Babban Bankin Nijeriya (CBN) da Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPCL) sun ƙulla yarjejeniyar fahimtar juna (MoU) da nufin ƙarfafa daidaiton tattalin arziki, inganta shigar kuɗaɗen musayar ƙasashen waje da faɗaɗa hanyoyin samun kuɗaɗen zuba jari a ɓangaren makamashi.
An rattaba hannu kan yarjejeniyar a hedikwatar CBN da ke Abuja a ranar Laraba, 18 ga Nuwamba, 2026, domin samar da tsayayyen tsarin haɗin gwiwa tsakanin cibiyoyin biyu wajen bunƙasa tattalin arzikin Nijeriya da tabbatar da daidaiton sa na dogon lokaci.
Da yake jawabi a wajen bikin sanya hannu kan yarjejeniyar, Gwamnan CBN, Mista Olayemi Cardoso, ya ce haɗin gwiwar zai ƙarfafa tafiyar da tattalin arzikin ƙasa, inganta shigar kuɗaɗen musayar ƙasashen waje da kuma taimakawa wajen tabbatar da ɗorewar tattalin arzikin ƙasar.
Cardoso ya bayyana yarjejeniyar a matsayin wani muhimmin mataki a dangantakar haɗin gwiwa da ta daɗe tsakanin cibiyoyin biyu, yana mai cewa rawar da kowannen su ke takawa wajen samar da kuɗaɗen shiga ga gwamnati, ƙarfafa ajiyar kuɗaɗen ƙasashen waje da samar da kuɗaɗen musayar ƙasashen waje na nuna muhimmancin ƙarfafa haɗin gwiwar su.
Ya ce yarjejeniyar za ta inganta yadda ake tafiyar da kuɗaɗen da ake samu daga cinikin mai da iskar gas, tabbatar da samun kuɗaɗen musayar ƙasashen waje a kai a kai, da kuma zurfafa haɗin gwiwa wajen samar da kuɗaɗen gudanar da ayyukan makamashi, cin moriyar kadarorin man fetur da iskar gas da samar da tallafin kuɗi.
A cewar sa, haɗin gwiwar zai kuma yi amfani da matsayin CBN wajen haɗa kan manyan cibiyoyin kuɗi na duniya domin samar da hanyoyin samun kuɗaɗen zuba jari da za su taimaka wajen amfani da ɗimbin arzikin iskar gas da Nijeriya ke da shi.
Sauran fannoni da yarjejeniyar ta ƙunsa sun haɗa da sarrafa harkokin biyan kuɗi ta na’ura, haɗa tsarin baitulmalin cibiyoyin biyu, daidaita dokoki da ƙa’idoji, kula da haɗurra, tsaron na’urorin sadarwa da bayanai, da inganta ƙwarewar ma’aikata.
Cardoso ya bayyana cewa kafa kwamitocin gudanarwa da na aiki tare zai taimaka wajen daidaita ayyukan cibiyoyin biyu, bibiyar aiwatar da yarjejeniyar da tabbatar da cimma manufofin da suka sanya a gaba.
Ya jaddada cewa yarjejeniyar ba ta ƙirƙiro sabuwar dangantaka ba ce, sai dai ta mayar da haɗin gwiwar da aka daɗe ana yi tsakanin cibiyoyin biyu zuwa tsayayyen tsari na hukuma.
Ya bayyana tabbacin cewa ƙarfafa haɗin gwiwar zai taimaka wajen tabbatar da daidaiton tattalin arziki, ƙara amincewar masu zuba jari da samar da ingantaccen tubalin bunƙasar tattalin arziki mai ɗorewa.
A nasa jawabin, Babban Daraktan NNPCL, Mista Bayo Ojulari, ya bayyana yarjejeniyar a matsayin wani tsari na dabarun haɗa ɓangarorin makamashi da kuɗi domin tallafa wa bunƙasar tattalin arzikin Nijeriya da tabbatar da daidaiton sa.
Ojulari ya ce muhimmiyar rawar da man fetur da iskar gas ke takawa wajen samar da kuɗaɗen musayar ƙasashen waje ga Nijeriya na nuna buƙatar ƙarfafa alaƙa tsakanin ɓangaren makamashi da tsarin hada-hadar kuɗi na ƙasar.
