Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kan ta ta Ƙasa (INEC) ta ce za ta dogara ne da hukuncin da Kotun Ɗaukaka Ƙara za ta yanke kan ƙarar da aka shigar a gaban ta, wajen ɗaukar matakin da ya dace kan rikicin shugabancin jam’iyyar ADC, bayan kotu ta soke shugabancin tsohon shugaban Majalisar Dattawa, David Mark.
Sai dai ɓangaren jam’iyyar da Nafiu Bala Gombe ke jagoranta ya buƙaci hukumar ta gaggauta aiwatar da hukuncin da Kotun Tarayya ta yanke, ta hanyar amincewa da shugabancin su da kuma cire sunayen Mark da tsohon Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola, daga bayanan hukumar.
Kwamishinan INEC na ƙasa, Mohammed Haruna, ya bayyana matsayar hukumar a ranar Laraba, inda ya ce an sanar da ita a hukumance game da ƙarar ɗaukaka da aka shigar, kuma za ta jira hukuncin kotun ɗaukaka ƙara kafin ta yanke shawarar matakin da za ta ɗauka.
“An riga an kai ƙarar Kotun Ɗaukaka Ƙara, sun riga sun ɗaukaka ƙara. An yi mana sanarwar ɗaukaka ƙarar, don haka ba za mu yi kamar ba mu san abin da ke faruwa ba,” in ji Haruna.
Ya ƙara da cewa, “Saboda haka, wannan shi kansa yana zama tamkar wani ma’auni, don haka dole ne mu jira hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara.”
Sai dai lauyan Gombe, wanda ƙarar da ya shigar ta haifar da hukuncin da ya shafi shugabancin Mark, ya dage cewa ya kamata INEC ta bi umarnin kotu da ke aiki a yanzu, maimakon jiran ƙarin wasiƙu ko sanarwa daga hukumar.
Ɗaya daga cikin lauyoyin Gombe, Haruna Musa, SAN, ya shaida wa jaridar The PUNCH cewa INEC ba ta amsa wasiƙar da shugaban ɓangaren ya rubuta mata ba.
Da aka tambaye shi ko hukumar ta amsa wasiƙar, Musa ya ce, “Ba tukuna ba.”
Sai dai ya jaddada cewa ba lallai ne hukumar ta amsa wasiƙar ba, abin da ya kamata ta yi shi ne aiwatar da umarnin kotu.
“Ba sai sun amsa ba, abin da ya kamata su yi shi ne su bi umarnin kotu,” inji shi.
Da aka tambaye shi inda Gombe zai gudanar da ayyukan sa, ganin zargin cewa ginin hedikwatar ADC na ƙasa mallakar tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar ne, Musa ya ce, “Ku tambaye shi (Nafiu Bala), mu mun yi namu aikin.”
A halin da ake ciki, Kwamitin Amintattu (BoT) na ADC da Gombe ke jagoranta ya buƙaci INEC ta gaggauta aiwatar da hukuncin Kotun Tarayya na ranar 5 ga Nuwamba, 2026, kan rikicin shugabancin jam’iyyar.
Kwamitin ya kuma buƙaci hukumar ta cire sunayen Mark da Aregbesola daga bayanan da take da su na shugabannin jam’iyyar, tare da cire sunayen ’yan takarar da shugabancin Mark ya ɗora a shafin ta.
A cikin wata sanarwa da shugaban kwamitin, Cif Rufus Ikanmi, ya fitar, ya ce hukuncin da Mai Shari’a Peter Lifu ya yanke a ƙarƙashin ƙarar mai lamba FHC/ABJ/CS/1819/2025, wadda Hon. Nafi’u Bala Gombe ya shigar a kan ADC da wasu mutum huɗu, yana nan daram kuma yana da cikakken ƙarfi a hukumance.
Ikanmi ya ce, “Hukuncin kotun mai girma yana da inganci, yana da ɗauri kuma yana nan a kan aiki. Babu wata babbar kotu da ta dakatar da shi, ta sauya shi ko ta soke shi. INEC, a matsayin ta na hukumar da doka ta kafa kuma doka ta ɗaure ta, tana da nauyin kundin tsarin mulki na aiwatar da shi gaba ɗaya ba tare da wani ƙarin jinkiri ba.”
Ya buƙaci hukumar ta amince da shugabancin Gombe tare da yin mu’amala da shi kaɗai, wanda ya ce kotu ta tabbatar da halaccin sa.
