• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Saturday, November 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai Siyasa

Neja za ta ba Tinubu da Bago babbar nasara a zaɓen 2027 – Idris

ABUBAKAR IBRAHIM by ABUBAKAR IBRAHIM
November 12, 2026
in Siyasa
A A
0
Neja za ta ba Tinubu da Bago babbar nasara a zaɓen 2027 – Idris
r

r

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Al’umma, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana tabbacin cewa Jihar Neja za ta kawo nasara mai ɗimbin yawa ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Gwamna Mohammed Umar Bago a babban zaɓen 2027.

Ya ambaci ƙaruwar goyon bayan da jam’iyyar APC take samu da kuma cigaban da aka samu a ƙarƙashin gwamnatocin biyu.

Ministan ya bayyana haka ne a wajen ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa da na gwamna na APC a Jihar Neja a Minna ranar Alhamis.

Shugabannin jam’iyya, masu ruwa da tsaki da magoya baya sun hallara a wurin domin fara shirye-shiryen jama’a a hukumance gabanin zaɓen.

Idris ya nuna farin cikin sa da yadda ‘ya’yan jam’iyya da magoya baya suka fito ƙwan su da kwarkwatar su.

Ya bayyana taron a matsayin babbar shaida ta ƙarfin APC tun daga ƙasa, da haɗin kan ta da kuma ƙaruwar karɓuwar ta a faɗin jihar.

Ya ce ƙwazon da membobin jam’iyyar suka nuna yana nuna amincewar su da shugabancin Shugaba Tinubu da Gwamna Bago, da kuma ƙudirin su na ci gaba da aiwatar da shirye-shiryen cigaba da ake yi a matakin tarayya da na jiha.

Ministan ya ce gwamnatin Tinubu ba ta kauce wa aiwatar da sauye-sauyen tattalin arziki masu zurfi ba, tana ƙarfafa kayayyakin more rayuwa na ƙasa, tana faɗaɗa damarmaki ga ‘yan Nijeriya, tare da kafa tubali mai ƙarfi na cigaban tattalin arziki mai ɗorewa da wadata.

Ya yaba wa Gwamna Bago bisa shirye-shiryen kawo cigaba na gwamnatin sa, musamman zuba jari a fannin kayayyakin more rayuwa da noma.

Ya ce waɗannan na taimakawa wajen sauya fasalin Jihar Neja da ƙarfafa matsayin ta mai muhimmanci a cigaban noma a Nijeriya.

Idris ya jaddada muhimmancin haɗin kai, ci gaba da tuntuɓar juna da kuma ingantaccen shirya jama’a a cikin jama’a tsakanin ‘ya’yan jam’iyya. Ya ce damar APC ta samun nasara a zaɓe za ta ƙaru ta hanyar iya bayyana nasarorin gwamnatocin biyu da kuma kasancewa kusa da al’umma a faɗin jihar.

Ya bayyana fatan cewa mutanen Jihar Neja za su sabunta wa Shugaba Tinubu da Gwamna Bago wa’adin su, a matsayin yabo ga shugabancin su da jajircewar su wajen kawo cigaba.

Da yake jawabi a taron, Gwamna Mohammed Umar Bago ya ce yana da tabbacin cewa nasarorin gwamnatin sa a cikin shekaru ukun da suka gabata za su sa mutanen Jihar Neja su ba shi wani wa’adi.

Gwamnan ya ce ayyukan gwamnatin sa a manyan fannoni za su yi magana da kan su a wajen zaɓe.

Ya kuma sake jaddada ƙudirin sa na tabbatar da nasara mai ƙarfi ga Shugaba Tinubu a jihar.

Ya bayyana cewa APC ce babbar siyasa mai ƙarfi a Jihar Neja, kuma yana da tabbaci kan ikon jam’iyyar na samun nasarori masu ɗimbin yawa a zaɓen 2027.

Haka kuma, Ministan Noma da Samar da Abinci na Jiha, Sen. Dakta Aliyu Sabi Abdullahi, ya jaddada muhimmancin Jihar Neja ga shirin Nijeriya na samar da abinci.

Ya ce zuba jarin gwamnatin Bago a fannin hanyoyi na inganta zirga-zirga tsakanin cibiyoyin noma da kasuwanni.

Ya bayyana cewa ingantattun hanyoyin sufuri za su sauƙaƙa jigilar amfanin gona, rage matsalolin kai da kawo kaya, da ƙarfafa sarƙoƙin darajar noma, wanda hakan zai ƙara samuwar abinci da damarmakin tattalin arziki.

Ƙaddamarwar a hukumance ta kasance farkon ayyukan yaƙin neman zaɓe na haɗin gwiwa na Majalisar Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa da na Gwamna ta APC a Jihar Neja. Ana sa ran ƙarfafa shirya jama’a a matakin tushe a ƙananan hukumomin jihar gabanin babban zaɓen 2027.

Tags: APCGwamna Mohammed Umar BagoMinnaMohammed IdrisNejaShugaba Bola Ahmed Tinubuyaƙin neman zaɓezaben2027
Previous Post

Nijeriya ta shirya karɓar baƙuncin Taron Hulɗar Jama’a na Duniya – Minista

Next Post

Cewar Tinubu: Bambancin ra’ayin siyasa ko neman mulki ba hujja ce ta dalilin zubar da jini ko tayar da rikici ba

Related Posts

Al’ummar Shinkafi sun yi alƙawarin goyon bayan Tinubu, Dauda Lawal da sauran ’yan takarar APC a 2027
Siyasa

Al’ummar Shinkafi sun yi alƙawarin goyon bayan Tinubu, Dauda Lawal da sauran ’yan takarar APC a 2027

November 28, 2026
Tinubu ya umurci sojoji su ƙara ƙaimi kan ’yan ta’adda a Arewa-Maso-Gabas domin ɗorewar zaman lafiya
Siyasa

Tinubu ya umurci sojoji su ƙara ƙaimi kan ’yan ta’adda a Arewa-Maso-Gabas domin ɗorewar zaman lafiya

November 25, 2026
Tinubu ya taya Atiku murnar cika shekaru 80
Siyasa

Tinubu ya taya Atiku murnar cika shekaru 80

November 25, 2026
Sanata Barau ya haɗa malamai sama da 2,000 domin tallata Tinubu, Gwamna Abba da ’yan takarar APC
Siyasa

Sanata Barau ya haɗa malamai sama da 2,000 domin tallata Tinubu, Gwamna Abba da ’yan takarar APC

November 24, 2026
Kwankwaso ya tura ni wajen Tinubu bayan mun yi alƙawarin komawa APC, inji Abba Yusuf
Siyasa

Kwankwaso ya tura ni wajen Tinubu bayan mun yi alƙawarin komawa APC, inji Abba Yusuf

November 23, 2026
Rikicin ADC: INEC ta bayyana dalilin da ya sa Mark da Aregbesola ke ci gaba da kasancewa a cikin bayanan ta, yayin da ɓangaren Nafiu Gombe ke nuna rashin amincewa
Siyasa

Rikicin ADC: INEC ta bayyana dalilin da ya sa Mark da Aregbesola ke ci gaba da kasancewa a cikin bayanan ta, yayin da ɓangaren Nafiu Gombe ke nuna rashin amincewa

November 20, 2026
Next Post
Cewar Tinubu: Bambancin ra’ayin siyasa ko neman mulki ba hujja ce ta dalilin zubar da jini ko tayar da rikici ba

Cewar Tinubu: Bambancin ra'ayin siyasa ko neman mulki ba hujja ce ta dalilin zubar da jini ko tayar da rikici ba

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • November 2026
  • October 2026
  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!