• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Monday, September 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Gwamnatin Kano ta hana hawan dawakai da hawan Durbar na sarakuna saboda dalilan tsaro

ALI KANO by ALI KANO
September 27, 2026
in Labarai
A A
0
Abin da ya sa na fice daga NNPP – Gwamnan Kano
Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano

Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano

Gwamnatin Jihar Kano ta dakatar da duk wani nau’in hawan Durbar da hawan dawakai a cikin birnin Kano har sai baba-ta-gani, saboda dalilan tsaro.

Wannan umarni ya biyo bayan wani taron gaggawa na Majalisar Tsaro ta Jihar Kano da aka gudanar a gidan gwamnatin jihar, inda aka yi nazari kan halin da ake ciki na tsaro dangane da shirye-shiryen gudanar da hawan Durbar da hawan dawakai da sarakuna suke shiryawa.

A wata sanarwa da ya fitar yau Lahadi, Darakta-Janar na Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na Gidan Gwamnatin Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya ce an ɗauki matakin ne domin kauce wa yiwuwar samun arangama, tabbatar da zaman lafiya da hana asarar rayuka ko dukiyoyi.

Sanarwar ta ce bayanan da hukumomin tsaro suka samu sun nuna cewa ana samun gagarumin gangamin magoya baya dangane da shirye-shiryen gudanar da waɗannan harkoki, lamarin da ya haifar da fargabar yiwuwar rikici da taɓarɓarewar doka da oda.

Saboda haka, Majalisar Tsaro ta Jihar ta bayar da umarnin dakatar da duk wani shirin hawan Durbar da hawan dawakai a cikin birnin Kano.

Gwamnatin ta ce ta ɗauki wannan mataki ne bisa nauyin da kundin tsarin mulki ya ɗora mata na kare rayuka da dukiyoyin al’umma tare da tabbatar da zaman lafiya da doka da oda a jihar.

Ta ƙara da cewa an umurci dukkan hukumomin tsaro da abin ya shafa da su tabbatar da aiwatar da wannan takunkumi tare da ɗaukar matakin da doka ta tanada kan duk wanda aka samu ya karya umarnin ko ya aikata wani abu da ka iya barazana ga zaman lafiya da tsaron jama’a.

Gwamnatin jihar ta yi kira ga mazauna Kano, masarautun gargajiya, ‘yan siyasa, magoya baya da sauran masu ruwa da tsaki da su kwantar da hankalin su, su kasance masu bin doka da oda tare da mutunta wannan umarni.

Haka kuma, gwamnatin ta tabbatar wa da al’ummar Jihar Kano cewa tana ɗaukar dukkan matakan da suka dace domin kare rayuka da dukiyoyi da kuma tabbatar da zaman lafiya da doka da oda a faɗin jihar.

Umarnin dai ya biyo bayan fitar da wasiƙu biyu daban-daban daga hannun Sarkin Kano Aminu Ado Bayero da Sarkin da gwamnati ta amince da shi, Muhammadu Sanusi II, waɗanda suka bayyana shirin su na gudanar da hawan doki na gargajiya a ranar Lahadi, 27 ga Satumba, 2026.

Wasiƙar Aminu, wadda Sakataren sa na Musamman ya sanya wa hannu, an aika ta ne zuwa ga Hakiman Ƙananan Hukumomi, inda aka sanar da su umarnin tsohon sarkin na su raka shi zuwa bikin Saukar Karatu a Unguwar Yakasai. An tsara cewa zai tashi daga gidan sa da ke Nasarawa da safe domin gudanar da wasu ayyuka, ciki har da zagayawa cikin birnin da kuma ganawa da jama’a.

An ce zai isa gidan sa da ke Mandawari da misalin ƙarfe 11:30 na safe, inda za a gudanar da wasu ayyuka, sannan da misalin ƙarfe 4:00 na yamma zai tashi a kan doki tare da tawagar sa domin halartar bikin Saukar Karatu a Unguwar Yakasai.

Wasiƙar ta bayyana cewa bayan kammala bikin, tsohon sarkin zai sake hawa doki tare da tawagar sa su koma Gidan Nasarawa.

Ita kuwa wasiƙa ta biyu, wadda ta fito daga Sakatariyar Majalisar Masarautar Kano ƙarƙashin jagorancin Sarki Sanusi, an aika ta zuwa ga Hakimai ne dangane da bikin Hawan Babban Ɗaki da aka tsara gudanarwa a ranar ta Lahadi, 27 ga Satumba, 2026.

Wasiƙar ta bayyana cewa ana sa ran wanda aka aike wa da wasiƙar zai halarci bikin Hawan Babban Ɗaki, wanda za a gudanar bisa tsarin shirye-shirye da ƙa’idojin da aka tanada.

An kuma buƙaci wanda aka aike wa wasiƙar da ya kasance a wurin bikin a kan lokaci, tare da shiga cikin ayyukan da aka tanada yadda ya kamata.

A taƙaice, wasiƙun biyu sun bayyana shirye-shiryen ayyukan gargajiya na ranar 27 ga Satumba, 2026, na sarakunan biyu da ke gaba da juna.

Sarakunan biyu sun shafe shekaru suna kai ruwa rana a kotu kan buƙatar kowane ɗayan su ta riƙe da babbar kujerar sarautar Kano.

Previous Post

Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta

Related Posts

Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta
Labarai

Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta

September 25, 2026
Kotu ta amince wa ICPC ta binciki na’urorin da aka ƙwato daga gidan El-Rufa’i
Tsaro

Cewar: El-Rufai Na koyi darussa daga shirun da abokan hulɗa ta suka yi kan halin da nake ciki

September 24, 2026
Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96
Labarai

Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96

September 24, 2026
Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya
Labarai

Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya

September 22, 2026
An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya
Tsaro

An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya

September 21, 2026
Gwamnatin Tarayya ta kare rashin halartar Tinubu a UNGA, ta ce Shettima na da cikakken iko
Siyasa

Gwamnatin Tarayya ta kare rashin halartar Tinubu a UNGA, ta ce Shettima na da cikakken iko

September 21, 2026

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!