• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Thursday, May 14, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai Siyasa

Ba da daɗewa ba Tinubu zai fara ciwo bashi har daga Opay da Moniepoint, inji Dino Melaye

Admin-content by Admin-content
September 9, 2025
in Siyasa
A A
0
Ba da daɗewa ba Tinubu zai fara ciwo bashi har daga Opay da Moniepoint, inji Dino Melaye

 

Tsohon sanatan Kogi, Dino Melaye, ya yi wa Shugaba Bola Tinubu shaguɓe cewa nan ba da daɗewa sai ya riƙa ciwa wa Najeriya bashi, har a Opay da Moniepoint.

 

Da yake bayyana ra’ayin sa dangane da kukan yawan basussukan da ake bin Nijeriya, bayan ƙorafin da Kakakin Majalisar Tarayya, Abbas Tajuddeen ya yi, Melaye ya nuna irin ganganci da kasadar da Majalisar Tarayya ta riƙa yi, wajen amincewa Tinubu na ciwo basussuka ba bisa ƙa’ida ba.

 

Ya yi tsokacin ne a tattaunawar sa da Arise TV, a ranar Litinin.

 

“Me ya sa shugaban ƙasa zai ƙara ciwo bashin biliyan 1.7 daga Bankin Duniya? Me ya sa kuma Majalisar Dattawa ta amince ya ciwo bashin Dala biliyan 21, har ma da wasu basussuka da nan gaba zai kai domin amincewa?”

 

Melaye ya ce a tarihin Nijeriya ba a taɓa yin gwamnatin da ta ciwo bashi kamar gwamnatin Tinubu ba.

 

“Nan ba da daɗewa ba har a Opay da Moniepoint sai Tinubu ya riƙa ciwo wa Nijeriya bashi.

 

Idan za a iya tunawa, a ranar Litinin New Citizen Hausa ta buga labarin yadda Kakakin Majalisar Tarayya, Abbas Tajuddeen, ya bayyana fargaba dangane da ɗimbin bashin da ake bin Nijeriya, yana mai gargaɗi cewa yawan bashin ya zarce adadin dokar ƙasa ta gindaya ciwowa fintinkau.

 

Ya ce a yanzu haka yawan bashin da yawan kuɗaɗen ruwan da ake biya na yin barazana ga kuɗaɗen shiga da waɗanda gwamnati ke kashewa wajen gudanar da ayyukan yau da kullum na wajibi, har ma ga ɗorewar tattalin arziki.

 

Da yake jawabi a ranar Litinin yayin buɗe taron shekara-shekara na 11, na Majalisar Kwamiti-kwamitin Masu Sa-ido Kan Harkokin Kuɗaɗe na Majalisun Ƙasashen Afrika ta Yamma (WAAPAC) a Majalisar Ƙasa, a Abuja, Abbas ya ce bashin da ake bin Nijeriya “ya kai maƙurar barazana.'” Sai ya yi kira a gaggauta kawo sauye-sauye wajen gyara tsari da ƙa’udojin ciwo basussuka, sannan kuma majalisa ta riƙa sa-ido kan ayyukan da gwamnati ke aiwatarwa.

 

“Zuwa ƙarshen watanni uku na farkon 2025, adadin bashin da ake bin Nijeriya ya kai Naira tiriliyan 149.39, kwatankwacin kusan Dala biliyan 97. Hakan kuwa ya nuna cewa adadin ya ƙaru daga Naira tiriliyan 121.7 da ake bin Nijeriya a 2024”. Cewar sa.

 

“Wani ƙarin abin damuwa shi ne idan aka ɗora adadin bashin bisa sikelin ƙarfin tattalin arziki na cikin gida, za a ga ya haura ƙa’idar adadin da doka ta ce a ciwo bashi ya kai kusan kashi 52 bisa 100. Domin dokar mu cewa ta yi kada fa bashin da aka ciwo ya haura kashi 40 bisa 100 na ƙarfin tattalin arzikin cikin gida, wanda dokar mu ta ce kada ya wuce haka.”

 

Ya ce saboda haka wannan abin damuwa ne matuƙar gaske. Sai ya yi kira a samar da sabbin ƙa’idoji kuma a riƙa sa-ido.

 

“Ya kamata kuɗaɗen da ake ciwowa bashi a riƙa ganin alfanun su ƙuru-ƙuru a fannin ayyukan raya ƙasa, kiwon lafiya, inganta ilmi da kuma masana’antu domin a samu ayyuka, sannan a rage fatara, talauci da raɗaɗin tsadar rayuwa. Amma yawan ciwo basussukan da ba su haifar da komai sai cin hanci da rashawa.”

Previous Post

Ƙwangen kuɗaɗen shiga: Majalisar Tarayya Ta Ƙwato Wa Nijeriya Naira Bilyan 200 – Hon Salam

Next Post

Buba Marwa, Mutum Mai Baiwa Da Jajircewa Ya Cika Shekara 72

Related Posts

An kama Bello Boɗejo, shugaban Fulani Kuma ɗan takarar kujerar Sanata na APC a Taraba
Siyasa

An miƙa ɗan takarar Sanata kuma shugaban Fulani, Bello Boɗejo ga EFCC

May 10, 2026
Tinubu ya taya Garo murnar zama mataimakin gwamnan Kano
Siyasa

Tinubu ya taya Garo murnar zama mataimakin gwamnan Kano

May 5, 2026
Shugaban NDC, Dickson ya yi wa Umar Arɗo raddi kan barazanar kai su kotu kan batun rajista
Siyasa

Shugaban NDC, Dickson ya yi wa Umar Arɗo raddi kan barazanar kai su kotu kan batun rajista

May 5, 2026
Kwankwaso da Obi sun koma NDC
Siyasa

Kwankwaso da Obi sun koma NDC

May 3, 2026
Dalili na na ficewa daga ADC – Peter Obi
Siyasa

Dalili na na ficewa daga ADC – Peter Obi

May 3, 2026
Binani ta fice daga ADC ta koma NDC watanni tara bayan barin APC
Siyasa

Binani ta fice daga ADC ta koma NDC watanni tara bayan barin APC

May 1, 2026
Next Post
Buba Marwa, Mutum Mai Baiwa Da Jajircewa Ya Cika Shekara 72

Buba Marwa, Mutum Mai Baiwa Da Jajircewa Ya Cika Shekara 72

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!