Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana alhinin sa kan rasuwar Sarkin Zamfaran Zurmi, Mai Martaba Alhaji Bello Sulaiman,wanda ya rasu a ranar Litinin bayan ya shafe shekaru biyar a kan karagar mulkin Masarautar Zurmi.
A cikin wata sanarwa da Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Yaɗa Labarai da Dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Laraba, Shugaba Tinubu ya miƙa ta’aziyyar sa ga iyalan marigayin, Majalisar Masarautar Zurmi, Gwamnatin Jihar Zamfara da al’ummar jihar, tare da ɗaukacin masarautun Nijeriya.
Shugaban Ƙasar ya bayyana marigayin a matsayin basarake mai girma da ƙima, wanda ya jagoranci al’ummar sa cikin hikima, mutunci da jajircewa a wani lokaci mai matuƙar wahala.
Ya ce marigayin ya nuna ƙwarewa da hangen nesa wajen jagoranci, musamman wajen tunkarar matsalolin tsaro da suka addabi Masarautar Zurmi.
Tinubu ya ce Sarkin ya kasance babban jigo wajen tabbatar da zaman lafiya, haɗin kai da juriya a tsakanin al’ummar sa.
A cewar sa, shawarwari masu hikima da ƙoƙarin marigayin na samar da zaman lafiya sun taimaka ba kawai ga Masarautar Zurmi ba, har ma ga Jihar Zamfara baki ɗaya, musamman a ƙoƙarin dawo da zaman lafiya mai ɗorewa a yankin Arewa maso Yammacin Nijeriya.
Shugaba Tinubu ya roƙi Allah Maɗaukakin Sarki Ya gafarta wa marigayin kurakuran sa, Ya saka masa da alheri kan ayyukan da ya gudanar, tare da yi masa rahama da Aljannar Firdausi.
Haka kuma, Shugaban Ƙasar ya roƙi Allah ya bai wa iyalan marigayin da duk waɗanda wannan rashi ya shafa haƙuri da ƙarfin zuciyar jure wannan babban rashi.







