Fadar Shugaban Ƙasa ta yi watsi da wasu rahotanni da suka fito daga birnin Washington na ƙasar Amurka dangane da Shugaba Bola Ahmed Tinubu, tana mai bayyana su a matsayin farfagandar siyasa da aka shirya domin yin tasiri a harkokin siyasar Nijeriya gabanin babban zaɓen 2027.
Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara na Musamman kan Yaɗa Labarai da Hulɗar Jama’a, Dakta Sunday Dare, shi ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya zargi tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar, da ɗaukar wani kamfanin ‘yan barandar siyasa da ke birnin Washington domin gudanar da wani kamfen da ya ce yana da alaƙa da siyasar Nijeriya.
Dare ya ce rahotannin da ake yaɗawa daga Amurka ba wasu bayanan sirri na hukumomin ƙasar ba ne, illa abin da ya kira “hasashen siyasa da aka naɗe cikin rigar bayanan sirri.”
A cewar sa, ana ƙoƙarin gabatar da wasu bayanan sanarwa da ake fitarwa daga Washington da sunan ra’ayin gwamnatin Amurka, alhali kuwa ba haka lamarin yake ba.
“Takardun sanarwar da ake fitarwa daga Washington, waɗanda ke ɗauke da kalamai masu tayar da hankali, kayan farfaganda ne na hulɗar jama’a da ake ƙoƙarin gabatarwa kamar ra’ayin Gwamnatin Amurka. Amma ba haka ba ne,” inji Dare.
Ya ce ya kamata a yi watsi da rahotannin saboda, a cewa sa, ba su da hujjojin da za su tabbatar da zarge-zargen da suke ɗauke da su.
“Rahoton bai gabatar da wata takardar bayanan sirri ba, bai ambaci sunan wani jami’in ƙasashen Yamma muraran ba, sannan bai kawo wata hujja ta musayar sirrin Nijeriya ko albarkatun ta ba,” inji shi.
Dare ya ƙalubalanci masu yaɗa rahotannin da su fito da abin da suke kira rahoton bayanan sirri mai muhimmanci tare da bayyana majiyoyin su.
Ya ce: “Ba komai ba ne face hasashen siyasa da aka naɗe cikin rigar bayanan sirri. Muna ƙalubalantar su da su fito da abin da suke kira ‘rahoton bayanan sirri mai matuƙar muhimmanci’, su bayyana majiyoyin su da ba su bayyana sunan su ba, sannan su gabatar da tabbatattun hujjoji kan zarge-zargen su.”
Mai bai wa shugaban ƙasar shawarar ya ce bayanan da ake iya gani a bainar jama’a ƙarƙashin dokar rajistar wakilan ƙasashen waje ta Amurka, wato Foreign Agents Registration Act (FARA), sun nuna cewa Atiku ya ɗauki hayar wani kamfanin ‘yan barandar siyasa mai suna Von Batten-Montague-York, L.C., da ke Washington aiki na tsawon watanni 12 kan kuɗin da aka ce sun kai dala miliyan 1.2.
A cewar Dare, manufar yarjejeniyar ita ce gudanar da wani kamfen na siyasa domin ƙalubalantar bayanan gwamnatin Nijeriya da kuma amfani da tsofaffin bayanan shari’a domin neman galaba a siyasar cikin gida gabanin zaɓen 2027.
“Manufar wannan yarjejeniya ba bayar da shawarwari na gaskiya kan shugabanci ba ce, sai dai aiwatar da wani yaƙin neman tasiri na siyasa domin ‘daidaita’ bayanan gwamnatin Nijeriya da kuma amfani da tsofaffin takardun shari’a da aka riga aka warware domin neman galaba ta siyasa a cikin gida gabanin babban zaɓen 2027,” inji Dare.
Har ila yau, Dare ya yi watsi da matsayin Dakta Karl-Marx Edward Okeke-Von Batten a matsayin wani jami’in gwamnati, yana mai bayyana shi a matsayin mai gudanar da aikin barandar siyasa na kasuwanci.
“Laƙabin ‘Babban Mai Bai wa Gwamnati Shawara’ da ya ba kan sa wata dabara ce ta amfani da kalmomi domin haifar da wata fahimta ta daban,” inji shi.
Ya ce bai kamata a ɗauki kalaman Okeke-Von Batten a matsayin ra’ayin gwamnatin Amurka ko na Shugaba Donald Trump ba.
“Kalaman Dakta Karl Von Batten suna wakiltar ra’ayin wani mutum ne kawai da ke da alaƙa da muradun siyasar ɓangaren Atiku, ba ra’ayin gwamnatin Amurka ko Shugaba Trump ba,” inji Dare.
