A ƙoƙarin sa na ci gaba da wayar da kan jama’a dangane da kare daraja da ingancin takardun naira, Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya yi kira ga ’yan Nijeriya, musamman ’yan kasuwa da su riƙa sarrafa takardun naira cikin kulawa, alfahari da mutunci, inganci da nagarta domin tsawaita dogon lokacin mu’amala da amfanin takardun kuɗi, tare da rage kuɗin da ake kashewa wajen sauya tsofaffi.
Haka kuma wannan kira da gargaɗi ya ƙunshi jawo hankulan jama’a su daina shafa wa takardun kuɗi datti, domin gwamnati na kashe maƙudan kuɗaɗe wajen sauya lalatattun takardun kuɗi.
Daraktan Ayyukan Kuɗaɗe da Gudanar da Rassa na CBN, Dakta Adedeji Adetona, ne ya yi wannan kira ranar Litinin a Kano, yayin wani gangamin wayar da kan jama’a kan yadda ya kamata a riƙa kula da Naira, wanda aka gudanar a Kasuwar Tirin Galadima, da ke Kano, jikin Kasuwar Sabon Gari.
Adetona, wanda Mataimakin Darakta a Sashen Ayyukan Kuɗaɗe, Ibrahim Yahya ya wakilta, ya ce an shirya gangamin ne domin isar da saƙon kula da naira kai tsaye ga jama’a, musamman waɗanda suka fi yawan mu’amala da kuɗin hannu.
Ya bayyana naira a matsayin alamar ’yancin kai da martabar Nijeriya, tare da jaddada buƙatar ’yan Nijeriya su riƙa sarrafa kuɗin cikin kulawa da nagarta.
“Babban saƙon shi ne yadda ya kamata a riƙa kula da Naira. Naira alama ce ta ’yancin kan mu. Ita ce martabar ƙasar mu, don haka ya kamata mu riƙa sarrafa Naira cikin matuƙar kulawa da nagarta,” inji shi.
Ya ci gaba da cewa CBN da kuma Gwamnatin Tarayya suna kashe ɗimbin kuɗaɗe wajen sauya takardun kuɗin da suka yi datti, waɗanda suka tsufa, lalatattu ko waɗanda suka yage.
Ya ce kula da kuɗin yadda ya kamata zai taimaka wajen tsawaita lokacin da takardun za su yi amfani, tare da rage kuɗaɗen da za a kashe wajen sauya waɗanda suka lalace.
“Mun yi imanin cewa idan muka riƙa kula da naira yadda ya kamata, za mu tsawaita tsawon lokacin amfanin ta, kuma hakan zai taimaka wajen rage yawan kuɗin da ake kashewa wajen sauya Naira,” cewar Adetona.
Ya ce CBN ya fara wannan gangamin wayar da kai ne a Kasuwar Galadima da ke Kano, kuma yana shirin kai saƙon zuwa sauran kasuwanni a faɗin jihar.
Adetona ya buƙaci jama’a da su riƙa riƙe naira cikin alfahari da mutunci, yana mai cewa manufar gangamin ita ce ƙarfafa ɗaukar matakin da ya dace wajen kula da kuɗin ƙasa.
Ya bayyana cewa an zaɓi kasuwanni ne a matsayin muhimman wuraren wayar da kai saboda muhimmiyar rawar da suke takawa wajen harkokin musayar kuɗi da mu’amalolin kuɗi hannu da hannu.
“Mun yi imanin cewa kasuwa ita ce babbar cibiyar mu’amalar musayar kuɗi. Mutane suna kawo kuɗaɗe, kuma mun fahimci muhimmiyar rawar da Kano ke takawa a harkokin kasuwanci.
“Kano cibiya ce ta kasuwanci da ake gudanar da mu’amalolin kuɗi hannu da hannu masu yawa, abin da ya sa ’yan kasuwa suke daga cikin muhimman masu ruwa da tsaki wajen inganta yadda ake kula da kuɗin ƙasa,” inji shi.
Adetona ya ce ’yan kasuwa suna karɓa da sarrafa kuɗaɗe akai-akai daga hannun abokan cinikin su, kuma a lokuta da dama suna tara kuɗin kafin su kai ribar ko kuɗaɗen da suka samu zuwa banki.
A cewar sa, tabbatar da cewa ’yan kasuwa suna kula da kuɗin da suke karɓa daga abokan ciniki yadda ya kamata, muhimmin mataki ne na farko wajen cimma manufar kare daraja da ingancin naira.
“Saboda haka, mun yi imanin cewa idan muka yi magana da ’yan kasuwa da kan su, wannan shi ne matakin farko.
“Suna tara kuɗaɗe, kuma wani ɓangare na kuɗin na iya kasancewa sun yi amfani da shi wajen gudanar da mu’amalolin su, yayin da sauran kuɗin kuma wataƙila za su kai banki.
“Saboda haka, mun yi imanin cewa kula da kuɗin da suka karɓa yadda ya kamata tun daga matakin farko zai taimaka matuƙa wajen cimma manufofin mu,” cewar daraktan.
Ya ce CBN zai ci gaba da tattaunawa da masu ruwa da tsaki da kuma jama’a domin ƙara wayar da kai kan muhimmancin kare da adana Naira.
Tun da farko, Shugaban Ƙungiyar ’Yan Kasuwar Galadima, Shu’aibu Suleiman, ya ce shugabancin kasuwar zai haɗa gwiwa da CBN wajen wayar da kan ’yan kasuwa, musamman ƙananan ’yan kasuwa, game da yadda ya kamata su riƙa kula da takardun Naira.
Ya yaba da matakin CBN na zaɓar kasuwar domin gudanar da gangamin wayar da kan jama’a, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen inganta yadda ake kula da kuɗin ƙasa.
Ya bayyana cewa kasuwar tana da ƙananan ’yan kasuwa da dama, ciki har da masu sayar da kifi, waɗanda za a kai wa saƙon wayar da kan jama’a ta wannan shiri.
Suleiman ya tabbatar wa tawagar CBN cewa shugabancin kasuwar zai ba da cikakken haɗin kai wajen isar da wannan saƙo ga ’yan kasuwa da abokan cinikin su.
Ya ce ci gaba da wayar da kan jama’a yana da muhimmanci wajen ƙarfafa ’yan Nijeriya su riƙa kula da naira yadda ya kamata tare da kiyaye ingancin ta.





