• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Sunday, November 29, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN ya ƙarfafa dangantakar kuɗi da nahiyar Asiya, ya sa hannu kan yarjejeniyar haɗin gwiwa a fannin ƙirƙire-ƙirƙire a Singapore

Ashafa Murnai Barkiya by Ashafa Murnai Barkiya
October 9, 2026
in Kuɗi Da Tattalin Arziki
A A
0
CBN ya ƙarfafa dangantakar kuɗi da nahiyar Asiya, ya sa hannu kan yarjejeniyar haɗin gwiwa a fannin ƙirƙire-ƙirƙire a Singapore
Gwamnan CBN, Olayemi Cardoso, lokacin haɗuwar sa da jami'an Hukumar Kuɗi ta Singapore (MAS) a birnin Singapore

Gwamnan CBN, Olayemi Cardoso, lokacin haɗuwar sa da jami'an Hukumar Kuɗi ta Singapore (MAS) a birnin Singapore

Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya ƙara zurfafa hulɗar sa ta fannin kuɗi da hukumomi da ƙasashen Nahiyar Asiya, bayan gudanar da jerin manyan tarurruka a Singapore.

Tarurrukan dai sun haɗa da tattaunawa da Hukumar Kuɗi ta Singapore (MAS), tare da sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna, wato MoU, kan ƙirƙire-ƙirƙire a fannin kuɗi.

Gwamnan CBN, Olayemi Cardoso, ne ya jagoranci waɗannan tattaunawa a kan hanyar sa ta zuwa Bangkok domin halartar Taron Shekara-shekara na Asusun Bayar da Lamuni na Duniya (IMF) da Bankin Duniya.

CBN dai na ƙoƙarin ƙarfafa alaƙar Nijeriya da kasuwannin kuɗi na nahiyar Asiya da kuma jawo ƙarin jarin da zai daɗe yana tasiri a ƙasar nan.

CBN ya kuma sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna da Global Finance & Technology Network (GFTN), wadda ta samar da tsarin haɗin gwiwa kan ƙirƙire-ƙirƙire a fannin kuɗi, tare da haɗa cibiyoyi da tsarin bunƙasa sabbin dabaru da fasahohi a Nijeriya da Singapore.

A cewar CBN, waɗannan hulɗoɗi na daga cikin ƙoƙarin mayar da sauye-sauyen da ake yi a ɓangaren kuɗi na Nijeriya zuwa ingantattun haɗin gwiwa da ƙasashen duniya, faɗaɗa kasuwannin kuɗi da samar da hanyoyi masu amfani don zuba jari, kasuwanci da ƙirƙire-ƙirƙire a fannin kuɗi.

A yayin tattaunawar sa da MAS, tawagar CBN ta yi musayar ra’ayoyi kan bunƙasa ɓangaren kuɗi, dokoki da ƙa’idojin gudanar da harkokin kuɗi, haɗin kan kasuwanni da sabbin fasahohi.

Haka kuma, sun gano wasu fannoni da za su ci gaba da haɗin gwiwa a kai tsakanin hukumomin biyu.

A wani taron tattaunawa mai taken Haɗa Kasuwannin Kuɗi Tsakanin Nijeriya da Asiya, wanda CBN ya shirya tare da haɗin gwiwar J.P. Morgan, Nigerian Exchange Group (NGX) da FMDQ Group, Cardoso ya bayyana burin Nijeriya na gina kasuwannin kuɗi masu zurfi, masu yawan hada-hadar kuɗi, kuma masu kyakkyawar alaƙa da kasuwannin duniya.

An gudanar da taron ne a ofisoshin J.P. Morgan da ke Singapore, ƙarƙashin jagorancin Dapo Olagunji, Manajan Daraktan J.P. Morgan mai kula da Yammacin Afirka. Taron ya haɗa masu zuba jari, cibiyoyin kuɗi, ‘yan kasuwa da kuma ‘yan Nijeriya da ke zaune da aiki a sassa daban-daban na nahiyar Asiya.

Cardoso ya ce an tsara sauye-sauyen da Nijeriya ta aiwatar a kasuwar canjin kuɗaɗen ƙasashen waje ne domin kawar da gurɓatattun hanyoyin gudanar da kasuwa, inganta gaskiya da bayyana bayanai, da kuma dawo da amincewa da ƙa’idojin da ke jagorantar masu shiga harkokin kuɗaɗe.

Ya ce: “Babban abin da zai nuna nasarar gyare-gyare ba wai ko za ka iya jawo jari sau ɗaya ba ne; a’a, shi ne ko za ka samar da amincewar da za ta sa jarin ya zauna, ya dawo, kuma ya ci gaba da bunƙasa.”

Gwamnan ya bayyana cewa ingantacciyar manufar kuɗi, ƙarfafa tsarin shugabanci da gudanarwa, inganta yadda kasuwanni ke aiki, da samar da ƙa’idoji masu tabbas, duk suna da muhimmanci wajen jawo jarin cikin gida da na ƙasashen waje wanda zai daɗe yana aiki.

