• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Saturday, November 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Gwamnatin Tarayya ta fara raba kayan noma kyauta a Neja

Wakilin Mu by Wakilin Mu
September 13, 2025
in Labarai
A A
0
Gwamnatin Tarayya ta fara raba kayan noma kyauta a Neja
Tarin wasu daga cikin kayan da aka raba wa manoman Neja

Tarin wasu daga cikin kayan da aka raba wa manoman Neja

Gwamnatin Tarayya ta fara rabon kayan noma kyauta ga ƙananan manoma a Jihar Neja domin ƙarfafa noman ko wane lokaci na shekara da kuma bunƙasa samar da abinci.

Ƙaramin Ministan Aikin Gona da samar da Abinci, Dakta Aliyu Sabi Abdullahi, ya ce wannan shiri wani ɓangare ne na manufofin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu na tabbatar da wadatar abinci da kuma tsaron abinci a Nijeriya.

Kayan da ake rabawa sun haɗa da taki, magungunan kashe ƙwari, iri, sinadaran bunƙasa amfanin gona, injinan feshi da sauran kayayyakin da za su taimaka wa manoma. Za a ci gaba da raba irin waɗannan kayan a jihohi 36 da kuma Babban Birnin Tarayya.

Ministan ya jinjina wa Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, bisa nasarorin da jihar ta samu a fannin noma, lamarin da ya ce ya sanya ta zama abin koyi wajen aiwatar da shirye-shiryen gwamnati.

Babban Sakataren Ma’aikatar Aikin Gona Da Samar Da Abinci ta Tarayya, Dakta Marcus O. Ogunbiyi, da Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, da Ƙaramin Ministan ma’aikatar, Dakta Aliyu Sabi Abdullahi, a lokacin ƙaddamar da shirin raba kayan aikin gona da iri, a Minna, Jihar Neja.

Shi ma gwamnan ya gode wa Shugaba Tinubu bisa tallafin da ya bayar, yana mai cewa shirin zai ƙarfafa gwiwar manoma kuma ya ba su damar dogaro da kan su.

Ya kuma bayyana cewa Jihar Neja ta samu damar fitar da irin waken  soya na dalar Amurka miliyan 2.2 zuwa ƙasashen waje, tare da shirin dawo da Bankin Tattalin Arzikin Ƙananan Manoma (Cooperative Bank) da naira biliyan 2 domin rage raɗaɗin rancen da ke da ruwa mai yawa.

Tags: Cooperative BankgonaGwamna Mohammed Umaru Bagokayan aikiMa'aikatar Aikin GonamanomaSanata Aliyu Sabi Abdullahitallafi
Previous Post

Etsu Nupe ginshiƙin zaman lafiya da haɗin kai ne a Nijeriya — Idris

Next Post

Sojoji sun bindige Babangida Kachalla,mataimakin kwamandan ’yan bindiga a Kogi

Related Posts

Al’ummar Shinkafi sun yi alƙawarin goyon bayan Tinubu, Dauda Lawal da sauran ’yan takarar APC a 2027
Siyasa

Al’ummar Shinkafi sun yi alƙawarin goyon bayan Tinubu, Dauda Lawal da sauran ’yan takarar APC a 2027

November 28, 2026
Zargin taɓa jikin Baturiya: Gwamnatin Katsina ta bayyana sunayen ‘yan kwamitin binciken Sarkin Daura
Labarai

Zargin taɓa jikin Baturiya: Gwamnatin Katsina ta bayyana sunayen ‘yan kwamitin binciken Sarkin Daura

November 25, 2026
Tinubu ya umurci sojoji su ƙara ƙaimi kan ’yan ta’adda a Arewa-Maso-Gabas domin ɗorewar zaman lafiya
Siyasa

Tinubu ya umurci sojoji su ƙara ƙaimi kan ’yan ta’adda a Arewa-Maso-Gabas domin ɗorewar zaman lafiya

November 25, 2026
Tinubu ya taya Atiku murnar cika shekaru 80
Siyasa

Tinubu ya taya Atiku murnar cika shekaru 80

November 25, 2026
Iƙirarin satar sauraron wayar NSA da na yi kalamin siyasa ne kawai, inji El-Rufai a kotu
Tsaro

Iƙirarin satar sauraron wayar NSA da na yi kalamin siyasa ne kawai, inji El-Rufai a kotu

November 25, 2026
Gwamnatin Katsina ta dakatar da Sarkin Daura, ta kafa kwamitin binciken zargin cin zarafin Baturiya da ake masa
Labarai

Gwamnatin Katsina ta dakatar da Sarkin Daura, ta kafa kwamitin binciken zargin cin zarafin Baturiya da ake masa

November 24, 2026
Next Post
Sojoji sun bindige Babangida Kachalla,mataimakin kwamandan ’yan bindiga a Kogi

Sojoji sun bindige Babangida Kachalla,mataimakin kwamandan ’yan bindiga a Kogi

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • November 2026
  • October 2026
  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!