• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Saturday, November 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai Siyasa

Tinubu ya ƙaddamar da kilomita 81 na Babbar hanyar Abuja-Kaduna

* Ya zargi 'yan adawa da cewa sune tushen matsalolin Nijeriya

WAKILIN MU by WAKILIN MU
October 24, 2026
in Siyasa
A A
0
Tinubu ya ƙaddamar da kilomita 81 na Babbar hanyar Abuja-Kaduna
Shugaba Tinubu yana jawabi a wurin taron ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar APC a filin wasa na Ranchers Bees da ke Kaduna, ranar Asabar

Shugaba Tinubu yana jawabi a wurin taron ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar APC a filin wasa na Ranchers Bees da ke Kaduna, ranar Asabar

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya zargi ’yan adawa da haddasa yunwa da talaucin da suke amfani da su wajen sukar gwamnatin sa, yana mai cewa gwamnatin sa na ƙoƙarin kawar da matsalolin.

Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Asabar, yayin ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar APC a filin wasa na Ranchers Bees da ke Kaduna, gabanin zaɓen shekarar 2027.

“Ina jin ’yan adawa suna magana kan yunwa da talauci. Wa ya haddasa su? Su ne. Su suka haddasa yunwar da talaucin. Mu kuma muna ƙoƙarin kawar da su,” in ji shugaban.

A cikin wata sanarwa da mai ba shugaban ƙasa shawara kan yaɗa labarai da dabarun sadarwa, Bayo Onanuga, ya fitar ranar 24 ga Oktoba, 2026, an bayyana cewa Tinubu ya yi wannan furuci ne yayin da yake jawabi ga ɗimbin magoya bayan APC da suka halarci taron.

Sanarwar ta danganta kalaman shugaban da sukar da ’yan adawa ke yi wa gwamnatin sa kan matsalolin tattalin arziki, inda ta yi nuni da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, wanda ya riƙe muƙamin tsakanin shekarun 1999 zuwa 2007.

Sanarwar ta yi zargin cewa a lokacin mulkin wancan gwamnati, an mayar da wasu kamfanonin gwamnati hannun masu zaman kan su ba tare da biyan dubban ma’aikatan da aka sallama hakkokin su na fansho da alawus ba, tana mai cewa gwamnatin Tinubu na biyan wasu daga cikin waɗannan haƙƙoƙi.

A yayin taron, Tinubu ya kuma ƙaddamar da aikin wani sashe mai tsawon kilomita 81 na babbar hanyar Abuja-Kaduna, ta hanyar.

Shugaban ya tuna da muhimmancin Kaduna a tarihin siyasar Nijeriya, yana mai bayyana birnin a matsayin cibiyar shugabanni da kuma hedikwatar siyasar Arewacin Nijeriya a baya.

Ya gode wa al’ummar Jihar Kaduna bisa goyon bayan da suka ba shi a zaɓen 2023, tare da kira gare su da su sake zaɓen sa a karo na biyu.

Tinubu ya ce ya kamata masu zaɓe su yi la’akari da ayyukan da gwamnatin sa ta aiwatar, musamman zuba jari a muhimman ayyukan more rayuwa a Kaduna da sauran jihohin Arewa.

Taron ya samu halartar shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda; Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima; uwargidan shugaban ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu; da uwargidan mataimakin shugaban ƙasa.

Haka kuma, gwamnonin APC 32 da tsohon shugaban jam’iyyar na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, da tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje, na cikin manyan waɗanda suka halarci taron.

A nasa jawabin, Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya sake jaddada ƙudirin gwamnatin Tinubu na ƙarfafa haɗin kan ƙasa, tabbatar da zaman lafiyar dimokiradiyya da bunƙasa tattalin arziki.

Shettima ya buƙaci ’yan Nijeriya da su mara wa shugaban baya domin ba shi damar ci gaba da shirye-shiryen gwamnatin sa.

Ya tuna da yadda Tinubu ya goyi bayan ’yan takarar shugaban ƙasa daga Arewa a zaɓukan baya, ciki har da tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, wanda ya lashe zaɓukan 2015 da 2019.

Ya kuma ambaci goyon bayan da Tinubu ya bayar ga wasu ’yan siyasar Arewa, ciki har da Atiku Abubakar da Malam Nuhu Ribadu, a fafatawar siyasa ta baya.

A cewar sa, waɗannan matakai sun nuna aminci, mutunta juna da ƙudirin haɗa kan ’yan Najeriya, duk da bambancin yankuna da ra’ayoyin siyasa.

Shettima ya ce irin wannan dangantaka ta taimaka wajen ƙarfafa APC da kuma nuna muhimmancin haɗin kai wajen gina ƙasa mai wadata.

“Mun lashe zaɓen da ya gabata ne saboda kun ga mafi dacewa a gaban ku. Ga al’ummar kirki ta jihar Kaduna, mun fahimci dalilin da ya sa kuka tsaya tare da mu a ƙarƙashin APC, domin dawo da martabar wannan babbar jiha,” inji Shettima.

