• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, May 5, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Shirin Sabunta Fata na Tinubu yana samar da damarmakin cigaba — Minista

NEW CITIZEN HAUSA by NEW CITIZEN HAUSA
July 10, 2025
in Labarai
A A
0

 

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana cewa Shirin Sabunta Fata na Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu yana samar da damarmaki na cigaban ƙasa a fannoni daban-daban na tattalin arzikin Nijeriya.

Ministan ya bayyana haka ne a ranar Alhamis a Minna, Jihar Neja, yayin taron Kwamishinonin Yaɗa Labarai daga jihohin da jam’iyyar APC take mulki, wanda Ƙungiyar Gwamnonin APC ta shirya don ƙarfafa dabarun sadarwa da haɗin gwiwa tsakanin matakai daban-daban na gwamnati.

Ya ce: “Shirin Sabunta Fata ya wuce sauye-sauyen tattalin arzikin ƙasa gaba ɗaya. Magana ce ta samar da damarmakin cigaban ƙasa a fannoni daban-daban – ga mutum ɗaya, ga iyalai, da kuma ga al’umma gaba ɗaya.”

Ya bayyana cewa gwamnatin Tinubu tana aiwatar da shirye-shirye masu ɗaukar hankali ta hanyar manyan ayyukan gine-gine, shirye-shiryen tallafa wa matasa, da kuma sauye-sauye a fannonin noma, makamashi, ilimi da ƙere-ƙere.

Ministan ya bayyana cire tallafin fetur a matsayin ɗaya daga cikin manyan matakan da gwamnatin ta ɗauka domin farfaɗo da tattalin arziki.

Ya ce: “Ɗaya daga cikin manya kuma mafi tasiri daga cikin matakan da wannan gwamnati ta ɗauka shi ne cire tallafin fetur, wanda ko da yake ya kasance mai raɗaɗi, amma sauyi ne da ya zama dole. Bayan ceton tattalin arzikin ƙasa daga rugujewa, wannan mataki ya hana ɓarna da asarar kuɗi sosai a tattalin arzikin mu.”

A cewar sa, kuɗaɗen da aka ceto daga cire tallafin ana amfani da su ne wajen manyan ayyukan raya ƙasa irin su hanyar Legas zuwa Kalaba, hanyar Sakkwato zuwa Badagiri, shimfiɗa layin dogo na Kaduna zuwa Kano, da sake gina hanyar mota ta Abuja zuwa Kaduna da Kano.

Ya ƙara da cewa akwai cigaba da aka samu wajen saka hannun jari a fannin ayyukan jin daɗi a faɗin ƙasar nan, tare da ƙaruwa a cikin kuɗaɗen da ake tura wa jihohi a kowane wata, wanda ke ba su damar aiwatar da ayyuka masu tasiri a matakin jiha da ƙananan hukumomi.

Dangane da shirye-shiryen tallafa wa jama’a, Idris ya bayyana cewa sama da ƙananan harkokin kasuwanci 900,000 sun riga sun amfana daga Shirin Tallafi da Lamunin Shugaban Ƙasa, yayin da sama da ɗalibai 350,000 suke amfana da lamunin karatu domin tabbatar da cewa babu matashin da zai kasa karatu sakamakon rashin kuɗi.

Ya bayyana cewa gwamnati ta ware kimanin naira biliyan 70 don lamunin karatu, wanda sama da matasa 600,000 suke neman amfana da shirin.

Ministan ya kuma bayyana ƙirƙirar Hukumomin Cigaban Yankuna a faɗin ƙasar nan da cewa wani mataki ne da Shugaban Ƙasa Tinubu ya ɗauka domin tabbatar da cigaba bisa yanayin kowane yanki daga cikin yankunan siyasa shida na ƙasar nan.

Ya ce aikin bututun gas ɗin Ajakuta zuwa Kaduna da Kano (AKK) yana tafiya yadda ya kamata, kuma zai bai wa masana’antu da ke kan wannan hanya wutar lantarki domin farfaɗo da masana’antu.

Ya ce: “Da zarar an kammala aikin, zai kawo wutar lantarki daga Ajakuta zuwa Kaduna da Kano. Wannan yana nufin cewa dukkan masana’antun da ke kan wannan layi za a farfaɗo da su.”

Idris ya bayyana gwamnatin Tinubu a matsayin gwamnati mai ɗaukar rayuwar matasa da muhimmanci, inda ya ambaci shigar matasa da dama cikin Majalisar Zartarwa ta Tarayya a matsayin ministoci da kuma wasu muƙamai a hukumomin gwamnati.

