa labarai na ƙasa na APC, Felix Morka, ya ce an bayyana wannan tsarin ne a cikin jadawalin ayyukan jam’iyyar da aka fitar, wanda ya haɗa da tarurrukan gundumomi a faɗin ƙasa, babban taron ƙasa, da sauran ayyuka na shekarar 2026.
Ya ƙara da cewa tsarin rabon muƙaman NWC a tsakanin jihohi cikin yankunan siyasa na ƙasa har yanzu yana nan daram kuma zai kasance a taron.
Morka ya shawarci masu neman muƙaman ƙasa a jam’iyyar da su bi wannan tsarin rabon muƙamai ba tare da kaucewa ba.
A ci gaba da aiwatar da wannan mataki, an dawo da Yilwatda da Basiru ba tare da hamayya ba a matsayin shugaba da sakatare, bi da bi.
Taron, mai taken “Haɗin kai don ci gaba: ƙarfafa Sabuwar Fata”, ya samu halartar Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima, Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio, da Kakakin Majalisar Wakilai Tajudeen Abbas, tare da sauran manyan jiga-jigan jam’iyyar.
Kwamitin shirya taron, wanda Aminu Masari, tsohon gwamnan Jihar Katsina, da Anyim Pius Anyim, tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), suka jagoranta, shi ne ya shirya taron.
A cewar Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris, kimanin wakilai 8,453 ne suke halartar taron.