A jawabin sa na maraba, Gwamnan Kaduna, Sanata Uba Sani, ya yaba wa Tinubu bisa goyon bayan da yake bai wa gwamnatocin jihohi wajen aiwatar da shirye-shiryen ci gaba.

Gwamnan ya ce haɗin gwiwa tsakanin gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi na da muhimmanci wajen samar da cigaba mai ɗorewa, musamman a fannonin gine-gine, noma da shirye-shiryen inganta rayuwar jama’a.

Ya kuma yaba wa uwargidan shugaban ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, bisa ayyukan da take yi na tallafa wa mata, yara da iyalai.

Uba Sani ya buƙaci magoya bayan APC da su kasance masu taka-tsantsan da yaɗa bayanan ƙarya a lokacin yaƙin neman zaɓe, musamman saƙonnin yaudara da ake yaɗawa a kafafen sada zumunta da wasu hotuna ko bidiyoyi da aka ƙirƙira ta amfani da fasahar basirar ɗan Adam (AI).

Shi ma Darakta-Janar na kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na APC, Abdulaziz Yari, ya bayyana tabbacin cewa jam’iyyar za ta iya tattara goyon bayan jama’a domin sake zaɓen Tinubu a 2027.

Yari ya yaba wa Gwamna Uba Sani, shugabannin jam’iyyar da sauran masu ruwa da tsaki bisa haɗin gwiwar da suka yi wajen shirya taron.

Ya kuma kare sauye-sauyen tattalin arziki da gwamnatin Tinubu ke aiwatarwa, inda ya yi nuni da sauye-sauyen da ake samu a kasuwar canjin kuɗaɗen ƙasashen waje.

Tsohon gwamnan Zamfara ya buƙaci ’yan Najeriya da su auna gwamnati bisa manufofin ta da ayyukan da ta aiwatar, tare da kira ga magoya bayan APC da su guji yaɗa bayanan da ba su da tushe.

A yayin bikin ƙaddamar da aikin ta hanyar sadarwa daga nesa, Ministan Ayyuka, Injiniya Dave Umahi, ya yi bayani kan ayyukan tituna da gwamnatin Tinubu ke gudanarwa a yankin Arewa maso Yamma da sauran sassan ƙasar.

Aikin da aka ƙaddamar ya shafi sashe na farko mai tsawon kilomita 81 na babbar hanyar Abuja-Kaduna-Zariya-Kano mai hanyoyi biyu na zirga-zirga.

Tags: KadunaShugaba Bola Ahmed Tinubuyaƙin neman zaɓezaben2027
Previous Post

Arewa-Maso-Yamma na tare da Tinubu don wa’adi na biyu, cewar Uba Sani

Next Post

Taron Kaduna: Arewa ta Bayyana Matsayar Ta Kan Tinubu

Related Posts

Al’ummar Shinkafi sun yi alƙawarin goyon bayan Tinubu, Dauda Lawal da sauran ’yan takarar APC a 2027
Siyasa

Al’ummar Shinkafi sun yi alƙawarin goyon bayan Tinubu, Dauda Lawal da sauran ’yan takarar APC a 2027

November 28, 2026
Tinubu ya umurci sojoji su ƙara ƙaimi kan ’yan ta’adda a Arewa-Maso-Gabas domin ɗorewar zaman lafiya
Siyasa

Tinubu ya umurci sojoji su ƙara ƙaimi kan ’yan ta’adda a Arewa-Maso-Gabas domin ɗorewar zaman lafiya

November 25, 2026
Tinubu ya taya Atiku murnar cika shekaru 80
Siyasa

Tinubu ya taya Atiku murnar cika shekaru 80

November 25, 2026
Sanata Barau ya haɗa malamai sama da 2,000 domin tallata Tinubu, Gwamna Abba da ’yan takarar APC
Siyasa

Sanata Barau ya haɗa malamai sama da 2,000 domin tallata Tinubu, Gwamna Abba da ’yan takarar APC

November 24, 2026
Kwankwaso ya tura ni wajen Tinubu bayan mun yi alƙawarin komawa APC, inji Abba Yusuf
Siyasa

Kwankwaso ya tura ni wajen Tinubu bayan mun yi alƙawarin komawa APC, inji Abba Yusuf

November 23, 2026
Rikicin ADC: INEC ta bayyana dalilin da ya sa Mark da Aregbesola ke ci gaba da kasancewa a cikin bayanan ta, yayin da ɓangaren Nafiu Gombe ke nuna rashin amincewa
Siyasa

Rikicin ADC: INEC ta bayyana dalilin da ya sa Mark da Aregbesola ke ci gaba da kasancewa a cikin bayanan ta, yayin da ɓangaren Nafiu Gombe ke nuna rashin amincewa

November 20, 2026
Next Post
Taron Kaduna: Arewa ta Bayyana Matsayar Ta Kan Tinubu

Taron Kaduna: Arewa ta Bayyana Matsayar Ta Kan Tinubu

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • November 2026
  • October 2026
  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!