Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya yi watsi da yiwuwar jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC) ta janye takarar ta shugaban ƙasa domin mara wa Atiku Abubakar na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) baya a zaɓen shekarar 2027.
Kwankwaso, wanda shi ne ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na NDC tare da ɗan takarar shugaban ƙasa, Peter Obi, ya kuma zargi kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na ADC (ADC-PCC) da kai hare-hare marasa amfani a kan sa, Obi da kuma jam’iyyar su.
A cikin wata sanarwa, Kwankwaso ya yi watsi da zarge-zargen da ke nuna cewa NDC tana yi wa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki aiki ko kuma tana shirin janye takarar ta domin mara wa ɗan takarar ADC baya.
Ya ce waɗannan zarge-zarge ba su da tushe, yana mai jaddada cewa NDC tana nan daram kan matsayin ta na neman shugabancin ƙasa, kuma tana da ƙwarin gwiwar lashe zaɓen.
Kwankwaso ya ce, “Bari in bayyana ƙarara kuma ba tare da wata shakka ba cewa ba za mu janye takarar mu domin ADC ko wata jam’iyya ba.”
Ya zargi tawagar yaƙin neman zaɓen ADC da mayar da hankali kan kai wa NDC hari maimakon gabatar da cancanta, sahihanci da nasarorin ɗan takarar ta ga ’yan Nijeriya.
Ya shawarci kwamitin yaƙin neman zaɓen ADC da ya mayar da hankalin sa wajen ba da amsa ga zarge-zargen da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya yi wa ɗan takarar ta, maimakon kai hari ga shugabannin NDC.
Tsohon gwamnan na Jihar Kano ya kuma yi gargaɗin cewa tawagar ADC na iya ƙoƙarin yaudarar magoya bayan NDC a jajibirin zaɓe, ta hanyar yaɗa labarin ƙarya cewa jam’iyyar za ta janye takarar ta domin mara wa ADC baya.
Ya jaddada cewa shi da Peter Obi ba sa yi wa APC ko wani ɗan takarar ta aiki, yana mai cewa babu wani dalili da zai sa NDC ta janye daga takarar shugaban ƙasa domin goyon bayan ADC ko wata jam’iyya.
Da yake tsokaci kan yanayin siyasar ƙasar, Kwankwaso ya ce gwamnatin APC ta gaza wajen sauke nauyin da ke kan ta ga ’yan Nijeriya, yayin da ADC ba ta da wani zaɓi mafi kyau da za ta gabatar wa al’umma.
Ya bayyana tikitin takarar shugaban ƙasa na NDC, wanda aka fi sani da tikitin OK, a matsayin sahihin zaɓin da ’yan Nijeriya za su iya dogaro da shi, bisa la’akari da ƙwarewa, tarihin nasarori, sahihanci da kuma goyon bayan da yake samu a Arewa da Kudancin Nijeriya.
A cewar sa, tikitin na da manufar haɗa kan ƙasa da magance manyan matsalolin da ke addabar Nijeriya, ciki har da rashin tsaro, ilimi, noma, ababen more rayuwa, kiwon lafiya da bunƙasa tattalin arziki.
Kwankwaso ya kuma bayyana NDC a matsayin jam’iyyar adawa mafi ƙarfi kuma mafi cancanta a ƙasar, inda ya buƙaci magoya bayan jam’iyyar da sauran ’yan Nijeriya masu kishin ƙasa da su ci gaba da ƙoƙarin ganin ta samu nasara a zaɓe.
A ƙarshe, ya bayyana kyakkyawan fata game da makomar ƙasar, inda ya ce: “Nijeriya za ta zama OK.”







