Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana shirin samar da motocin bas masu amfani da iskar gas (CNG) guda 300, a ƙarƙashin shirin National Affordable CNG Transit Programme domin rage kuɗin sufuri da sauƙaƙa wa ‘yan Najeriya matsin tattalin arziki.
Shugaban ya ce kamfanin Yutong, wanda shi ne mafi girman kamfanin ƙera motocin bas a duniya, zai kafa masana’antar haɗa motocin bas masu amfani da CNG a tsohuwar masana’antar Leyland da ke Ibadan, Jihar Oyo.
A cikin wani saƙo da ya wallafa a soshiyal midiya ranar Alhamis, Tinubu ya bayyana cewa Yutong zai samar da motocin bas 300 na farko bisa yarjejeniyar da ya ƙulla da Shirin Shugaban Ƙasa na CNG da Motocin Lantarki (Pi-CNG & EV), inda ake sa ran motocin farko guda 100 za su iso tun farkon watan gobe.
Ya ƙara da cewa sauran motocin za a riƙa haɗa su a Ibadan ta hannun kamfanin YP Automobiles, matakin da zai samar da ayyukan yi ga injiniyoyi, ƙwararrun masu fasaha da sauran ma’aikata.
Tinubu ya ce shirin ya fara haifar da sakamako mai ƙarfafa gwiwa a aƙalla jihohi 10 da Babban Birnin Tarayya Abuja, inda aka samu raguwar kuɗin sufuri a wasu hanyoyi.
A cewar sa, tafiyar daga Inugu zuwa Nsukka, wadda a baya ake biyan naira 4,000, yanzu ana biyan naira 1,600 a motocin bas masu amfani da CNG da ke cikin shirin.
Ya kuma ce a Jihar Borno ana samun kuɗin hawa bas na naira 50, yayin da a Kaduna ake gudanar da zirga-zirgar motocin bas na CNG kyauta.
Shugaban ya ce ƙarin ‘yan Najeriya za su amfana da shirin yayin da gwamnatocin jihohi ke ci gaba da sayen motocin CNG, sannan masu zuba jari a kamfanoni masu zaman kan su ke faɗaɗa cibiyoyin cika iskar gas a ƙasar.
Ya bayyana cewa umurnin da ya bayar na samar da ƙarin cibiyoyin cika iskar gas guda 2,000 a faɗin ƙasar nan zai ƙara taimakawa wajen faɗaɗa shirin.
Tinubu ya kuma bayyana cewa a cikin tsarin “Reforms to Prosperity Agenda” na shekarar 2027 zuwa 2031, ya yi alƙawarin rage kuɗin sufuri da kusan kashi 40 cikin 100 a hanyoyin da shirin ya shafa, inda ya ce an fara shirye-shiryen aiwatar da wannan buri.
Ya ce Najeriya na da albarkatun iskar gas masu yawa, waɗanda ya kamata a yi amfani da su wajen samar da sufuri mai sauƙin kuɗi ga ‘yan ƙasa, musamman ‘yan kasuwa, ma’aikata, ɗalibai da iyalai da ke fama da tsadar rayuwa.
Shugaban ya jaddada cewa gwamnati na ƙoƙarin tabbatar da cewa sauye-sauyen tattalin arzikin da take aiwatarwa sun haifar da ingantacciyar rayuwa ga ‘yan Najeriya, yana mai cewa ba za a koma tsarin da zamba wajen neman tallafin mai ke wadatar da ‘yan tsaka-tsaki yayin da talakawa ke shan wahala ba.
Ya ce babban burin shirin shi ne tabbatar da cewa ‘yan Najeriya suna kashe kuɗi kaɗan wajen sufuri, suna samun abin da ya dace da aikin su, sannan su samu isasshen abin tallafa wa iyalan su.







