• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Saturday, November 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

Ƙananan ’yan kasuwa 5,000 ‘sun amfana da shirye-shiryen tallafi daban-daban na Gwamnatin Tarayya a Borno’

WAKILIN MU by WAKILIN MU
November 25, 2026
in Kuɗi Da Tattalin Arziki
A A
0
Ƙananan ’yan kasuwa 5,000 ‘sun amfana da shirye-shiryen tallafi daban-daban na Gwamnatin Tarayya a Borno’
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, yana jawabi a wurin taron tattaunawa da masu sana’o’i da suka amfana da tallafi a Jihar Borno, a Maiduguri yau Laraba 

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, yana jawabi a wurin taron tattaunawa da masu sana’o’i da suka amfana da tallafi a Jihar Borno, a Maiduguri yau Laraba 

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya jaddada aniyar gwamnatin tarayya na tallafa wa ƙananan ’yan kasuwa da masu sana’o’i, yana mai bayyana su a matsayin ginshiƙin tattalin arzikin Nijeriya.

Shettima ya bayyana hakan ne yayin halartar taron MSME Clinics da da taron tattaunawa na masu sana’o’i da suka amfana da tallafi a Jihar Borno, inda ya ce gwamnati na ci gaba da ƙoƙarin samar da damarmaki da ƙarfafa harkokin kasuwanci.

Ya bayyana cewa an samu ci gaba mai ma’ana a ɓangaren ƙananan kasuwanci tun bayan hawan Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan mulki a shekarar 2023, yana mai jaddada cewa ƙarfafa ƙananan ’yan kasuwa na taimakawa wajen samar da ayyukan yi, rage talauci da bunƙasa tattalin arziki.

Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya ce ƙarfafa tattalin arzikin al’umma ya wuce magance talauci kawai, yana mai tabbatar da cewa gwamnatin sa za ta ci gaba da tallafa wa ƙananan ’yan kasuwa a matsayin wani muhimmin ɓangare na shirin sake gina jihar.

Dandazon mahalarta taron

Shi ma Ministan Masana’antu, Sanata John Owan Enoh, ya yaba wa ƙwazon da basirar masu sana’o’i wajen samar da ayyukan yi da taimakawa ci gaban tattalin arzikin ƙasa.

A nasa jawabin, Mai ba Shugaban Ƙasa shawara kan samar da ayyukan yi da ƙananan kasuwanci, Temitola Adekunle-Johnson, ya bayyana cewa an shirya taron ne domin tantance cigaban kasuwancin da suka samu tallafin gwamnati.

Ya bayyana cewa ƙananan ’yan kasuwa 5,000 a Jihar Borno sun amfana da shirye-shiryen tallafi daban-daban na gwamnatin tarayya, yana mai jaddada cewa za a ci gaba da ƙarfafa su domin faɗaɗa sana’o’insu da samar da ƙarin damarmakin tattalin arziki.

Tags: BornoKashim Shettimasana'o'i
Previous Post

Tinubu ya taya Atiku murnar cika shekaru 80

Next Post

Tinubu ya umurci sojoji su ƙara ƙaimi kan ’yan ta’adda a Arewa-Maso-Gabas domin ɗorewar zaman lafiya

Related Posts

Muna samun nasarori a tsaro, ilimi da ababen more rayuwa – Tinubu 
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Tinubu ya ware Naira biliyan 450 domin tallafa wa manoma 500,000

November 22, 2026
Tinubu ya bayyana shirin samar da motoci masu amfani da gas guda 300, tare da alƙawarin rage kuɗin sufuri da kashi 40
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Tinubu ya bayyana shirin samar da motoci masu amfani da gas guda 300, tare da alƙawarin rage kuɗin sufuri da kashi 40

November 19, 2026
CBN ya naɗa kamfanoni takwas domin kula da fitar da ɗanyen mai da iskar gas
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN da NNPCL sun ƙulla yarjejeniyar ƙarfafa tattalin arziki da samar da kuɗaɗen zuba jari a ɓangaren makamashi

November 18, 2026
CBN ya fitar da sabbin ƙa’idojin adana bayanan kwastomomi ga bankunan Access, Zenith, OPay, PalmPay da sauran su
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN ya fitar da sabbin ƙa’idojin adana bayanan kwastomomi ga bankunan Access, Zenith, OPay, PalmPay da sauran su

November 17, 2026
Hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ya ragu zuwa kashi 14.06 cikin 100 a watan Oktoba – NBS
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ya ragu zuwa kashi 14.06 cikin 100 a watan Oktoba – NBS

November 16, 2026
Kamfanin Ɗangote ya ƙaddamar da tirela mai amfani da lantarki ta farko da aka harhaɗa a Nijeriya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Kamfanin Ɗangote ya ƙaddamar da tirela mai amfani da lantarki ta farko da aka harhaɗa a Nijeriya

November 16, 2026
Next Post
Tinubu ya umurci sojoji su ƙara ƙaimi kan ’yan ta’adda a Arewa-Maso-Gabas domin ɗorewar zaman lafiya

Tinubu ya umurci sojoji su ƙara ƙaimi kan ’yan ta’adda a Arewa-Maso-Gabas domin ɗorewar zaman lafiya

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • November 2026
  • October 2026
  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!