Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ce Jam’iyyar APC za ta yi kamfen gabanin babban zaɓen 2027 bisa nasarorin gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a fannin sauye-sauyen tattalin arziki, samar da ababen more rayuwa da sauya fasalin ƙasa.
Idris ya bayyana hakan ne a jiya Litinin a Minna, babban birnin Jihar Neja, yayin bikin ƙaddamar da kwamitocin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa da na gwamnan jihar na APC, wanda Gwamna Mohammed Umaru Bago ya jagoranta.
Ya ce manufofin gwamnatin Tinubu a cikin shekaru uku da rabi da suka gabata sun fara magance matsalolin tattalin arziki da suka daɗe suna addabar ƙasar, ƙarfafa ginshiƙan tattalin arziƙi da kuma samar da damarmakin ci gaba mai ɗorewa.
Ya ce: “Gaskiyar magana ita ce, gwamnatin APC ƙarƙashin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ta sauya tattalin arzikin Nijeriya da rayuwar ’yan ƙasar. Za mu yi kamfen ne bisa nasarorin da Shugaban Ƙasa ya samu a cikin shekaru uku da rabi da suka gabata.”
Ministan ya bayyana APC a matsayin jam’iyyar da za ta iya yin gogayya sosai a zaɓen da ke tafe, yana mai cewa ayyukan Tinubu da gwamnonin APC a faɗin ƙasar sun ƙarfafa matsayin jam’iyyar.
Ya ce Ajandar Sabunta Fata ta gwamnatin Tinubu ta kawo sauye-sauye domin gyara matsalolin da suka gurɓata tsarin tattalin arziki, inganta harkokin kuɗaɗen gwamnati, jawo hankalin masu zuba jari da kuma faɗaɗa muhimman ababen more rayuwa.
Idris, wanda aka naɗa a kwamitocin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa da na gwamnan Jihar Neja, ya yaba wa Bago bisa jagorancin sa da ƙoƙarin ƙarfafa tsarin jam’iyyar da tattara masu ruwa da tsaki a faɗin jihar.
Yayin ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓen mai mambobi 525, Bago ya ce APC a Jihar Neja na da burin samo wa Tinubu ƙuri’u sama da miliyan biyu a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
“Idan kowa ya kawo ƙuri’un sa, za mu samu sama da ƙuri’a miliyan ɗaya. Amma burin mu ya wuce haka. A wannan karon, burin mu shi ne mu fito da ƙuri’u sama da miliyan biyu, kuma da yardar Allah za mu cimma hakan,” inji Bago.
Ya ƙara da cewa za a ƙaddamar da ofishin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na APC na yankin Arewa ta Tsakiya da ke Minna a mako mai zuwa.
Ana sa ran Shugaban Ƙasa Tinubu, Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima, Shugaban Majalisar Dattawa, Kakakin Majalisar Wakilai ko Shugaban APC na ƙasa za su halarta.
Bikin ƙaddamar da kwamitin ya samu halartar shugabannin jam’iyya, masu riƙe da muƙaman siyasa da sauran masu ruwa da tsaki daga sassa daban-daban na Jihar Neja, yayin da APC ta fara shirye-shiryen babban zaɓen 2027.







