Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya umurci hukumomin tsaro da su ɗauki tsauraran matakai kan masu aikata ta’addancin siyasa da sauran ayyukan da suka saɓa wa tsarin dimokiraɗiyya, yayin da ake tunkarar babban zaɓen 2027.
Shugaban ya kuma gargaɗi ‘yan siyasa da magoya bayan su da su guji duk wani nau’in tashin hankali.
Ya jaddada cewa gwamnatin sa ba za ta lamunci ayyukan da za su kawo cikas ga zaman lafiya da tsaron al’umma a lokacin yaƙin neman zaɓe ba.
Tinubu ya bayyana haka ne cikin wata sanarwa da fadar shugaban ƙasa ta fitar ranar Juma’a, bayan rahotannin tashe-tashen hankula da aka samu a wasu sassan ƙasar nan yayin harkokin siyasa.
Ya ce duk wani nau’in tashin hankali abin Allah-wadai ne, kuma bai kamata a same shi a yaƙin neman zaɓe ba yayin da ƙasar ke shirin zaɓen 2027.
Ya buƙaci jam’iyyun siyasa da ‘yan takara da su mayar da hankali kan gabatar da manufofi da ra’ayoyin da za su inganta rayuwar ‘yan Nijeriya da bunƙasa ƙasa, maimakon rikici da gaba da juna.
“Ni ne shugaban ƙasar nan, kuma na sha alwashin tabbatar da zaɓe cikin lumana, ‘yanci da adalci. Ina kira ga shugabannin siyasa da magoya bayan su a dukkan jam’iyyu da su kasance masu ɗa’a da sanin ya kamata,” inji shi.
Tinubu ya jaddada cewa bambancin jam’iyya ko burin neman wani muƙami bai kamata ya mayar da ‘yan siyasa abokan gaba ba, domin dukkan ‘yan Nijeriya al’umma ɗaya ce.
Ya ƙara da cewa dukkan jam’iyyun siyasa da ‘yan takarar su suna da ‘yancin yin yaƙin neman zaɓe a duk inda suke a faɗin ƙasar nan, ba tare da fuskantar barazana, tsangwama ko cin zarafi ba.
Shugaban ya ce ya ba hukumomin tsaro izinin yin amfani da cikakken ƙarfin su wajen fuskantar masu aikata ta’addancin siyasa da sauran ayyukan da ke barazana ga zaman lafiya da tsarin zaɓe.
Umurnin ya zo ne a lokacin da ake samun rahotannin hare-hare da tashe-tashen hankula a wasu wuraren harkokin siyasa a ƙasar nan, lamarin da ya ƙara nuna muhimmancin tabbatar da tsaro da zaman lafiya gabanin babban zaɓen 2027.







