• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Saturday, November 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

Yabon gwani ya zama dole: Abdul Samad ya jinjina yadda tsare-tsaren CBN suka samar da hanyoyin canjin dala a sauƙaƙe

Ashafa Murnai Barkiya by Ashafa Murnai Barkiya
October 27, 2026
in Kuɗi Da Tattalin Arziki
A A
0
Yabon gwani ya zama dole: Abdul Samad ya jinjina yadda tsare-tsaren CBN suka samar da hanyoyin canjin dala a sauƙaƙe
Abdul Samad Rabiu, Shugaban BUA Group

Abdul Samad Rabiu, Shugaban BUA Group

Shugaban rukunin kamfanonin BUA Group, Abdul Samad Rabiu, ya bayyana cewa sauye-sauyen da aka yi a kasuwar canjin kuɗaɗen waje a Nijeriya sun sauƙaƙa wa ‘yan kasuwa samun dalar Amurka da sauran kuɗaɗen waje, tare da rage dogaro da rabon kuɗaɗen waje kai tsaye daga Babban Bankin Nijeriya (CBN).

Da yake jawabi a Taron Ƙolin Tattalin Arzikin Nijeriya karo na 32 (Nigerian Economic Summit) a ranar Litinin, Rabiu ya bayyana cewa a baya kamfanoni kan je CBN duk bayan mako biyu domin neman kuɗaɗen waje da za su sayi injuna da kayayyakin sarrafa masana’antu, lamarin da ke haifar da cikas ga hadahadar manyan jarin kasuwanci.

“A baya, duk bayan mako biyu sai mun yi tattaki zuwa CBN da ke nan Abuja,” inji shi.

Rabiu ya ce amma yanzu wannan yanayi ya sauya, sakamakon gyare-gyaren da CBN ya yi, waɗanda suka ba wa ‘yan kasuwa damar samun kuɗaɗen waje ta kasuwa bisa farashin da ake amfani da shi a lokacin, maimakon dogaro da rabon daloli kai tsaye daga CBN.

“Yanzu dai ba na buƙatar zuwa CBN domin neman canjin dala. A gaskiya, tun bayan da Yemi Cardoso ya zama Gwamnan CBN, ina ganin na haɗu da shi sau uku ko huɗu ne kawai, domin ba na buƙatar sa wajen samun musayar kuɗaɗen waje. Wannan shi ne gaskiya,” inji Rabi’u.

Ya bayyana cewa ya fi son kasuwar canjin kuɗaɗen waje mai gaskiya da bayyana farashi, wadda kamfanoni za su iya tsara harkokin su bisa farashin da ake samu a kasuwa, maimakon tsarin da farashin hukuma yake da kyau a zahiri amma babu dalar da za a iya samu.

“Tabbacin samun kuɗaɗen waje yana bai wa ‘yan kasuwa kwarin gwiwar zuba jari,” inji shugaban kamfanin BUA.

Rabi’u ya ce sassaucin da aka samu a kasuwar canjin kuɗaɗen waje na daga cikin gyare-gyaren tattalin arziki da aka aiwatar cikin shekaru uku da suka gabata, tare da cire tallafin man fetur da sauye-sauyen harkokin kuɗaɗen gwamnati da haraji.

A Samar Da Ƙarin Manyan Masana’antu:

Rabi’u ya ce wajibi ne Nijeriya ta faɗaɗa masana’antun ta ta hanyar taimaka wa ƙananan ‘yan kasuwa su bunƙasa zuwa manyan kamfanoni masu ƙarfin zuba jari a masana’antu, noma, haƙar ma’adinai da sauran sassan tattalin arziki masu samar da kayayyaki.

“Tambayar da ya kamata mu yi wa kanmu ba wai kawai yadda BUA zai ci gaba da bunƙasa ba ce. Ya kamata mu tambayi kan mu yadda Nijeriya za ta samar da wasu masana’antu kamar 100 irin na BUA,” inji shi.

Ya bayyana samun jari mai sauƙin kuɗin ruwa da kuma na dogon lokaci a matsayin ɗaya daga cikin manyan ƙalubalen faɗaɗa masana’antu, yana mai cewa zuba jari a masana’antu na iya ɗaukar shekaru 10 zuwa 20 kafin a cimma cikakkiyar ribar sa.

Tags: Abdul Samad Rabi'uBabban Bankin Nijeriya (CBN)BUA Groupyabo
Previous Post

’Yan sanda a Katsina sun tabbatar da kashe Sheikh Yahaya Masussuka da abokin sa

Next Post

2027: APC za ta yi kamfen kan sauye-sauyen tattalin arzikin Tinubu, inji Idris

Related Posts

Ƙananan ’yan kasuwa 5,000 ‘sun amfana da shirye-shiryen tallafi daban-daban na Gwamnatin Tarayya a Borno’
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Ƙananan ’yan kasuwa 5,000 ‘sun amfana da shirye-shiryen tallafi daban-daban na Gwamnatin Tarayya a Borno’

November 25, 2026
Muna samun nasarori a tsaro, ilimi da ababen more rayuwa – Tinubu 
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Tinubu ya ware Naira biliyan 450 domin tallafa wa manoma 500,000

November 22, 2026
Tinubu ya bayyana shirin samar da motoci masu amfani da gas guda 300, tare da alƙawarin rage kuɗin sufuri da kashi 40
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Tinubu ya bayyana shirin samar da motoci masu amfani da gas guda 300, tare da alƙawarin rage kuɗin sufuri da kashi 40

November 19, 2026
CBN ya naɗa kamfanoni takwas domin kula da fitar da ɗanyen mai da iskar gas
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN da NNPCL sun ƙulla yarjejeniyar ƙarfafa tattalin arziki da samar da kuɗaɗen zuba jari a ɓangaren makamashi

November 18, 2026
CBN ya fitar da sabbin ƙa’idojin adana bayanan kwastomomi ga bankunan Access, Zenith, OPay, PalmPay da sauran su
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN ya fitar da sabbin ƙa’idojin adana bayanan kwastomomi ga bankunan Access, Zenith, OPay, PalmPay da sauran su

November 17, 2026
Hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ya ragu zuwa kashi 14.06 cikin 100 a watan Oktoba – NBS
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ya ragu zuwa kashi 14.06 cikin 100 a watan Oktoba – NBS

November 16, 2026
Next Post
2027: APC za ta yi kamfen kan sauye-sauyen tattalin arzikin Tinubu, inji Idris

2027: APC za ta yi kamfen kan sauye-sauyen tattalin arzikin Tinubu, inji Idris

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • November 2026
  • October 2026
  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!