• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, September 29, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN zai fito da tsarin magance yawan samun matsalolin kati da na’urar ATM

ASHAFA MURNAI BARKIYA by ASHAFA MURNAI BARKIYA
January 24, 2026
in Kuɗi Da Tattalin Arziki
A A
0
CBN zai fito da tsarin magance yawan samun matsalolin kati da na’urar ATM
Wani kwastoma yana cirar kuɗi daga ATM

Wani kwastoma yana cirar kuɗi daga ATM

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya bayyana shirin ƙaddamar da sabuwar dokar tsari da nufin daidaita fitar da katinan cire kuɗi da kuma ayyukan na’urorin ATM a bankunan Nijeriya, domin magance matsalolin cinkoso da wahalar samun kuɗi.

Gwamnan CBN, Yemi Cardoso, ya bayyana hakan ta hannun mai ba shi shawara na musamman, Fatai Karim, a wajen Taron Kwamitin Shugabannin Ayyukan Bankuna na shekarar 2026 da aka gudanar ranar Juma’a.

A cewar babban bankin, sabuwar dokar za ta tabbatar da cewa adadin katunan da bankuna ke fitarwa ya dace da yawan na’urorin ATM da suka girke, domin rage cinkoso, yawan lalacewar ATM, da rashin daidaiton samun kuɗi a faɗin ƙasar.

CBN ta bayyana cewa matsalolin lalacewar ATM akai-akai da ƙarancin kuɗi suna ci gaba da rage ƙarfin amincewar jama’a ga hanyoyin biyan kuɗi na zamani, duk da cewa mu’amalar kuɗi ta hanyar zamani na ƙaruwa cikin sauri a ɓangaren bankuna.

“Ba da daɗewa ba, Babban Bankin Nijeriya zai fito da wata sabuwar doka domin gyara da inganta wannan yanayi, musamman game da adadin katunan da bankuna ke fitarwa idan aka kwatanta da yawan ATM da suke tallafawa. Idan samun kuɗi ya gaza, ko saboda samun cikas da tangarɗar lalacewar ATM ko rashin daidaiton rarraba kuɗi, hakan na raunana amincewar tsarin biyan kuɗi gaba ɗaya,” inji bankin.

Cardoso ya ƙara da cewa, “CBN na tattaunawa da masu ruwa da tsaki a ɓangaren, kuma ana sa ran dokar za ta fara aiki cikin ‘yan watanni, mai yiyuwa kafin ƙarshen zango na biyu na shekarar 2026.

Ana sa ran wannan mataki zai inganta amincin ATM, ya daidaita rarraba kuɗi, tare da dawo da amincewar jama’a ga tsarin biyan kuɗi na zamani a Nijeriya, abin da zai amfani bankuna da kwastomomi a duk faɗin ƙasar.”

Tags: ATMCBNkuɗiOlayemi Cardoso
Previous Post

Gwamnatin Tarayya da Amurka za su haɗa kai don inganta ’yancin addini da ƙarfafa tsaro a Nijeriya

Next Post

Gyaran tsarin ilimi na Tinubu yana samar da damarmaki ga matasan Nijeriya – Minista

Related Posts

Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso

September 25, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN: Tasirin rage kuɗin ruwa zuwa kashi 23% ga ’yan kasuwa da ’yan Nijeriya

September 24, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Yadda Cardoso ya sauya fasalin CBN, ya saisaita manufofin kuɗi, ya daidaita tsare-tsaren tattalin arzikin Nijeriya

September 22, 2026
Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba

September 16, 2026
Tsakuren muhimman bayanai daga jawabin Gwamnan CBN a Taron Shugabannin Kamfanoni na 2026 wanda BusinessDay ta shirya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Lambar yabo daga NES ta tabbatar da ingancin manufofin CBN wajen tabbatar da daidaiton tattalin arziki — Cardoso

September 13, 2026
Shawarar CBN ga gwamnatocin jihohi: “A kiyaye bin ƙa’idojin kashe kuɗaɗe, a daina ciwo bashin alaƙaƙai
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN ya ƙara ba da fifikon sa-ido wajen daƙile hadahadar kuɗaɗen ɗaukar nauyin ta’addanci

September 9, 2026
Next Post
Gyaran tsarin ilimi na Tinubu yana samar da damarmaki ga matasan Nijeriya – Minista

Gyaran tsarin ilimi na Tinubu yana samar da damarmaki ga matasan Nijeriya – Minista

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!