Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta fara bincike kan zarge-zargen cin hanci da rashawa da ake yi wa Farouk Ahmed, tsohon Manajan Darakta na Hukumar Kula da Harkokin Man Fetur ta Midstream da Downstream ta Nijeriya (NMDPRA).
Wannan ya biyo bayan wata takardar ƙorafi da hamshaƙin ɗan kasuwa, Aliko Ɗangote, ya shigar a hukumar a makon jiya ta hannun lauyoyin sa.
A cewar wani babban jami’in EFCC a Abuja da ya yi magana da jaridar PUNCH bisa sharaɗin a sakaya sunan sa domin ba shi da izinin yin magana a bainar jama’a, ya ce: “Sun kawo mana ƙorafin, kuma an riga an fara bincike a kai. Aiki mai tsanani yana gudana game da lamarin.”
Ƙorafin da aka shigar kan Ahmed na zargin sa da amfani da muƙami ta hanyar da ba ta dace ba da kuma tara dukiya ta hanyar cin hanci, inda ake zargin ya kashe kimanin dala miliyan 5 wajen biyan kuɗin karatun sakandare a ƙasar Switzerland ga ’ya’yan sa huɗu — adadin da lauyoyin Ɗangote suka ce ya fi ƙarfin halastacciyar hanyar samun kuɗin wani jami’in gwamnati.
A cikin takardar shari’a da babban lauya Dakta O.J. Onoja ya sanya wa hannu, Ɗangote ya buƙaci EFCC, a ƙarƙashin jagorancin shugaban ta Olanipekun Olukoyede, da ta bincika tare da gurfanar da Ahmed gaban ƙuliya idan hujjoji suka tabbatar da zarge-zargen.
“Mun bayyana a sarari cewa hukumar tana da cikakken matsayi tare da hukumomin ’yan’uwan ta wajen gurfanar da laifukan kuɗi da na cin hanci da rashawa, kuma idan aka kafa hujjar farko (prima facie), kotuna ba sa jinkirin hukunta masu laifi,” inji abin da ke cikin takardar ƙorafin.
Lauyoyin Ɗangote sun kuma bayyana cewa shigar da ƙorafin ga EFCC ya biyo bayan janye irin wannan ƙorafi da aka shigar tun farko a hukumar ICPC—mataki na dabarar da aka ɗauka domin hanzarta aiwatar da shari’a.
Ko da yake Ɗangote ya janye ƙorafin daga ICPC, hukumar ta ce za ta ci gaba da nata binciken.
Zarge-zargen sun tayar da muhawara a tsakanin jama’a a ɓangaren harkar man fetur da iskar gas ta Nijeriya, wanda tuni ke fuskantar tsauraran bincike kan hanyoyin da ake bi wajen sa ido, hulɗa da masu zuba jari, da muradun tattalin arziki.
Ƙorafin Ɗangote ya jaddada damuwa kan yiwuwar rikicin muradun aiki da kuma sahihancin tsarin sa ido na hukumomi, musamman idan manyan jami’ai suna rayuwa fiye da abin da halastacciyar samun kuɗin su zai iya ɗauka.
Duk da ƙoƙarin da ’yan jarida suka yi na tuntuɓar kakakin EFCC, Dele Oyewale, domin samun martani a hukumance, ya ƙi yin tsokaci a lokacin da ake tattara rahoton, amma ya yi alƙawarin fitar da sanarwa.
Masu lura da harkokin shari’a sun ce sakamakon shari’ar na iya ta’allaƙa ne kan bayanan kuɗi, sanarwar kadarori, da kuma hujjojin karkatar da dukiya idan har akwai.







