Gobara daga kogi, maganin ta Allah! Gwamnatin Tarayya ta gargaɗi mazauna jihohi 11 cewa ana sa ran za a kyara ruwan sama mai ƙarfi a tsakanin ranakun Alhamis da Asabar mai zuwa wanda ka iya haifar da bala’in ambaliya da ruguza wurare.
Cibiyar Gargaɗin Wuri ta Ƙasa (National Flood Early Warning Centre, NFEWC) wadda ke ƙarƙashin Ma’aikatar Muhalli ta Tarayya, ita ce ta fitar da sanarwar inda ta lissafa wuraren da ake jin abin zai shafa a jihohin Adamawa, Binuwai, Nasarawa, Taraba, Delta, Neja, Kebbi, Kano, Katsina, Sokoto, da Zamfara.
A cewar cibiyar, wuraren da al’amarin zai fi shafa su ne kamar haka:
- Adamawa: Ganye, Natubi
- Binuwai: Abinsi, Agyo, Gogo, Ito, Makurdi, Udoma, Ukpiam
- Nasarawa: Agima, Rukubi, Odogbo
- Taraba: Beli, Serti, Donga
- Delta: Umugboma, Umukwata, Abraka, Aboh, Okpo-Krika
- Neja: Rijau
- Kebbi: Riɓah
- Kano: Gwarzo, Ƙaraye
- Katsina: Jibiya
- Sokoto: Makira
- Zamfara: Ƙaura Namoda, Shinkafi, Maradun, Gusau, Anka, Bunguɗu
Cibiyar ta bayyana cewa yawan ruwa ya ƙaru matuƙa a kogunan Gongola, Kogin Kwara da Kogin Neja, wanda hakan na iya sa su yi ambaliya.
Ta ce: “Ana ba garuruwan da ke yankunan da ake ambaliya a Kogin Gongola har zuwa Numan, da waɗanda suke gefen kogunan Binuwai da Kwara har zuwa Lokoja, ƙwaƙƙwarar shawarar cewa su tashi daga inda suke ba tare da ɓata lokaci ba domin su ceci rayukan su.”

Gwamnatin ta nanata cewa ƙin tashi daga wuraren zai iya haifar da rasa rayuka, salwantar dukiya, lalacewar gonaki, da kuma ababen more rayuwa, musamman da yake gar yau jihohi da dama ba su gama murmurewa ba daga bala’in ambiyar ruwa da ta faru a bara.”
Cibiyar ta yi kira ga gwamnatocin jihohi, ƙananan hukumomi, da cibiyoyin rigakafin bala’in da su tashi tsaye su fara aiki don aikin ceton rai kuma su wayar da kan jama’a kan ɗaukar matakan da suka dace.
Nijeriya dai tana shan fama da bala’in ambaliya a ‘yan shekarun nan, inda a shekarar 2022 ta fuskanci bala’in ambaliya mafi girma a gomiyar shekaru masu yawa wanda ya tarwatsa sama mutum miliyan 1.4 tare da kashe mutum sama da 6000 a faɗin ƙasar nan.