Ya ƙara da cewa daidaituwar kasuwannin kuɗi ya kamata ta zama tubalin ƙara shigar masu zuba jari na dogon lokaci, ƙarfafa kayayyakin more rayuwa da tsarin gudanar da kasuwannin kuɗi, da kuma zurfafa alaƙa da kasuwannin kuɗi na duniya.

Taron ya kuma tattauna kan tafarkin gyare-gyaren da Nijeriya ke bi, samar da jari, dawo da amincewa da kasuwar canjin kuɗaɗen ƙasashen waje, da kuma kayayyakin more rayuwa da ake buƙata domin tabbatar da ci gaba da shigar masu zuba jari na ƙasashen duniya.

Wani zaman tattaunawa da Gbolahan Taiwo, Babban Masanin Tattalin Arziƙi na J.P. Morgan mai kula da Afirka, ya jagoranta, ya ƙunshi Temi Popoola, Babban Darakta kuma Babban Jami’in Gudanarwa na NGX Group; Zeal Akaraiwe, Babban Darakta kuma Babban Jami’in Gudanarwa na FMDQ Group; Aderinola Shonekan, Daraktan Ciniki da Canjin Kuɗi a CBN; da Olumayokun Ajibade, Mai Ba Gwamnan CBN Shawara na Musamman kan Kasuwannin Kuɗi da Manufofin Tattalin Arziƙi.

Cardoso ya ce hulɗar Nijeriya da Asiya ba ta taƙaita ga jawo kuɗaɗen zuba jari kawai ba. A maimakon haka, ana kuma son gina dangantaka mai ɗorewa tsakanin cibiyoyin kuɗi, kasuwanni, ‘yan kasuwa da kuma ‘yan Nijeriya da ke zaune a yankin.

Ya bayyana cewa akwai damar ƙarfafa alaƙa tsakanin bankunan Nijeriya da na Asiya, da kuma cibiyoyin kasuwannin kuɗi na ɓangarorin biyu. Haka kuma, akwai damar samar da hanyoyin biyan kuɗi da daidaita hada-hadar kuɗi cikin sauƙi da inganci, tare da ƙara shigar ‘yan Najeriya da ke zaune da aiki a Asiya cikin harkokin kasuwannin kuɗi.

Gwamnan ya kuma jaddada muhimmiyar rawar da fasahar kuɗi da basirar na’ura mai kwakwalwa (AI) ke takawa wajen inganta ayyukan kuɗi, ƙarfafa hanyoyin tantancewa da kula da haɗurra, bunƙasa shigar jama’a cikin harkokin kuɗi, da inganta ƙarfin hukumomin sa-ido da tsara dokoki.

Waɗannan tarurruka da aka gudanar a Singapore na daga cikin babban shirin CBN na gudanar da hulɗa da hukumomi da kasuwannin kuɗi a faɗin Asiya. Ana kuma sa ran gudanar da ƙarin tarurruka a birnin Beijing na ƙasar Sin.

Tags: haɗin gwiwaOlayemi CardosoSingapore
Previous Post

Shettima ya ce Nijeriya na shirin dasa bishiyoyi biliyan 20, za ta yi koyi da tsarin noma na Habasha

Next Post

2027: Tinubu zai ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen sa a Kaduna

Related Posts

Ƙananan ’yan kasuwa 5,000 ‘sun amfana da shirye-shiryen tallafi daban-daban na Gwamnatin Tarayya a Borno’
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Ƙananan ’yan kasuwa 5,000 ‘sun amfana da shirye-shiryen tallafi daban-daban na Gwamnatin Tarayya a Borno’

November 25, 2026
Muna samun nasarori a tsaro, ilimi da ababen more rayuwa – Tinubu 
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Tinubu ya ware Naira biliyan 450 domin tallafa wa manoma 500,000

November 22, 2026
Tinubu ya bayyana shirin samar da motoci masu amfani da gas guda 300, tare da alƙawarin rage kuɗin sufuri da kashi 40
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Tinubu ya bayyana shirin samar da motoci masu amfani da gas guda 300, tare da alƙawarin rage kuɗin sufuri da kashi 40

November 19, 2026
CBN ya naɗa kamfanoni takwas domin kula da fitar da ɗanyen mai da iskar gas
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN da NNPCL sun ƙulla yarjejeniyar ƙarfafa tattalin arziki da samar da kuɗaɗen zuba jari a ɓangaren makamashi

November 18, 2026
CBN ya fitar da sabbin ƙa’idojin adana bayanan kwastomomi ga bankunan Access, Zenith, OPay, PalmPay da sauran su
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN ya fitar da sabbin ƙa’idojin adana bayanan kwastomomi ga bankunan Access, Zenith, OPay, PalmPay da sauran su

November 17, 2026
Hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ya ragu zuwa kashi 14.06 cikin 100 a watan Oktoba – NBS
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ya ragu zuwa kashi 14.06 cikin 100 a watan Oktoba – NBS

November 16, 2026
Next Post
2027: Tinubu zai ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen sa a Kaduna

2027: Tinubu zai ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen sa a Kaduna

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • November 2026
  • October 2026
  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!