Rundunar ’Yan Sandan Jihar Katsina ta tabbatar da kashe fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Yahaya Ibrahim Masussuka, tare da abokin sa, Adamu Abubakar, da wasu da ake zargin ’yan bindiga ne a garin Dutsin-Ma da ke jihar.
Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 7:30 na daren yau Litinin, 26 ga Oktoba, 2026, a gaban gidan malamin, lokacin da wasu mutane biyu ɗauke da makamai, waɗanda suke kan babur, suka buɗe wa waɗanda abin ya shafa wuta.
’Yan sandan sun ce duka mutanen biyu sun samu raunukan harbin bindiga da suka yi sanadin mutuwar su. An garzaya da su asibiti mafi kusa domin ba su agajin gaggawa, amma likitan da ya duba su ya tabbatar da cewa sun mutu.
A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Litinin, Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar ’Yan Sandan Jihar Katsina, DSP Abubakar Sadiq Aliyu, ya ce da samun rahoton harin, jami’in ’yan sanda mai kula da sashen Dutsin-Ma (DPO) ya jagoranci tawagar jami’an rundunar zuwa wurin da lamarin ya faru.
Sanarwar ta ƙara da cewa Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Katsina, CP Ali Umar Fage, ya bayar da umarnin tura jami’an rundunonin yaƙi da laifuffuka da sauran jami’an tsaro zuwa yankin domin bin sawun waɗanda ake zargin tare da kama su.
A cewar ’yan sandan, an fara gudanar da bincike kan lamarin, yayin da ake ƙara ƙaimi wajen gano waɗanda suka aikata laifin da kuma gurfanar da su a gaban kotu.
Kwamishinan ’yan sandan ya miƙa saƙon ta’aziyyarsa ga iyalan mamatan, abokan su, da mabiyan su, da kuma al’ummar ƙaramar hukumar Dutsin-Ma bisa wannan babban rashi.
Ya kuma tabbatar wa al’umma cewa rundunar ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba har sai ta kama waɗanda suka aikata wannan aika-aika tare da tabbatar da an gurfanar da su domin fuskantar hukunci.
Rundunar ’yan sandan ta ce za ta ci gaba da sanar da al’umma duk wani sabon bayani da ya samu dangane da lamarin.






