Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya al’ummar Musulmi murnar zagayowar ranar Maulidin Annabi Muhammad (SAW), inda ya buƙace su da su yi koyi da kyawawan halaye da koyarwar Manzon Allah.
A cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan yaɗa labarai da dabarun sadarwa, Bayo Onanuga, ya fitar ranar Talata, Shugaba Tinubu ya ce bai kamata bikin Maulidi ya tsaya kawai kan tunawa da ranar haihuwar Annabi Muhammad (SAW) ba.
Ya ce ya kamata a yi amfani da wannan lokaci wajen yin nazari a kan rayuwar Manzon Allah, yin addu’a da kuma koyon darussan da ke cikin ta.
Shugaban ya jaddada muhimmancin bin koyarwar Annabi Muhammad (SAW), yana mai cewa rayuwar sa ta ƙunshi manyan darussa da suka shafi ibada, haƙuri, juriya, sadaukar da kai da kuma kyautata mu’amala da jama’a.
Tinubu ya kuma yi kira ga malaman addini da su yi amfani da lokacin Maulidi wajen yi wa Najeriya addu’ar samun zaman lafiya da ci gaba, tare da wayar da kan mabiyan su kan muhimmancin mayar da darussan rayuwar Annabi zuwa aikace-aikace.
A cewar sa, hakan zai taimaka wajen ƙarfafa kishin ƙasa, zaman lafiya da haɗin kan al’umma.
Haka kuma, Shugaban Ƙasar ya bukaci Musulmin da ke gudanar da bukukuwan Maulidi da su tallafa wa mabuƙata da masu rauni, musamman a wannan lokaci da ake fuskantar ƙalubalen tattalin arziki da na rayuwa.
Ya kuma yi kira ga al’ummar Nijeriya da su ci gaba da yi wa ƙasar addu’a domin samun nasara wajen shawo kan matsalolin tsaro da sauran ƙalubalen da ke addabar wasu sassan ƙasar.







