Wata ƙididdiga ta nuna cewa Nijeriya ta jima ba ta ga bala’in ambaliyar ruwan sama irin na wannan shekarar ba, domin kuwa aƙalla mutum 165 aka tabbatar da mutuwar su, sannan sama da wasu ƙarin mutum 119,000 abin ya shafa a jihohi 19 ya zuwa ranar 16 ga Agusta, 2025.
An bayyana wannan ƙididdigar ne a shafin gidan talabijin na NTA na manhajar X da taken “2025 flood dashboard.”
A cewar ƙididdigar, mutum 82 suka ɓata ba a gan su ba, 138 suka samu rauni, yayin da 43,936 suka bar muhallin su sakamakon ambaliya.
Ambaliya ta ragargaji garuruwa, ta mamaye gidaje da gonaki da ababen more rayuwa. Ta tarwatsa ko lalata jimillar gidaje 8,594 , yayin da ta shafe gonaki 8,278 wanda hakan zai iya shafar ƙoƙarin samar da abinci a ƙasar nan.
A ƙididdigar, an lissafa waɗanda abin ya shafa kamar haka: ƙananan yara 53,314, mata 36,573, maza 24,600, dattawa 5,304, da naƙasassu 1,863. Wannan ya nuna damuwa mabambanta da ta hau kan waɗannan rukunoni na al’umma.
Jihohin da abin ya fi shafa su ne Kaduna, Borno Imo, Ribas, da Abiya.
Sauran jihohin da abin ya shafa su ne Adamawa, Akwa Ibom, Anambra, Bayelsa, Borno, Edo, Gombe, Imo, Jigawa, Kano, Kogi, Kwara, Neja, Ondo, Sokoto, da Gundumar Birnin Tarayya (FCT).
Gaba ɗaya, Ƙananan Hukumomi 43 ne bala’in ambaliyar ya fi shafa har abin ya fi ƙarfin jami’an su.
Masana sun yi kira ga hukumomin da abin ya shafa, wato gwamnatoci da ƙungiyoyi masu zaman kan su da su gaggauta kai kayan agaji kamar su abinci da magani da wurin kwana na wucin-gadi a wuraren da abin ya shafa.