Musamman, ya buƙaci INEC ta gaggauta cire sunayen shugabancin Mark da Aregbesola daga bayanan hukumar a matsayin shugabannin ADC, tare da cire dukkan ’yan takarar da ɓangaren ya ɗora a shafin ta.
Kwamitin ya yi zargin cewa an ɗora waɗannan sunaye ne ta hanyar karya Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Nijeriya (wanda aka yi wa gyara), Dokar Zaɓe ta 2022 da kuma kundin tsarin mulkin jam’iyyar.
Haka kuma, ya buƙaci tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, da sauran mutanen da ake zargin suna aiki tare da shugabancin Mark, da su dakatar da ayyukan yaƙin neman zaɓe, tarurruka da sauran harkokin jama’a da suke gudanarwa da sunan ADC, har sai an bi hukuncin kotun.
Ikanmi ya ce, “Duk wani ci gaba da bijire wa hukuncin Kotun Tarayya yana zama raina kotu, tare da kai hari kai tsaye ga dimokuraɗiyya mai bin kundin tsarin mulki da bin doka.”
Kwamitin ya yi kira ga ’yan jam’iyyar da magoya bayan ta da su kasance cikin natsuwa da bin doka, yana mai cewa yana da ƙudirin tabbatar da zaman lafiya, haɗin kai da bin tsarin kundin tsarin mulkin jam’iyyar.
Rikicin ya samo asali ne daga hukuncin Kotun Tarayya da ke Abuja, wadda ta soke shugabancin ADC da Mark ke jagoranta, tare da rushe wasu matakai da aka ɗauka ƙarƙashin kwamitin riƙon ƙwarya, ciki har da tsarin da ya samar da Atiku a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar a zaɓen 2027.
Mai Shari’a Lifu ya bayyana Kwamitin Riƙon Ƙwarya da Mark ke jagoranta a matsayin wanda ba bisa doka ba, tare da soke tsarin da ya gudanar na zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa.
Kotun ta kuma soke zaɓen Aregbesola a matsayin Sakataren Ƙasa, da na sauran jami’an ƙasa da aka naɗa, tare da soke zaɓen ’yan takarar da jam’iyyar ta gabatar domin zaɓen 2027.
Hukuncin ya biyo bayan ƙarar mai lamba FHC/ABJ/CS/1819/2025, wadda Gombe, tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa na ADC a Arewa maso Gabas, ya shigar. Ya ƙalubalanci tsarin da Mark da sauran mambobin kwamitin riƙon ƙwarya suka bi wajen karɓar shugabancin jam’iyyar.
Gombe ya yi iƙirarin cewa bayan tsohon shugaban jam’iyyar na ƙasa, Ralph Nwosu, ya yi murabus, kundin tsarin mulkin jam’iyyar ya ba shi damar karɓar shugabancin jam’iyyar.
Saboda haka, ya buƙaci kotu ta soke matakan da shugabancin Mark ya ɗauka, tare da hana Mark da Aregbesola bayyana kan su a matsayin shugaban ƙasa da sakataren ƙasa na jam’iyyar, bi da bi.
Da ta amince da ƙarar Gombe, Mai Shari’a Lifu ya ce samuwar shugabancin Mark ya saɓa wa kundin tsarin mulkin ADC, wasu tanade-tanaden Dokar Zaɓe da kuma Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya na 1999.
Alƙalin ya kuma umarci INEC da kada ta amince da matakan da aka ɗauka a taron Kwamitin Zartarwa na Ƙasa (NEC) na jam’iyyar karo na 99, wanda aka gudanar a ranar 27 ga Yuli, 2025, ko ta yi aiki da su.
Sai dai shugabancin ADC da Mark ke jagoranta ya ɗaukaka ƙara kan hukuncin, tare da bayyana cewa ya shigar da buƙatar dakatar da aiwatar da hukuncin har sai an saurari ƙarar ɗaukaka ƙara kuma an yanke hukunci a kanta.
Wani rahoto da Arise News ta fitar a ranar Alhamis, wanda ya dogara da bayanin wani babban jami’in hukumar, ya ce ci gaba da kasancewar ’yan takarar a cikin bayanan hukumar na da alaƙa da sanarwar ɗaukaka ƙara da kuma buƙatar dakatar da aiwatar da hukuncin da aka shigar dangane da hukuncin kotun.
Rahoton ya ƙara da cewa hukumar ba za ta iya yin watsi da ƙarar da ke gaban Kotun Ɗaukaka Ƙara ba yayin da take nazarin buƙatun neman amincewa da shugabanci da suka samo asali daga hukuncin Kotun Tarayya.







