• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Saturday, November 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai Siyasa

Tinubu ya umurci sojoji su ƙara ƙaimi kan ’yan ta’adda a Arewa-Maso-Gabas domin ɗorewar zaman lafiya

* Yaƙin neman zaɓen APC a Maiduguri

ALI KANO by ALI KANO
November 25, 2026
in Siyasa
A A
0
Tinubu ya umurci sojoji su ƙara ƙaimi kan ’yan ta’adda a Arewa-Maso-Gabas domin ɗorewar zaman lafiya
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu yana jawabi a wurin gangamin yaƙin neman zaɓen APC a Maiduguri, Jihar Borno, yau Laraba

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu yana jawabi a wurin gangamin yaƙin neman zaɓen APC a Maiduguri, Jihar Borno, yau Laraba

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar da cewa gwamnatin sa za ta ci gaba da ƙoƙarin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a Arewa maso Gabas, tare da umurtar jami’an tsaro da su ƙara ƙaimi wajen fatattakar ’yan ta’addan da ke gudun hijira bayan hare-haren da ake kai musu.

Tinubu ya bayyana haka ne a Maiduguri, Jihar Borno, ranar Laraba, yayin gangamin yaƙin neman zaben APC, inda ya ce zaman lafiyar da aka samu a yankin sakamakon ƙoƙarin sojoji da haɗin kan al’umma za a tabbatar da ɗorewar sa tare da mayar da shi cikakken farfaɗowar tattalin arziki. Ya kuma yaba wa Gwamna Babagana Zulum bisa dawo da jihar kan turbar ci gaba, inda ya ce ya ƙaddamar da wasu ayyuka da suka haɗa da masaukin mata na NYSC da Cibiyar Taro ta Ƙasa da Ƙasa ta Borno.

Dandazon mahalarta taron APC a Maiduguri a yau
Tinubu da Shettima a wurin taron

Shugaban ƙasar ya buƙaci ’yan ta’adda da su miƙa wuya tare da ajiye makaman su, sannan ya tabbatar wa jami’an tsaro da ke yaƙi da ta’addanci cewa gwamnati za ta ƙara kula da walwala da jin daɗin iyalan su. Ya kuma ce za a ƙara ƙarfafa tattara bayanan sirri domin ceto ɗaliban da aka sace a Askira Uba, yana mai fatan za a kuɓutar da su cikin gaggawa. Tinubu ya danganta nasarorin tsaro da aka samu da haɗin kan shugabanni da al’ummar yankin.

A nasa jawabin, Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya yabawa Tinubu bisa tallafin da yake bai wa Borno da sauran jihohin Arewa maso Gabas, yana mai cewa ya kamata a ba shi damar ci gaba da mulki na wa’adi na biyu. Gwamna Zulum ma ya yaba da ayyukan gwamnatin tarayya, ciki har da jami’o’i, hanyoyi da sauran ababen more rayuwa, musamman hanyar Biu–Maiduguri. Ya kuma yaba wa NEDC bisa samar da motocin lantarki guda 10,000 ga yankin, yayin da shugaban APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya miƙa tutocin jam’iyyar ga ’yan takarar ta a jihar.

Tags: APCBornoKashim ShettimaShugaba Bola Ahmed Tinubuzaɓen 2027
Previous Post

Ƙananan ’yan kasuwa 5,000 ‘sun amfana da shirye-shiryen tallafi daban-daban na Gwamnatin Tarayya a Borno’

Next Post

Zargin taɓa jikin Baturiya: Gwamnatin Katsina ta bayyana sunayen ‘yan kwamitin binciken Sarkin Daura

Related Posts

Al’ummar Shinkafi sun yi alƙawarin goyon bayan Tinubu, Dauda Lawal da sauran ’yan takarar APC a 2027
Siyasa

Al’ummar Shinkafi sun yi alƙawarin goyon bayan Tinubu, Dauda Lawal da sauran ’yan takarar APC a 2027

November 28, 2026
Tinubu ya taya Atiku murnar cika shekaru 80
Siyasa

Tinubu ya taya Atiku murnar cika shekaru 80

November 25, 2026
Sanata Barau ya haɗa malamai sama da 2,000 domin tallata Tinubu, Gwamna Abba da ’yan takarar APC
Siyasa

Sanata Barau ya haɗa malamai sama da 2,000 domin tallata Tinubu, Gwamna Abba da ’yan takarar APC

November 24, 2026
Kwankwaso ya tura ni wajen Tinubu bayan mun yi alƙawarin komawa APC, inji Abba Yusuf
Siyasa

Kwankwaso ya tura ni wajen Tinubu bayan mun yi alƙawarin komawa APC, inji Abba Yusuf

November 23, 2026
Rikicin ADC: INEC ta bayyana dalilin da ya sa Mark da Aregbesola ke ci gaba da kasancewa a cikin bayanan ta, yayin da ɓangaren Nafiu Gombe ke nuna rashin amincewa
Siyasa

Rikicin ADC: INEC ta bayyana dalilin da ya sa Mark da Aregbesola ke ci gaba da kasancewa a cikin bayanan ta, yayin da ɓangaren Nafiu Gombe ke nuna rashin amincewa

November 20, 2026
Tinubu ya faɗaɗa jadawalin kamfen ɗin 2027 daga jihohi 12 zuwa 19 da Abuja
Siyasa

Tinubu ya faɗaɗa jadawalin kamfen ɗin 2027 daga jihohi 12 zuwa 19 da Abuja

November 18, 2026
Next Post
Zargin taɓa jikin Baturiya: Gwamnatin Katsina ta bayyana sunayen ‘yan kwamitin binciken Sarkin Daura

Zargin taɓa jikin Baturiya: Gwamnatin Katsina ta bayyana sunayen 'yan kwamitin binciken Sarkin Daura

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • November 2026
  • October 2026
  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!