An yi wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu eho a Babban Masallacin Shehu Shagari da ke Abuja a jiya, jim kaɗan bayan ya gudanar da sallar Juma’a.
Bidiyoyi da dama da suka yaɗu a jiya sun nuna matasa suka riƙa rera taken adawa da shugaban ƙasar yayin da ayarin sa ke barin masallacin.
Wani ganau da ya halarci sallar ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa ƙila takunkumin da aka sanya wa masu ibada saboda ziyarar shugaban ne ya haddasa zanga-zangar.
Shaidan, wanda ya nemi a ɓoye sunan sa, ya ce Shugaba Tinubu ya isa masallacin da misalin ƙarfe 1:49 na rana, kuma a lokacin an riga an hana shiga harabar masallacin.
A cewar majiyar, jami’an tsaro sun hana mutane shiga masallacin bayan shugaban ya iso. An kuma toshe hanyoyin da ke kaiwa masallacin, yayin da wasu jami’an tsaron suka hau katangar masallacin a matsayin wani ɓangare na tsare-tsaren tsaro.
Shaidan ya ce takunkumin ya ci gaba bayan sallah, inda aka hana masu ibada fita har sai da shugaban ya tafi.
Majiyar ta ce wasu mutane sun bayyana fushin su ta hanyar rera, “Ba mayi, ba ma so.”
Wasu kuma sun rera “Tinubu Must Go” (Dole Tinubu ya tafi), taken da ake alaƙantawa da adawa da neman sake zaɓen sa.
Wata majiya ta daban a masallacin ita ma ta alaƙanta ehon, a wani ɓangare, da tsare-tsaren tsaron da ta bayyana a matsayin masu yawa fiye da ƙima.
“An hana mutane shiga masallacin bayan shugaban ya shiga. Mutane da yawa sun maƙale a waje,” inji majiyar.
Majiyar ta ƙara da cewa an hana masu ibada fita har sai da Tinubu ya tafi, kuma ehon ya fara ne daga wurin da aka kange mutane.
Lamarin ya faru ne a daidai lokacin da shugaban ke fuskantar ƙaruwar gasar siyasa gabanin zaɓen shugaban ƙasa mai zuwa.
Kakakin shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, bai amsa kira ba har zuwa lokacin da aka rubuta wannan rahoto.
A yayin sallar, Babban Limamin Masallacin Shehu Shagari, Area 1, Garki, Sheikh Rabi’u Suleiman, ya gabatar da huɗuba ne bisa darussa daga Suratul Fatiha, babi na farko a Alƙur’ani.
Limamin ya yi kira ga Musulmi da su riƙe Allah ɗaya, su nemi dagewa ta wurin sa.
Ya kuma yi addu’ar neman zaman lafiya da lafiyar shugaban ƙasa, yana roƙon Allah ya ba Tinubu ƙarin hikima kuma ya shiryar da shi wajen jagorantar Nijeriya zuwa wadata.
Sheikh Rabi’u Suleiman ya yaba da gudunmawar da shugaban ƙasar ya bayar wajen gyaran masallacin.
Shugaban ya samu rakiyar Mai Ba da Shawara kan Harkokin Tsaron Ƙasa, Malam Nuhu Ribaɗu; da Mai Ba shi Shawara na Musamman kan Harkokin Siyasa, Alhaji Ibrahim Masari; da Shugaban Ma’aikata, Hon. Femi Gbajabiamila; da tsohon Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje.







