• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Saturday, November 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

Ziyara Ta Musamman: Cardoso zai ziyarci China don ƙarfafa biyan kuɗi da daidaita cinikayya tsakanin Naira da Yuan

Ashafa Murnai Barkiya by Ashafa Murnai Barkiya
October 18, 2026
in Kuɗi Da Tattalin Arziki
A A
0
Ziyara Ta Musamman: Cardoso zai ziyarci China don ƙarfafa biyan kuɗi da daidaita cinikayya tsakanin Naira da Yuan
Olayemi Cardoso

Olayemi Cardoso

Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN) Olayemi Cardoso, ya bayyana cewa Nijeriya za ta nemi ƙarfafa tsarin biyan kuɗi da daidaita hada-hadar kuɗaɗen cinikayya tsakanin ta da Sin.

Cardoso ya ce zai tabbatar da wanzuwar hakan yayin wata ziyara da zai kai birnin Beijing nan ba da jimawa ba.

Ya ce ƙasashen biyu na ƙoƙarin zurfafa haɗin gwiwar kuɗi domin sauƙaƙa harkokin cinikayya da zuba jari a tsakanin su.

Cardoso ya bayyana hakan ne bayan halartar taron shekara-shekara na 2026 na Asusun Bayar da Lamuni na Duniya (IMF) da Bankin Duniya, wanda aka gudanar a Bangkok, babban birnin Thailand.

Ya ce ya gana da gwamnan Babban Bankin China, Pan Gongsheng, inda suka tattauna hanyoyin ƙarfafa dangantakar kuɗi tsakanin tattalin arzikin ƙasashen biyu.

Tattaunawar ta mayar da hankali kan biyan kuɗaɗen cinikayya tsakanin ƙasashe, tsarin daidaita hada-hadar kuɗi, fasahar kuɗi da kuma samar da kuɗaɗen gudanar da cinikayya.

Waɗannan fannoni na iya taimakawa wajen rage matsalolin da ‘yan kasuwa daga Nijeriya da China ke fuskanta yayin gudanar da hadahadar kasuwanci.

Cardoso ya ce za a ci gaba da tattaunawar a yayin ziyarar da zai kai Beijing, tare da maida hankali kan sauƙaƙa biyan kuɗi tsakanin ƙasashen biyu, tallafa wa cinikayya da zuba jari, da kuma ƙarfafa ayyukan cibiyoyin hada-hadar kuɗi.

Ana sa ran ziyarar za ta samar da damar zurfafa waɗannan tattaunawa, duk da cewa CBN bai bayyana takamaiman matakan aiwatarwa, adadin hada-hadar kuɗin da ake sa ran gudanarwa, ko lokacin fara sabon tsarin ba.

Ana Sa Ran Rage Tsadar Hada-hadar Kuɗi:

Ƙarfafa alaƙar tsarin biyan kuɗi tsakanin Nijeriya da China na iya taimaka wa ‘yan kasuwa wajen biyan kuɗin kayayyakin da suke shigowa da su, daidaita basussukan kasuwanci da kuma sauƙaƙa zuba jari.

Sai dai tasirin wannan mataki zai dogara ne da tsarin da ƙasashen biyu za su amince da shi, ciki har da kuɗin gudanar da hada-hadar, saurin kammala biyan kuɗi, buƙatar musayar kuɗaɗe da kuma damar da bankuna da ‘yan kasuwa za su samu na amfani da tsarin.

China na daga cikin manyan ƙasashen da Nijeriya ke hulɗar cinikayya da su. Saboda haka, samar da ingantaccen tsarin biyan kuɗi na daga cikin muhimman abubuwan da za su iya inganta dangantakar tattalin arzikin ƙasashen biyu.

A wasu lokuta, biyan kuɗaɗen cinikayya tsakanin ƙasashe na buƙatar shiga tsakanin bankuna da dama, musayar kuɗaɗe da kuma bin ƙa’idojin gudanar da hadahadar kuɗi

Previous Post

NDC ba za ta janye wa Atiku a zaɓen 2027 ba – Kwankwaso

Next Post

Gwamnan Kaduna zai samar wa iyalan Abubakar Zakka gida, ya ɗauki nauyin jinyar su

Related Posts

Ƙananan ’yan kasuwa 5,000 ‘sun amfana da shirye-shiryen tallafi daban-daban na Gwamnatin Tarayya a Borno’
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Ƙananan ’yan kasuwa 5,000 ‘sun amfana da shirye-shiryen tallafi daban-daban na Gwamnatin Tarayya a Borno’

November 25, 2026
Muna samun nasarori a tsaro, ilimi da ababen more rayuwa – Tinubu 
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Tinubu ya ware Naira biliyan 450 domin tallafa wa manoma 500,000

November 22, 2026
Tinubu ya bayyana shirin samar da motoci masu amfani da gas guda 300, tare da alƙawarin rage kuɗin sufuri da kashi 40
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Tinubu ya bayyana shirin samar da motoci masu amfani da gas guda 300, tare da alƙawarin rage kuɗin sufuri da kashi 40

November 19, 2026
CBN ya naɗa kamfanoni takwas domin kula da fitar da ɗanyen mai da iskar gas
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN da NNPCL sun ƙulla yarjejeniyar ƙarfafa tattalin arziki da samar da kuɗaɗen zuba jari a ɓangaren makamashi

November 18, 2026
CBN ya fitar da sabbin ƙa’idojin adana bayanan kwastomomi ga bankunan Access, Zenith, OPay, PalmPay da sauran su
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN ya fitar da sabbin ƙa’idojin adana bayanan kwastomomi ga bankunan Access, Zenith, OPay, PalmPay da sauran su

November 17, 2026
Hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ya ragu zuwa kashi 14.06 cikin 100 a watan Oktoba – NBS
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ya ragu zuwa kashi 14.06 cikin 100 a watan Oktoba – NBS

November 16, 2026
Next Post
Gwamnan Kaduna zai samar wa iyalan Abubakar Zakka gida, ya ɗauki nauyin jinyar su

Gwamnan Kaduna zai samar wa iyalan Abubakar Zakka gida, ya ɗauki nauyin jinyar su

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • November 2026
  • October 2026
  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!