ƘUNGIYAR Jama’atu Izalatil Bid’a Wa Iƙamatis Sunnah, ɓangaren Sheikh Abdullahi Bala Lau, ta bayyana cewa hukuncin da Kotun ECOWAS ta yanke kan dokar hana saɓo a Jihar Kano karan-tsaye ne kai-tsaye ga tsarkin addinin Musulunci.
A sanarwar da ƙungiyar ta bayar a yau, mai ɗauke da sa-hannun Shugaban ta, Sheikh Abdullahi Bala Lau, da Sakatare, Sheikh Muhammad Kabiru H. Gombe, Izala ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da kada ta nemi sauya dokar hana saɓo a Jihar Kano.
Ga cikakkiyar takardar sanarwar da Izala ɗin ta fitar:
Matsayin mu dangane da hukuncin da Kotun ECOWAS ta yanke kan sashi na 210 da 382(b) na dokar hukunta laifuka ta Jihar Kano da dokar shari’ar Musulunci (2000).
Jama’atu Izalatil Bid’a Wa Iqamatis Sunnah, JIBWIS Nigeria, ƙarƙashin jagorancin Sheikh Dr Abdullahi Bala Lau, na bayyana matuƙar damuwa da ƙin amincewa da hukuncin da Kotun ECOWAS ta yanke a ranar 9 ga Afrilu, 2025, wanda ke buƙatar gwamnatin Tarayyar Najeriya ta soke ko ta gyara sashe na 210 da 382(b) na dokokin Jihar Kano.
Wannan hukuncin, wanda ke cewa dokokin sun ci karo da haƙƙin ɗan’adam, tsoma baki ne da bai dace ba cikin ikon ƙasa na Najeriya wajen tsara dokoki, kuma karan-tsaye ne kai-tsaye ga tsarkin addinin Musulunci musamman a Jihar Kano, inda kashi 99% na al’ummar Musulmi ne.
Muna so mu bayyana abubuwan nan kamar haka:
1. Goyon bayan kundin tsarin mulki:
Sashe na 38(1) na kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 (wanda aka gyara) ya bayar da haƙƙin walwala da bin addini. Wannan ya haɗa da ‘yancin aiwatar da dokokin addini bisa ga abin da mutum ya yi imani da shi.
Bugu da ƙari, sashe na 4(7) na kundin tsarin mulkin ya bai wa majalisun dokoki na jihohi damar tsara dokoki a kan abubuwan da suka shafi laifuka. Don haka, ƙirƙirar dokar shari’ar Musulunci ta Jihar Kano da sashe na 382(b) ya yi daidai da kundin tsarin mulki kuma ya dace da haƙƙi da kuma damar ƙirƙirar dokar da ta dace da al’ada da addini ga gwamnatin Jahar Kano
2. Tsarkin Addini:
Sashe na 382(b) na dokar shari’ar Musulunci wanda ke hukunta wanda ya zagi ko ya ɓata suna ga Annabi Muhammad (SAW) da hukuncin kisa ya samo asali ne daga Alƙur’ani mai girma da sunnonin Annabi (SAW).
Kare mutuncin Annabi Muhammad (SAW) wani ɓangare ne da ba za a taɓa sassauci da shi ba a cikin addinin Musulunci. Zagin Annabi ba ‘yancin faɗar albarkacin baki ba ne, babban laifi ne da ke barazana ga zaman lafiya da ɗorewar dangantakar addinai.
3. Yarda daga Jama’a:
Dokar shari’ar Musulunci ba an ɗora wa mutane ba ne, sai da amincewa da kuma goyon bayan al’umma da tsarin dimokuraɗiyya da kuma kundin tsarin mulki. Duk wani yunƙuri na gyara ko soke dokar yana ƙetare ‘yancin addini da tsarin mulki na mutanen Jahar Kano.
4. Girmama bambancin addinai:
Haƙƙin ɗan’adam na gaskiya da ƙa’idodin ƙasa da ƙasa suna buƙatar a girmama bambancin addinai da ikon al’ummomin addini.
Hukuncin Kotun ECOWAS maimakon ya kare haƙƙi yana ƙarfafa tada hankali da rushe tsarin dokokin addini da ke daidaita da tsarin tarayya na Najeriya.
Saboda haka, muna roƙon gwamnatin Tarayyar Najeriya da ta ƙi amincewa da wannan hukunci tare da kare ‘yancin addini da tsarin mulki na mutanen Jihar Kano da sauran jihohin da Musulunci ya fi rinjaye.
Muna kuma kira ga dukkan Musulmai da su zauna lafiya, su bi doka, kuma su ci gaba da aiwatar da addinin Musulunci kamar yadda Allah (SWT) ya umarta a cikin Alƙur’ani da yadda Annabi Muhammad (SAW) ya nuna a rayuwarsa.
JIBWIS Nigeria, ƙarƙashin Sheikh Abdullahi Bala Lau, ta tsaya daram wajen kare addinin mu, dokokin mu da Annabi Muhammad (SAW), kuma za mu ci gaba da ƙin yarda da duk wani yunƙuri ko ƙoƙari da ke neman wulaƙanta imanin mu da ƙimar mu a matsayin Musulmai a Najeriya.
Sa hannu:
Sheikh Abdullahi Bala Lau, Shugaba
Sheikh Muhd. Kabiru H. Gombe, Sakatare
Jama’atu Izalatil Bid’a Wa Iqamatis Sunnah, JIBWIS Nigeria.
JIBWIS Nigeria







