• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Saturday, November 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai Tsaro

An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya

IRO MAMMAN by IRO MAMMAN
September 21, 2026
in Tsaro
A A
0
An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya
Tony Obina bayan ya sake shiga hannu

Tony Obina bayan ya sake shiga hannu

An ba da rahoton cewa an sake kama wani dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya, mai suna Tony Obina, bayan ya tsere daga Babban Gidan Yarin Kakata da ke gundumar Margibi a ƙasar Laberiya.

An ce Obina yana cikin fursunonin da suka tsere daga gidan yarin ranar Lahadi, bayan tserewar da Ma’aikatar Shari’a ta Laberiya ta tabbatar.

Kafar yaɗa labarai ta West Trybe News Media ta wallafa bidiyon da ke nuna Obina da wani mutum ana mayar da su gidan yarin, bayan an ce mazauna yankin sun gano su. A cikin bidiyon, an ga Obina sanye da gajeren wando shuɗi kaɗai yayin da ake mayar da shi gidan gyaran halin.

Wannan ya biyo bayan tabbatar da tserewar da Ma’aikatar Shari’ar Laberiya ta yi a wata sanarwa da ta fitar jiya Lahadi, 20 ga Satumba, 2026.

Ma’aikatar ta ce wasu fursunoni sun tsere daga Babban Gidan Yarin Kakata, kuma Jami’an Tsaro na Haɗin Gwiwa na Laberiya sun ƙaddamar da aikin nemo su da sake cafke su.

“Ma’aikatar Shari’a tana sanar da jama’a cewa an yi tserewar gidan yari a Babban Gidan Yarin Kakata da ke gundumar Margibi, wanda ya haifar da tserewar wasu fursunoni daga wurin,” inji sanarwar.

Ta ƙara da cewa jami’an tsaro suna ci gaba da neman waɗanda suka tsere, yayin da Hukumar Gidajen Yari da Gyaran Hali take duba bayanan gidan yarin domin tantance ainihin adadin waɗanda suka tsere da kuma ko su wane ne.

Ma’aikatar ta ce za a fitar da sunaye da sauran bayanan waɗanda suka tsere bayan kammala tantancewa, domin taimaka wa hukumomin tsaro da jama’a wajen nemo su.

Ta roƙi mazauna yankin da su kasance masu sa ido, kuma su bayar da bayani kan inda fursunonin da suka tsere suke ga ofishin ‘yan sanda mafi kusa ko wasu hukumomin tsaro.

Sai dai ma’aikatar ta gargaɗi jama’a da kada su yi ƙoƙarin kama ko ɓoye ɗaya daga cikin waɗanda suka tsere da kan su.

Kwanan nan ne wani kwamitin alƙalai (juri) mai membobi 12 na Kotun Da’ira ta 13 da ke gundumar Margibi ya samu Obina da laifi a wata babbar shari’ar fataucin miyagun ƙwayoyi.

An samu Obina da laifi tare da wasu jami’ai biyu na Hukumar Yaƙi da Miyagun Ƙwayoyi ta Laberiya, wato Joe Logan da Lovette Flowers. An ce shari’ar ta shafi miyagun ƙwayoyi masu kimanin darajar dalar Amurka $181,008 da kuma fiye da dalar Laberiya miliyan 63.2.

Rahotanni sun ce al’ummar yankin da jami’an tsaro ne suka kama Obina da sauran waɗanda suka tsere yayin da ake zargin suna ƙoƙarin arcewa bayan fasa gidan yarin.

Ma’aikatar Shari’ar Laberiya ta ce Jami’an Tsaro na Haɗin Gwiwa za su ci gaba da bayar da sababbin bayanai yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin sake kama sauran waɗanda suka tsere.

Tags: Laberiyamuggan ƙwayoyiTony Obinatserewa daga gidan yari
Previous Post

Gwamnatin Tarayya ta kare rashin halartar Tinubu a UNGA, ta ce Shettima na da cikakken iko

Next Post

Shekaru uku a CBN: Yadda Cardoso ya sauya fasalin CBN, ya saisaita manufofin kuɗi, ya daidaita tsare-tsaren tattalin arzikin Nijeriya

Related Posts

Iƙirarin satar sauraron wayar NSA da na yi kalamin siyasa ne kawai, inji El-Rufai a kotu
Tsaro

Iƙirarin satar sauraron wayar NSA da na yi kalamin siyasa ne kawai, inji El-Rufai a kotu

November 25, 2026
EFCC ta samu nasarar hukunta mutumin da ya yi ƙoƙarin sumogar zinari mai darajar Naira biliyan 4.4 a Kano
Tsaro

EFCC ta samu nasarar hukunta mutumin da ya yi ƙoƙarin sumogar zinari mai darajar Naira biliyan 4.4 a Kano

November 17, 2026
Sojoji sun halaka ’yan ta’adda, sun ceto mutum 16, sun ƙwato babura 38 a Neja da Kebbi
Tsaro

Sojoji sun halaka ’yan ta’adda, sun ceto mutum 16, sun ƙwato babura 38 a Neja da Kebbi

November 6, 2026
Ƙungiyar Amnesty ta buƙaci bincike kan bidiyon atisayen muzaharar Izala
Tsaro

’Yan sanda sun kama matashin Izala kan bidiyon da ke tunzura rikicin addini

October 27, 2026
Ƙungiyar Amnesty ta yi tir da kisan malamin addini Sheikh Yahaya Masussuka
Tsaro

’Yan sanda a Katsina sun tabbatar da kashe Sheikh Yahaya Masussuka da abokin sa

October 26, 2026
Ƙungiyar Amnesty ta yi tir da kisan malamin addini Sheikh Yahaya Masussuka
Tsaro

Ƙungiyar Amnesty ta yi tir da kisan malamin addini Sheikh Yahaya Masussuka

October 26, 2026
Next Post
AFC ta naɗa gwamnan CBN matsayin shugaban Kwamitin Daraktoci

Shekaru uku a CBN: Yadda Cardoso ya sauya fasalin CBN, ya saisaita manufofin kuɗi, ya daidaita tsare-tsaren tattalin arzikin Nijeriya

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • November 2026
  • October 2026
  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!