Ya ƙara da cewa gwamnatin tana kashe naira biliyan 75 ta hanyar Bankin Masana’antu (BOI) domin tallafa wa ƙanana da matsakaitan masana’antu a fannoni daban-daban da nufin samar da ayyukan yi da kuma ƙarfafa matasa.

Ya ce: “Waɗannan ba wai wasu alƙaluma ne kawai marasa ma’ana ko maganganu na manufofi ba. Waɗannan damarmaki ne—damarmaki na zahiri, waɗanda za a iya auna su, ga kowane ɗan Nijeriya.”

Idris ya yi kira ga Kwamishinonin Yaɗa Labarai na jihohi da su ɗauki nauyin isar da saƙon da ya shafi manufofin gwamnati ga jama’a da kuma fahimtar yadda za su amfana da su.

Ya ce: “Saboda haka, nauyin mu ne a matsayin masu kula da yaɗa labarai, mu tabbatar da cewa ‘yan ƙasa a faɗin jihohin tarayya ba kawai sun san da waɗannan sauye-sauye da shirye-shirye ba ne, amma su ma fahimci yadda za su iya samun dama su amfana da su.”

Ya shawarci kwamishinonin da su koma jihohin su da sabon ƙwazo, su yi amfani da Hukumar Wayar da Kai ta Ƙasa (NOA) da kuma haɗin gwiwa da masu ruwa da tsaki na cikin gida domin fassara shirye-shiryen Gwamnatin Tarayya zuwa ayyuka masu amfani a matakin ƙasa.

Taron, wanda Gwamnatin Jihar Neja ta karɓi baƙuncin sa, ya haɗa kwamishinonin yaɗa labarai daga jihohin APC domin ƙarfafa dabarun sadarwa da kuma inganta haɗin gwiwa wajen aiwatar da Shirin Sabunta Fata a matakin jihohi da ƙananan hukumomi.

Hoto:
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris (a tsakiya), tare da Sakataren Gwamnatin Jihar Neja, Alhaji Abubakar Usman Gawu (a dama), da Darakta Janar na Ƙungiyar Gwamnonin APC, Folorunso Aluko (a hagu), da Kwamishinonin Yaɗa Labarai a jihohin da jam’iyyar APC ke mulki a wurin taron su a Minna, Jihar Neja, a ranar Alhamis.

Previous Post

Hayaniyar siyasar 2027 ba za ta ɗauke hankalin Tinubu daga alƙibla ba – Idris

Next Post

Ƙarin Girma ‘Yan Sanda: Kwamishinoni 12 sun zama AIG, Kuma An Ɗaga Wasu Jami’an Zuwa Sama

Related Posts

Shugaban NDC, Dickson ya yi wa Umar Arɗo raddi kan barazanar kai su kotu kan batun rajista
Siyasa

Shugaban NDC, Dickson ya yi wa Umar Arɗo raddi kan barazanar kai su kotu kan batun rajista

May 5, 2026
Ranar ’Yancin ’Yan Jarida ta Duniya: Nijeriya na neman a haɗa gwiwa a yaƙi masu yaɗa labaran ƙarya
Labarai

Ranar ’Yancin ’Yan Jarida ta Duniya: Nijeriya na neman a haɗa gwiwa a yaƙi masu yaɗa labaran ƙarya

May 4, 2026
Kwankwaso da Obi sun koma NDC
Siyasa

Kwankwaso da Obi sun koma NDC

May 3, 2026
Dalili na na ficewa daga ADC – Peter Obi
Siyasa

Dalili na na ficewa daga ADC – Peter Obi

May 3, 2026
Shettima ya ƙaddamar da jigilar maniyyatan Hajjin bana da kwashe alhazai 500 a Abuja
Labarai

Shettima ya ƙaddamar da jigilar maniyyatan Hajjin bana da kwashe alhazai 500 a Abuja

May 3, 2026
Binani ta fice daga ADC ta koma NDC watanni tara bayan barin APC
Siyasa

Binani ta fice daga ADC ta koma NDC watanni tara bayan barin APC

May 1, 2026
Next Post
Ƙarin Girma ‘Yan Sanda: Kwamishinoni 12 sun zama AIG, Kuma An Ɗaga Wasu Jami’an Zuwa Sama

Ƙarin Girma 'Yan Sanda: Kwamishinoni 12 sun zama AIG, Kuma An Ɗaga Wasu Jami'an Zuwa Sama

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!