Gwamnatin Tarayya ta fara rabon kayan noma kyauta ga ƙananan manoma a Jihar Neja domin ƙarfafa noman ko wane lokaci na shekara da kuma bunƙasa samar da abinci.
Ƙaramin Ministan Aikin Gona da samar da Abinci, Dakta Aliyu Sabi Abdullahi, ya ce wannan shiri wani ɓangare ne na manufofin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu na tabbatar da wadatar abinci da kuma tsaron abinci a Nijeriya.
Kayan da ake rabawa sun haɗa da taki, magungunan kashe ƙwari, iri, sinadaran bunƙasa amfanin gona, injinan feshi da sauran kayayyakin da za su taimaka wa manoma. Za a ci gaba da raba irin waɗannan kayan a jihohi 36 da kuma Babban Birnin Tarayya.
Ministan ya jinjina wa Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, bisa nasarorin da jihar ta samu a fannin noma, lamarin da ya ce ya sanya ta zama abin koyi wajen aiwatar da shirye-shiryen gwamnati.

Shi ma gwamnan ya gode wa Shugaba Tinubu bisa tallafin da ya bayar, yana mai cewa shirin zai ƙarfafa gwiwar manoma kuma ya ba su damar dogaro da kan su.
Ya kuma bayyana cewa Jihar Neja ta samu damar fitar da irin waken soya na dalar Amurka miliyan 2.2 zuwa ƙasashen waje, tare da shirin dawo da Bankin Tattalin Arzikin Ƙananan Manoma (Cooperative Bank) da naira biliyan 2 domin rage raɗaɗin rancen da ke da ruwa mai yawa.