Fadar Shugaban Ƙasa ta kuma yi watsi da hasashen da ke ƙoƙarin danganta tafiyar Shugaba Tinubu zuwa Turai da shari’ar neman wasu bayanai ƙarƙashin dokar Freedom of Information Act (FOIA) da ke gudana a Amurka.
Dare ya ce shugaban ƙasar yana kan hutun sa na shekara da aka tsara tun da farko, yana mai jaddada cewa babu wata alaƙa tsakanin tafiyar sa zuwa Turai da shari’ar da ke gudana a Amurka.
“Wannan wani yunƙuri ne na karkatar da hankali ta hanyar danganta motsin shugaban ƙasa da wata shari’a a ƙasashen waje, amma gaskiyar magana ita ce Shugaba Tinubu yana kan hutun sa na shekara da aka tsara tun da farko, kuma babu wata alaƙa tsakanin tafiyar sa zuwa Turai da shari’ar FOIA da ke gudana a Amurka,” inji Dare.
Ya ce shari’ar da ke Amurka ta fara gudana tun shekarar 2023, yana mai cewa hukumomin binciken ƙasar suna kare wasu hanyoyin gudanar da bincike da kuma majiyoyin bayanan su.
Dare ya kuma ambaci wasu kalamai da lauya Wole Afolabi, SAN, ya yi a wata tattaunawa a gidan talbijin dangane da ƙarar neman a saki wasu tsofaffin bayanai da hukumomin gwamnatin tarayya na Amurka ke riƙe da su.
A cewar sa, yunƙurin hana fitar da wasu sassan takardun ya yi daidai da dokokin Amurka da aka tanada domin kare bayanan bincike da majiyoyin bayanai.
Dare ya ce ya kamata a bar ɓangaren shari’a da hukumomin tabbatar da doka na Amurka su gudanar da ayyukan su ba tare da katsalandan na siyasa ba.
“A bar ɓangaren shari’a da hukumomin tabbatar da doka na Amurka su gudanar da ayyukan su bisa tanadin doka ba tare da tsoma bakin siyasa ba, kamar yadda suka saba yi,” in ji shi.
Mai magana da yawun shugaban ƙasar ya kuma soki yadda ya ce ‘yan adawa suke tafiyar da shirye-shiryen su na zaɓen 2027, yana mai zargin su da mayar da hankali kan ce-ce-ku-ce da zarge-zarge maimakon gabatar da manufofi da tsare-tsaren cigaba.
Ya ce ‘yan adawa ba su gabatar da ingantattun hanyoyin warware matsalolin tattalin arziki, noma, masana’antu da sauran fannoni masu muhimmanci ga cigaban ƙasa ba.
Dare ya ce gwamnatin Shugaba Tinubu, a nata ɓangaren, tana ci gaba da aiwatar da manufofin gyaran tattalin arziki, bunƙasa ababen more rayuwa da kuma sauye-sauye a hukumomin gwamnati.
“Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu na ci gaba da shimfiɗa tubalan cigaba mai ɗorewa ta hanyar tsauraran matakan kula da harkokin kuɗi, bunƙasa ababen more rayuwa da kuma sauye-sauyen hukumomin tsaro,” inji shi.
Ya jaddada cewa ‘yan Nijeriya ne za su yanke hukunci kan makomar siyasar ƙasar ta hanyar zaɓe, bisa ayyukan shugabanni da manufofin da suka gabatar.
“Tabbacin dimokiraɗiyya na gaskiya ana samun sa ne ta hanyar akwatin zaɓe da kuma ayyukan da za su amfani jama’a a cikin ƙasa, ba ta hanyar ƙirƙirar manyan labarai da aka biya kuɗi da kuɗin waje ba,” inji Dare.
Ya ƙara da cewa ba za a iya samun nasarar zaɓe ta hanyar ɗaukar masu barandar siyasa daga ƙasashen waje ko gudanar da kamfen na farfaganda ba.
“’Yan Nijeriya sun fahimci abin da ke faruwa a bayan farfagandar da aka biya kuɗi. Ana samun nasarar zaɓe ne bisa ayyukan da za a iya tabbatarwa a cikin gida, hangen nesa na ƙasa da kuma ingantattun ababen more rayuwa, ba ta hanyar kalaman da aka shigo da su daga ƙasashen waje tare da kashe miliyoyin kuɗi domin neman farfaɗowar siyasa ba,” inji Dare.
Sanarwar ta ƙare da cewa gwamnatin Shugaba Tinubu za ta ci gaba da mayar da hankali kan ayyukan cigaba, yayin da ‘yan Nijeriya za su tantance jam’iyyun siyasa da shugabannin su bisa manufofin su, tarihin su da kuma irin ayyukan da suka gudanar domin inganta rayuwar jama’a.