Ya bayyana cewa sauyin da NNPCL ya samu zuwa kamfani mai tafiyar da harkokin sa bisa tsarin kasuwanci, ƙarƙashin Dokar Masana’antar Man Fetur (Petroleum Industry Act), ya ƙara muhimmancin samar da ingantacciyar dangantaka mai bayyana gaskiya tsakanin kamfanin da CBN.
Ya ce yarjejeniyar za ta taimaka wajen ƙarfafa kuɗaɗen shigar da ake samu daga fitar da mai zuwa ƙasashen waje, inganta shigar kuɗaɗen musayar ƙasashen waje da kuma daidaita ayyukan kamfanin da manufofin ƙasa na harkokin kuɗi da makamashi.
Babban Daraktan ya ƙara da cewa yarjejeniyar za ta ba kamfanin damar amfani da kadarorin sa da ƙarfin kuɗin sa wajen neman jarin gudanar da ayyuka, yayin da tsarin shugabanci na haɗin gwiwa da ma’aunin tantance nasarori za su tabbatar da ingantaccen aiwatar da yarjejeniyar.
Tun da farko, Mataimakiyar Gwamnan CBN mai kula da Ayyuka, Misis Emem Usoro, ta bayyana yarjejeniyar a matsayin wani muhimmin mataki na zurfafa haɗin gwiwar da ke tsakanin cibiyoyin biyu.
Ta ce yarjejeniyar ta samar da tsarin haɗin gwiwa a fannonin kasuwancin ƙasashen waje, shigar kuɗaɗen musayar ƙasashen waje, samar da kuɗaɗen ayyukan makamashi, cin moriyar arzikin man fetur da iskar gas, da daidaita dokoki da kula da haɗurra.
Usoro ta bayyana cewa ajiyar kuɗaɗen Nijeriya a ƙasashen waje ta haura dala biliyan 55 a ‘yan kwanakin nan, sakamakon ƙarin yawan man da ake haƙowa da kuma ci gaba da shigowar kuɗaɗen da ‘yan Nijeriya mazauna ƙasashen waje ke aikowa gida.
Ta nuna tabbacin cewa haɗin gwiwar zai ƙara ƙarfafa kuɗaɗen shigar da ake samu daga fitar da kayayyaki zuwa ƙasashen waje, inganta shigar kuɗaɗen musayar ƙasashen waje da kuma ƙara wa Nijeriya ƙarfin jure matsin tattalin arzikin duniya.
Shi ma da yake jawabi, Babban Jami’in Kuɗi na NNPCL, Mista Adedapo Segun, ya ce yarjejeniyar za ta maye gurbin tattaunawa da hulɗar da ba ta da tsayayyen tsari tsakanin cibiyoyin biyu da ingantaccen tsarin haɗin gwiwa mai gaskiya da riƙon amana.
Segun ya ce haɗin gwiwar zai taimaka wajen ƙarfafa ajiyar kuɗaɗen ƙasashen waje, inganta amincewar masu zuba jari, tabbatar da daidaiton darajar Naira da kuma bunƙasa amfani da Naira maimakon dogaro da dalar Amurka ta hanyar daidaita ayyukan kamfanin da manufofin CBN.
Ya ƙara da cewa haɗin gwiwar zai taimaka wajen inganta tsarin biyan kuɗi, amfani da fasaha da bunƙasa sabbin hanyoyin gudanar da harkokin kuɗi ta na’ura.
A cewar sa, haɗin gwiwar zai kuma tallafa wa ƙoƙarin NNPCL na ƙara yawan man da Nijeriya ke haƙowa daga ganga miliyan 1.8 zuwa miliyan uku a kowace rana, tare da hanzarta amfani da arzikin iskar gas na ƙasar.
Ya ce ƙungiyoyin aiki da aka amince da su, jadawalin aiwatar da ayyuka da tsarin ɗora alhaki za su jagoranci aiwatar da yarjejeniyar.
Babban abin da ya fi ɗaukar hankali a wajen taron shi ne rattaba hannu kan yarjejeniyar da Cardoso da Ojulari suka yi a hukumance, a gaban jami’an cibiyoyin biyu.







